ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tun Ina Karama Nake Sha’awar Harkar Wasan Kwaikwayo —Fartima Hamza

by Rabi'at Sidi Bala
4 months ago
Wasan

Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jaruman finafinan hausa manya da kanana daga cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, inda a yau shafin ya yi cozali da wata jarumar mai suna FATIMA HAMZA wacce aka fi sani da FATI GWARAMA. A yayin da take bayyana wa masu karatu yadda aka yi ta tsinci kanta a cikin masana’antar Kannywood, ta bayyana wasu halaye da wasu daga cikin ‘yan masana’antar suke da ita. Haka kuma jarumar ta yi kira ga masu kokarin shiga cikin masana’antar tare da basu shawarwari, har ma da wasu batutuwan masu yawa.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki

ADVERTISEMENT

Sunana Fatima Hamza Adam wacce aka fi sani da Fati Gwarama.

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

An haife ni a garin Lagos, amma na girma a garin Kano. Mahaifiya ta haifaffiyar garin Kano ce, mahaifina mutumin Bauchi ne. Nayi karatu na tun daga firamare har zuwa sakandire a garin Kano.

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?

Tun ina karama nake da sha’awar harkar wasan kwaikwayo, saboda har a makaranta ni ce wacce nake jagorantar ‘Hausa Club’. Sannan da na gama karatu ban bayyanawa mahaifana ba saboda mahaifina da ya fara jinyar ajali har sai da Allah yayi ikonsa. Bayan rasuwar mahaifina na shaidawa mahaifiyata, daga nan ta ba ni goyan baya.

Kina so ki ce baki fuskanci wani kalubale daga wajen mahaifiyarki ba kenan?

Eh, ban samu wani kalubale sosai a kanta ba, saboda irin yaddar da ta yi min.

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?

To, a gaskiya na fuskanci kalubale saboda mu hausa fulani bamu fiya yadda da fim ba, amma saboda mahaifiyata ta goyamin baya sai abin ya zo min da sauki. Sai bayan ita ma Allah ya yi mata rasuwa sannan kuma kalubalan ya kasance, amma dai Alhamdulillah.

Da su wa ki ka fara cin karo a farkon shigarki masana’antar kannywood?

Na fara haduwa da su Lawan Ahmad, Salisu S. Fulani, Ali Rabi’u Ali Daddy, Aminu Asarab da dai sauran.

Da wane fim ki ka fara?

Sunan fim din ‘Cikin Wane’, wanda ‘director G Sharif’ ya bada umarni.

Ya farkon farawar ta kasance?

Akwai wani furodusa ana kiransa da Ali bet, shi kuma dan unguwar mu ne. A sanadiyyar sa muka hadu da ‘director’ daga nan sai ya bani ‘roll’ din jarumar fim din gabadaya.

Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Na yi finafinai sun kai kamar guda ashirin ko sama da haka.

Ko za ki iya fadawa masu karatu sunayen kadan daga finafinan da ki ka fito ciki?

Eh, a gaskiya suna da yawa, sai dai na fada miki wasu daka ciki; “A Wani Gida, Kakanda, Maryama, Izzar so, Hujja, Ki Yafe Ni, da dai sauransu.

A finafinan da ki ka fito ciki wanne ne ya zamo bakandamiyyarki, kuma me ya sa?

Duk fim din da na fito ciki ina son shi amma na fi son fim din ‘A wani Gida’, saboda na sha wahala sosai, kuma ina cikin dimuwar rashin mahaifiyata. Sannan kuma an yi tunanin ba zan iya ba, saboda halin da nake ciki, amma kuma daga karshe sai nayi abin da ba a yi tunani ba, sanadin hakan na sami alkairi sosai.

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

Na sami nasarori sosai asanadiyyar fim wanda ba zan iya shaidawa ba amma dai Alhamdulillah an sami nasara.

Wane irin kalubale ki ka taba fuskanta game da fim?

Eh! to, kinsan kowace sana’a da nata kalubalen kuma ni kaina na fuskanci kalubale sosai, musamman ma a tare da abokan sana’ar mu. Saboda wasu daga cikinsu ba sa san cigaban wani wanda ya zo bayansu, sannan kuma wasu daga cikinmu suna sa kyashi, ga kuma wani lokacin ban gishiri ne na baka manda.

Bayan klubalen da ki ka fuskanta, ko akwai wani abu da ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwar ki?

Abin da ba zan iya mantawa da shi ba shi ne, rashin mahaifana da nayi a cikin shekara daya, ba zan taba iya mantawa da shi ba. Saboda ina matukar kewar mahaifana sosai.

Wane ne ubangidanki a masana’anyar Kannywood?

Ai Kinsan babu wani wanda yake ci gaba ba tare da agazawar wani ba, Ali Bet shi ne ubangidana na farko a cikin wannan masana’antar tamu.

Kafin shigarki masana’antar Kannywood wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?

Eh! to, babu jaruman da nake so kamar Hafsa Shehu, da kuma Ahmad S. Nuhu ina sansu sosai. Saboda san da nake mata har bikinta sai da aka kai ni kuma na je gidanta tana amarya muka yi sabani, na takaice miki da Ahmad ya rasu a gidanmu ranar babu wanda ya karya saboda ina ta kuka, babana ya mutu to, wadannan sune wadanda nake so.

Mene ne burinki na gaba game da fim?

To, burina shi ne na ga muna hada kanmu muna cire hassada, sannan kuma ina san na ga na kawo sauyi a cikinta da ci gaba.

Ya batun aure, yaushe ki ke saka ran yin aure.

Shi ai aure lokaci ne, kuma koyaushe ya zo ina maraba da shi.

Ko akwai wani jarumi da ya taba cewa yana sonki zai aure ki cikin masana’antar?

Eh to, akwai wani wanda muka taba batun aure da shi amma ba zan iya bayyana shi ba.

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Eh ni marubuciya ce ta finafanai, sannan kuma ina yin kasuwanci.

Wasu daga cikin masana’antar Kannywood na kokawa game da masana’antar, shin wace ce ita, kuma ya cikinta yake?

To, kowace sana’a akwai daidai akwai ba daidai ba, sannan kuma masana’antar fim masana’anta ce wacce duk abin da ka zo da shi take karbarka, kuma masana’anta ce wacce za a sami duk wani abu da aka zo domin shi.

Ko akwai wani kira da za ki yi ga masu kokarin shiga cikin masana’antar?

Duk wani wanda yake san wannan sana’ar ya shigo da niyya mai kyau, Saboda duk abin da ka zo domin shi, shi kake samu.

Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?

To masoyana na fadin duniya ina mai farinciki da kaunar ku gare ni, sannan kuma ku jira ku ga irin tanadin da nayi muku a cikin wannan shekarar. Ina gaida duk wani masoyina da ma wanda ba ya sona, duk ina yi musu fatan alkairi.

Wasan
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

MASU ALAKA

Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
Nishadi

Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Labarai

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

July 12, 2026
Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
Nishadi

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

June 14, 2026
Next Post
Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwarorinsa Na Afghanistan Da Holland

Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwarorinsa Na Afghanistan Da Holland

LABARAI MASU NASABA

Wasan

Ƴan Bindiga Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu

July 25, 2026
Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

Yadda Jami’an Tsaro Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda A Wasu Jihohin Nijeriya, Sun Kama ‘Yan Kasar Pakistan Bakwai

July 25, 2026
Wasan

Obasanjo Da Atiku Sun Sake Musayar Zafafan Kalaman Zargin Juna

July 25, 2026
Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

Manufofin Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Sun Lalata Rayukan Al’ummar Nijeriya —ADC

July 25, 2026
An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.