Yau 26 ga watan Agusta, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai bisa jigon “kyakkyawar farawa da tafiyar shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15”, inda wani jami’in ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa da abin ya shafa, ya gabatar da bayanai game da yadda ake aiwatar da shirin da kuma gaggauta ciyar da sabbin masana’antu gaba.
A taron, an bayyana cewa, a lokacin shirin karo na 14 , girman masana’antu na kasar Sin ya ci gaba da karuwa, kuma darajar masana’antu masu girma ta karu da kashi 5.9% a mizanin kowace shekara, yayin da jimillar darajar masana’antu ta karu daga Yuan tiriliyan 26.5 a shekara ta 2020 zuwa Yuan tiriliyan 34.7 a bana, adadin da ya kai yawan alkaluman GDPn kasar da kusan kashi 25%.
Bugu da kari, kasar Sin ta riga ta samu nasarar kera ma’aunai kusan 200 na manyan fasahohi na AI.
A taron, an bayyana cewa, a lokacin shirin karo na 15 , kasar Sin za ta kafa cibiyoyin ba da misali na bunkasa sabbin masana’antu na kasa, ta mayar da hankali kan sabbin manyan fannoni kamar fasahar sadarwa ta zamani, da sabbin makamashi, da sabbin kayan aiki, da motoci masu aiki da fasahar sarrafa kansu, da mutum-mutumin inji mai siffar dan adam, kana da magungunan halittu da kayan aiki masu inganci, da jiragen sama da na’urorin sararin samaniya, don samar da jerin abubuwan koyi da za su ba da jagoranci wajen bunkasa sabbin masana’antu.
Bugu da kari, za a kuma himmatu wajen bunkasa nagartattun kamfanoni masu inganci, da karfafa tsarin bunkasa wadannan kamfanoni a matakai-matakai, da habaka kananan kamfanoni masu kwarewa da kirkire-kirkire, da samar da karin kamfanoni dake da fifiko a bangaren kwarewa da “kere-kere na musamman” da samun riba mai yawa da fadada kasuwa da kuma kamfanonin da suka zamo zakaru a fannin masana’antu. (Amina Xu)














