ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Ta Samo Tallafin Dala Biliyan 1 Domin Aikin Zamanantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Ƙasar Nan

by Bello Hamza
3 weeks ago
Ruwa

Shugaban hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa NPA, Dakta Abubakar Ɗantsoho, ya bayyana cewa, NPA ta samu sahalewar dala biliyan ɗaya domin gudanar da shirin zamantar da a tashoshin Jiragen Ruwan ƙasa

Ɗantsoho ya sanar da cewa, za a fara gudanar da aikin ne, kafin  a zango na uku na shekarar 2026.

Shugaban ya ƙara da cewa, shirn na zamantar da tashoshin, wanda wata babbar nasara ce, wanda kuma  gwamnatin tarayya ta ƙaddamar na ɗaya daga cikin shirin da ke a ƙarƙashin ma’aiakatar bunƙasa tattalin arziki na Teku

ADVERTISEMENT

Ya ci gaba da cewa, an tsara shirin ne, bisa nufin, yi wa kayan aikin da ke a tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, garanbawul, musamman domin a ƙara ƙarfafa ayyukansu da ƙara tabatar da yin gasar hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka.

Shugaban ya bayyana cewa, tuni aka kammala tsare-tsaren yadda za a gudanar da aikin tare da wasu daga ƙasar waje, wanda kuma fara aikin, ya haɗa da masu ruwa da tsaki abokan tuntuɓa da kuma sauran alumomin da ke a yankunan da tashoshin Jiragen Ruwan ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cewar Dakta Ɗantsoho, an riga an samu sahalewar gaba ɗaya, ta dala biliyan ɗaya, domin fara gudanar da aikin, tare da wasu abokan haɗaka da sauran hukumi na ƙasar waje.

“Mun riga mun kammala dukkan ƙa’idojin samar da kuɗin aikin, inda kuma ake sa ran za a fara gudanar da aikin ne, kafin a zango na uku na shekarar 2026,” inji Dakta Ɗantsoho.

Kazalika, shugaban hukumar ta NPA, ya bai wa ƴan Nijeriya tabbacin cewa, za su fara gani a ƙas, na kayan da za a samar domin gudanar da aikin sabunta tashoshin Jiragen Ruwan ƙasa.

Ya ƙara da cewa, za su fara ganin hakan ne, tun a zango na huɗu na shekarar 2026, inda ya yi nuni da cewa, shirin na zamantar da tashoshin, ana sa ran zai ƙara taimaka wa, wajen ƙara inganta ayyukan dsa ake gudnarwa a tashoshin.

“Shirin na zamantar da kayan da ake gudanar da ayyuakan a tashoshin Jiragen Ruwan, an tsara shi ne, bisa nufin yiwa kayan garanbawul, musamman domin su tafi kafaɗa da kafaɗa da sauran kayan aikin irin na faɗin duniya, “a cewar shugaban.

“A zahirance kuma a hukumance aikin na dala biliyan ɗaya, za a fara yinsa ne a zango na uku na shekarar 2026. Inji Ɗantsoho.

Ya ƙara da cewa, ƴan Nijeriya za su fara ganin aikin ne tare da samar da kayan aikin na zamani daga zango na huɗu na shekarar 2026.

Ya ci gaba da cewa, da zarar an kamala aikin zai rage ƙalubalen da ake fuskanta kusan na kaso hamsin a cikin ɗari, musamman na Jiragen ruwa da ake samu a tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar tare da kuma ƙara inganta gudanar da ayyuka, a cikin sauƙi.

A cewar Ɗantsoho, aikin ba wai na ƙananan ma’aikata ba ne, aiki ne da ya haɗada, samar da kayan aikin na fasahar zamani, musamman kayan fasahar kimmiyar na ƁTS, da su ƙara taimaka wa, wajen zirga-zirgar Jiragen Ruwa da kuma gudanar da ayyuka a tashoshin, a cikin sauƙi.

“A yanzu kan ƙoƙarin tsara zirga-zirgar wasu Jiragen da a turance ake kira da tugboats da kuma wasu ƙananan Kwale-Kwale da kuma kan gyran Katangun kankaren Siminti da ke a Tashoshin Tin-Can da Apapa,” a cewar shugaban.

“Sanya kayan fasahar kimmiyar ta ƁTS, za ta taimaka matuƙa wajen da damar ci gaba da sanya Ido da kuma bayar da kariya ga ɗaukacin sararin Ruwan,” ini Ɗantsoho.

Shugaban ya ƙara da cewa, faɗaɗa guraren da ake ajiye kayan da aka tantancewa a Tashoshin kafin a fitar da su zuwa ƙetare wato EPT da kuma ƙara haɓaka ayyukan yin hada-hadar kasuwanci a tashoshin, na ɗaya daga cikin dabarun da za su ƙara matuƙar taimaka wa, wajen ƙara tara kuɗaɗen shiga, da kuma ƙara bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Ɗantsoho ya sanar da cewa, NPA na ci gaba da bayar da fifiko, wajen ƙara ƙarfafa hada-hadar kasuwanci a tashoshin ƙasar, ƙara inganta ayyuka a tashoshin, tare da turawa gwamnatin tarayya kuɗaɗen shiga, ta hanyar sauye-sauyen da aka samar na yin amfani da fasahar zamani.

“Abinda muka bayar da fifiko akai shi ne, ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci a tashoshin, wanda hakan ya bai wa ƙasar, a zangon farko na shekarar 2026 kacal, damar samun rarar da ta kai ta Naira tiriliyan 7.54,” a cewar Ɗantsho.

Ɗantsoho ya bai wa  masu ruwa da tsaki a fannin, tabbacin cewa, NPA za ta ci gaba da ƙara ƙaimi, wajen tara kuɗaɗen shiga wanda ake turawa a cikin gidaniyar tara kuɗaɗe ta CRF, tare da kuma ƙara inganta tsarin.

“Nan da sama da watanni sha biyu masu zuwa, masu ruwa da tsaki a fannin ina mai ba su tabbacin cewa, NPA za ta ci gaba da ƙara ƙaimi, wajen tara kuɗaɗen shiga wanda ake turawa a cikin gidaniyar tara kuɗaɗe ta CRF, tare da kuma ƙara inganta tsarin,” inji shugaban’

Haka zalika ya ce, NPA za ta ƙara ɗaga daragar kayan aikinta a sauran tashoshin Jiregen, domin a ƙara haɓaka ayyukansu.

“Za mu ƙara ɗaga daragar kayan aikinta a sauran tashoshin Jiregen, domin a ƙara haɓaka ayyukansu cikinsu har na Onne da Kalaba da kuma Warri,” a cewarsa .

Shugaban ya kuma sanar da cewa, aikin faɗaɗa EPT, zai bayar da gagarumar gudunmawa, wajen ƙara fitar da kayan da basu shafi fannin Mai ba, zuwa ƙetare, tare da bunƙasa shirin haɓaka tattalin arzki na gwamnatin tarayya..

Ya ce, NPA na kuma kan samar da tsarin PCS, wanda zai ƙara taimaka wa shirin NSW na ƙasa,  musamman wajen rage cunkosn Jiragen Ruwa a tashoshin.

“Burin mu shi ne, muga a cikin sa’io 48 duk wani cunkoso an kawar da shi, a cikin tashoshin, wanda hakan zai ƙara bayar da damar gudanar da gasa ga hada-hadar kasunwanci a tashoshin, “inji Ɗ Dantsoho .

Ruwa
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Adeleke Ya Lashe Zaɓen Osun Da Ƙuri’u 511,067

Adeleke Ya Lashe Zaɓen Osun Da Ƙuri’u 511,067

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.