ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Muhimman Abubuwa Da Ba A Sani Ba Game Da Ƙwaƙwalwa

by Sani Anwar
5 months ago
Kwakwalwa

A yayin da wani sashi na ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa (Brain cells), suka mutu, wani sashin na iya karɓar aikinsu. Wannan shi ne abin da ke faruwa a ƙwaƙwalwar mai shanyewar ɓarin jiki, ta yadda motsin hannu ko ƙafa kan dawo bayan ya shanye.

– Ƙwaƙwalwa ba ta ɗauke da maganaɗisin jin ciwo (Pain receptors), shi yasa ƙwaƙwalwa ba za ta iya jin ciwo kamar yadda sauran sassan jiki ke jin ciwo ba. Don haka, ciwon kai na zuwa ne daga sauran sassan da ke kewaye da ƙwaƙwalwa, amma ba ƙwaƙwalwar kanta ce ke ciwo ba.

  • Matsalar Ciwon Kwakwalwa A Gidajen Yarin Kasar Nan
  • An Yi Min Abin Da Zuciya Da Kwakwalwa Ba Za Su Taba Mantawa Ba A Wata Kungiyar Marubuta – Maryam

– Ƙwaƙwalwa ta fi kowane sashin jiki son kanta. Dalili kuwa, duk da cewa nauyinta ba ya wuce kashi uku cikin ɗari (3%) na nauyin jikin mutum, amma dole sai an ba ta kashi talatin cikin ɗari (30%) na yawan jinin da zuciya ke turawa a kowane bugu.

ADVERTISEMENT

– A mafi yawan lokaci, Ɗan’adam na amfani da dukkanin sassan ƙwaƙwalwarsa, saɓanin tatsuniyar da ke cewa; wai Ɗan’adam na iya amafani da ɗan wani sashi na ƙwaƙwalwarsa ne kawai a tsawon rayuwarsa.

– Kusan rabin sinadarin abincin da yara ke ci, na tafiya ne wajen gina ƙwaƙwalwarsu; domin koyon abubuwa daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

– Kamar yadda motsa jiki ko atisaye ke ƙara lafiyar jiki, haka nan ma yake ƙara lafiyar ƙwaƙwalwa.

– Kamar yadda tambarin babban yatsan hannunka (thumbprint) yake daban da na kowa, haka ma yadda ƙwaƙwalwarka ke aiki daban da ta kowa.

– Har ila yau, ƙwaƙwalwa na aiki ne da tsarin lantarki a yayin da mutum yake a farke, kazalika ƙwaƙwalwa na iya samar da ƙarfin lantarkin da zai iya kunna farin ƙwai na lantarki.

– Kimanin kashi sittin cikin ɗari (60%) na ƙwaƙwalwa kitse ce.

– Har wa yau, rashin isassshen barci na rage kaifin ƙwaƙwalwa. Domin kuwa, Ɗan’adam na buƙatar barci na kimanin awa bakwai zuwa tara a kullum.

– Ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa, ba sa iya jure rashin iskar oksijin da sinadarin gulukos na fiye da minti biyar, face sai sun mutu.

Kwakwalwa
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Rage Harajin Shigo Da Shinkafa, Motoci Da Wasu Kaya 127

Gwamnatin Tarayya Ta Rage Harajin Shigo Da Shinkafa, Motoci Da Wasu Kaya 127

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.