Bisa shirin ci gaban kasa da kyautata jin dadin zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar na kasar Sin da ya fara gudana daga bana zuwa shekarar 2030, akwai wasu muhimman sassa da za su taka rawar gani wurin cimma burin da aka sa a gaba.
Daya daga ciki shi ne zamanantar da tsoffin masana’antu ta yadda za su tashi daga matsayinsu na tsohon yayi zuwa sabo. Domin karfafa tushen ainihin tattalin arzikin kasar. A karkashin wannan shiri, za a ci gaba da daga matsayin tsoffin masana’antun tare da fifikon da ya kamata. Ana hasashen nan da shekaru 5 masu zuwa za su iya samar da karin kudi CNY tiriliyan 10 (dala tiriliyan 1.41) a fagen kasuwancin kasar. Don haka wannan yana mufin cewa, kamfanonin Sin ba tsufa za su yi ba, sai dai sake daidaita su su zamo na zamani. Bangaren ayyukan bayar da hidimomi shi ma zai yi rawar gani musamman ganin yadda yake kara samun tagomashi bisa kere-keren zamani.
Daga sabbin fasahohin wannan sashe, akwai wani mutum-mutumin injin aske ciyawa da kasar Sin ta kera da ke iya kaucewa cin karo da wani abu ko wani kalubale na ba-zata, yayin da yake aiki shi da kansa ba tare da wani ya sarrafa shi ba. Sannan yana aiki ba tare da bin tsarin wayar da ake binnewa a karkakashin kasa na yankin da yake aiki ba kamar yadda aka saba a tsohon yayi.
Kazalika, idan cajin batirinsa ya kare, da kansa zai koma wurin caji kuma ya yi wa kansa caji. Wannan fasaha tana saukaka wa masu gudanar da aikin aske ciyawa ba tare da gajiyarwa mai tsanani ba. Idan aka dubi sashen sabbin masana’antu kuma wanda shi ma muhimmi ne da zai taka rawa, kasar Sin tana ci gaba da bunkasa samar da sabbin masana’antu ta fuskar kere-keren mutum-mutumin inji a sassa daban-daban na rayuwa.
Tuni wannan sashe ya kasance mai ba da gudunmawar kashi 18% na alkaluman tattalin arzikin kasar. Sauran sassan da za su kasance ginshikan samar da ci gaban kasar sun hada da sarrafa kayayyaki a bangaren kimiyyar halittu, da fasahar sada kwakwalwar dan’adam da kwamfuta domin sadarwa kai-tsaye a tsakaninsu.
Wannan fasaha ce da take taimaka wa mutane masu lalurar nakasar kafafu da hannaye ta yadda za su rika biyan bukatunsu na rayuwa ta hanyar bai wa na’ura umarni bisa tunani ko halarto da abin da suke so a cikin kwakwalwarsu kawai. Abun za a gan shi kamar a mafarki amma kuma gaske ne, don ni kaina na ga irin fasahar har ma na gwada amfani da ita. Kuma wannan ba wai kawai ga kasar Sin ba, har ma ga sauran duniya, ta kasance wata sabuwar kofar ilimin kirkire-kirkire.
Sashen ayyukan jigila shi ma zai taka rawa sosai. Wannan sashe yana kara samun tagomashi. A shekarar 2025, sashen ayyukan jigila a bangaren shigo da kaya da fitar da su, ya kunshi jimillar kudin da ta kai CNY tiriliyan 8. Wannan sashe dake samun ci gaba cikin hanzari, yana kawo sabon kuzari ga tsarin samar da kayayyaki na duniya da kuma kara nuna wa duniya yadda kasuwar kasar Sin take kara gawurta da zama mai budaddiyar kofa tare da kara hadewa da sassan kasa da kasa. Ko kwanan baya, an yi wani salo mai taken “sayayya a kasar Sin” ta yadda ake iya sayen kayayyaki kai-tsaye a kasar Sin tare da biyan kudi nan take, da kuma jigilar da abin aka saya cikin sauki. Kana da ba da taimako ga masu sayayya idan suna bukatar hakan bayan sayayya.
Wadannan abubuwa da na kawo wasu ne daga cikin muhimman ginshikai da za su taka rawa ga karfafa ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a lokacin aiwatar da shirin na shekaru biyar-biyar da ya fara daga bana zuwa 2030, kana a ta fuska mai fadi, za su kara ba da tabbaci tare da karfafa tsarin samar da kayayyaki a duniya baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














