ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata Sabuwa…

by CMG Hausa
4 years ago
Wata Sabuwa

A yayin da duniya ke fuskantar manyan sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba cikin karni, gami da kalubalen annobar COVID-19 da har yanzu ke yaduwa a sassan duniya, a hannu guda masana sun yi gargadi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya. Wai ana kukan targade sai ga karaya.” 

Kwararru sun sha fadawa shugabannin kasashen duniya a lokuta daban-daban, kafin ma cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu saboda wasu dalilai. Kuma yanzu haka, ana fuskantar wannan matsala a yankin kahon Afirka, da ma wasu sassan duniya.

  • Ya Dace A Hukunta Ta’Addancin Da Birtaniya Da Amurka Suka Aikata A Afghanistan

Saboda girman wannan matsala, ofishin kula da harkokin jin kai na MDD (OCHA) ya yi kira da a gaggauta samar da karin kudade, domin tunkarar matsalolin jin kai dake karuwa a yankin kahon Afrika, yayin da yankin ke tsaka da fama da fari. Inda ya yi gargadin cikin rahotonsa na baya-bayan nan da ya fitar a Nairobin Kenya cewa, za a yi asarar rayuka idan ba a samar da karin kudaden ba.

ADVERTISEMENT

Bayanai na cewa, mutane a yankin kahon Afrika, wadanda ke fama da fari mafi muni da aka gani cikin shekaru 40 da suka gabata, na fuskantar barazanar yunwa, biyo bayan rashin ruwa a damina 4 a jere, a wasu sassan kasashen Habasha da Kenya da Somalia.

Rahoton ya ce, hasashe na nuna cewa, akwai yiwuwar ba za a samu ruwan sama a lokacin damina na bana tsakanin watan Oktoba da Disamba ba, lamarin da zai haifar da iftila’in da ba a taba gani ba. A don haka, akwai bukatar daukar mataki nan take, domin kare matsalolin da ka iya faruwa a watannin dake tafe.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Masu lura da al’amuran yau da kullum na cewa, akwai makaurata sama da miliyan 6 da ‘yan gudun hijira fiye da miliyan 3 a yankin kahon Afirka.

Haka kuma akwai wasu miliyoyin al’umma wadanda suke cikin akuba sakamakon bala’un ambaliyar ruwa ko fari. Wannan ita ce aljannar Waina, sama zafi kasa zafi”. Ga matsalar COVID-19, ga kuma wasu matsaloli dake kara kunno kai.

Abun da ya fi muhimmanci yanzu shi ne, ci gaba da tallafawa irin wadannan mutane da suka shiga irin wadannan matsaloli.

Baya ga yadda yaduwar annobar COVID-19 ke haifar da kalubale ga gwamnatocin kasashe daban-daban daga dukkan fannoni, wato daga bangaren lafiyar al’umma, zuwa kawar da talauci da samar da guraban ayyukan yi da isasshen abinci. (Ibrahim Yaya)

Wata Sabuwa
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
‘Yansanda Sun Cafke Wanda Ya Dirka Wa Agolarsa Ciki A Ekiti

'Yansanda Sun Cafke Wanda Ya Dirka Wa Agolarsa Ciki A Ekiti

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.