ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wike Ya Umarci Rushe Maɓoyar Masu Laifi A Abuja

by El-Zaharadeen Umar
1 month ago
wike

Ministan Abuja Nyesom Wike ya bada umarnin gaggawa na rushe duk wani wuri da ake zargin maɓoyar masu laifi ce a gundumar Karmajiji da ke yankin Kukwaba a Abuja, inda ya bayyana wurare a matsayin inda masu aikata laifin ke ɓoyewa a babban birnin tarayya.

Ministan ya bada wannan umarni ne a makon da ya gabata a lokacin da ya kai ziyara a wasu wuraren zama ba bisa ƙa’ida ba tare da rakiyar jami’an tsaro jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin tsaro a ƙoƙarin sa na karfafa tsaro a birnin tarayya Abuja

A cewar sa, bayanan sirri sun gano wasu wurare da ake zargin sun zama maɓoya ga masu aikata laifuffuka bayan kai wasu hare-hare a wurare daban-daban a Abuja

ADVERTISEMENT

Ya kuma bayyana irin waɗannan wurare a matsayin babbar barazanar tsaro, sai dai ya ce a ƙarƙashin kulawarsa irin waɗannan wurare ba za su  taɓa sha ba, zai kauda su.

“Duba wannan wuri, ba zaka iya sanin wa yake zama ba, ta ya ya zamu iya gano su? Ta ina zamu gano inda suke?  yanzu wannan daidai ne a cikin birnin irin Abuja? Wannan tamkar muna kan wata nakiya ce, ta inda babu wata hanya da zamu kyale wannan abu ya cigaba da faruwa. Shugabancin birnin tarayya Abuja ba zai taɓa kyale masu laifi su zauna lafiya ba” inji shi

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Haka kuma ministan ya baiwa  ɓangaren lura da  cigaba umarni da ya gaggauta rushe duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba sannan su yi  aikin tare  kwamishinan ƴan sanda na birnin tarayya Abuja, Ahmad Sunusi tare da sauran hukumomin tsaro

Ya ce wannan aikin na daga cikin abubuwan da shugabancin da ya sanya gaba, na kauda duk wata barazanar tsaro tare da maido da zaman lafiya  da aminci a cikin birnin tarayya Abuja.

Kazalika minista Wike ya yi gargaɗi  jama’ar da ke bada wurare ana amfani  da gine-gine ba bisa ƙa’ida ba, zai sanya ƙafar wando ɗaya da su kamar yadda doka ta tanada.

Ya kuma ƙara tabbatar da jajircewar  shugabancin sa na cigaba da lura da sa ido akan sha’anin tsaro a faɗin abuja tare da kare rayuka da dukiyoyi a matsayin abu mai mahimmanci da ya sanya gaba

Nyesom Wike ya ce shugabancin sa zai cigaba da gano irin waɗannan wurare tare da rushe su domin kauda barazanar tsaro a zukatan al’umma, ta hanyar aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin a tabbatar  Abuja ta samu tsaro da amince ga al’ummar da ke zaune a cikin ta

wike
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda

MASU ALAKA

Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Next Post
Ga Yadda Fasahar AI Ta Sin Ke Amfanar Da Al’ummar Afirka A Rayuwar Yau Da Kullum

Ga Yadda Fasahar AI Ta Sin Ke Amfanar Da Al'ummar Afirka A Rayuwar Yau Da Kullum

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.