A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wa shugaban Colombia Abelardo de la Espriella sakon ta’aziyya a kan girgizar kasa mai karfi da ta afka wa kasar.
Xi ya bayyana cewa, yana matukar alhini da jin labarin girgizar kasa mai karfi da ta auku a kasar Colombia, wadda ta janyo hasarar rayuka da raunata mutane masu yawa, da kuma munanan asarorin dukiya.
A madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, ya yi ta’aziyya game da wadanda suka rasa rayukansu, da kuma nuna jajantawa cikin sahihiyar zuciya ga iyalan wadanda suka ji raunuka.
A cewarsa, ya yi imanin cewa, a karkashin jagorancin gwamnatin kasar Colombia da shugaba de la Espriella ke shugabanta, al’ummar kasar za su hada kai, don shawo kan wannan ibtila’i da wuri, da kuma sake gina kasarsu. (Bilkisu Xin)














