ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaƙin Iran: Taƙaddama Ta Kaure Tsakanin Trump Da Pope Leo

by Sani Anwar
5 months ago

Fafaroma Leo, ya mayar da martani bayan Donald Trump ya kira shi a matsayin mutum mai rauni, saboda sukar yaƙin Iran da ya yi.

Fafaroma na Katolika, ya bayyana a ranar Litinin 13 ga Afrilu cewa; ya ɗaura ɗamarar shirin ci gaba da yin tsokaci a kan wannan yaƙi, bayan shugaban Amurka Donald Trump ya soke shi kai tsaye.

  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

A cikin tsokaci kan jirgin Fafaroma zuwa Algiers, inda Fafaroma na farko na Amurka ya fara rangadin kwana 10 zuwa ƙasashen Afirka huɗu, Fafaroma ya kuma ce ana cin zarafin Kiristoci.

ADVERTISEMENT

“Ba na son shiga muhawara da shi,” Leo ya ce; yayin da yake gaishe da ƴan jarida a cikin jirgin.

“Ba na jin cewa, ana son a ci zarafin saƙon bushara kamar yadda wasu suke yi.”

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Da yake magana da wasu manema labarai, Fafaroma Leo ya ƙara da cewa, “Ba na jin tsoron gwamnatin Trump ko yin magana da babbar murya game da saƙon Linjila, wanda Cocin ke aiki dominsa.”

“Mu ba ƴan siyasa ba ne, sannan mu ba ma kallon manufofin ƙasashen waje ta irin yadda za su kasance,” in ji Paparoma, ya ƙara da cewa; “Zan ci gaba da amfani da kakkausar murya a kan wannan yaƙi tare da neman inganta zaman lafiya da tattaunawa da kuma haɗin kai a tsakanin ƙasashe, domin nemo hanyoyin warware matsaloli.”

“Mutane da dama na shan wahala a duniya a yau,” in ji Leo. “Ana kashe mutane da yawa waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba. Don haka, ina ganin ya zama wajibi mu yi magana.”

Leo, wanda ɗan asalin Chicago ne, ya fito a matsayin mai sukar yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran a makwannin baya-bayan nan, sannan kuma ya yi tir da yaƙin a wani roƙon zaman lafiya da aka yi ranar Asabar.

Trump, a wani martani da ya fito fili ga sukar Fafaroman game da rikice-rikice da kuma manufofin shige da fice na fadar White House, ya faɗa a yammacin ranar Lahadi cewa, Leo ya haɗari ne.

“Fafaroma Leo yana da rauni a kan laifuka, sannan kuma yana da haɗari ga manufofin ƙasashen waje,” Trump ya rubuta a cikin wani saƙo da aka wallafa a kafafen sadarwa.

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Tawagar ‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-21 Sun Kammala Aikin Tattaki Karo Na 3 a Wajen Tashar Binciken Sararin Samaniya Cikin Nasara

Tawagar 'Yan Sama Jannatin Shenzhou-21 Sun Kammala Aikin Tattaki Karo Na 3 a Wajen Tashar Binciken Sararin Samaniya Cikin Nasara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.