Tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Ehiozuwa J. Agbonayinma, ya bukaci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC da ta sake buɗe wani tsohon bincike kan zargin aikata laifukan kuɗi da ya shafi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar. Ya ce buƙatar ta samo asali ne daga wani rahoton EFCC na shekarar 2006.
A cikin wata takarda mai kwanan wata 27 ga Agusta 2026, wadda lauyoyinsa suka aika wa shugaban EFCC, Agbonayinma ya buƙaci a sake duba rahoton hukumar na 2006 da kuma wani rahoton Kwamitin Bincike na Majalisar Dattawan Amurka na shekarar 2010. Ya ba hukumar wa’adin kwanaki 14, yana mai cewa idan ba ta ɗauki mataki ba, zai iya fara shari’a a kansa.
Agbonayinma ya yi iƙirarin cewa binciken da EFCC ta gudanar tsakanin 2005 zuwa 2006 ya ƙunshi zarge-zargen cin hanci, da safarar kuɗaɗe da wasu laifukan kuɗi da ake dangantawa da Atiku. Ya ce a lokacin da yake kan muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, kariyar kundin tsarin mulki ta hana gurfanar da shi, amma a ganinsa wannan kariyar bai kamata ta ci gaba da hana binciken ko gurfanar da shi bayan barin ofis ba.
Sai dai Atiku ya yi watsi da wannan mataki, yana mai cewa sake dawo da zarge-zargen da suka shafe kusan shekaru 20 alama ce ta yadda abokan hamayyarsa suka kasa kare matsalolin tattalin arziƙin ƙasar.
Ya ce an riga an binciki waɗannan batutuwa a lokacin gwamnatin shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, inda lamarin ya kai ga EFCC, da wasu kwamitoci, da Majalisar Tarayya da kotuna, amma ba a taɓa samun hukuncin kotu da ya same shi da laifi kan waɗannan zarge-zargen ba.
Atiku ya ƙalubalanci duk wanda ke da sahihiyar hujja a kansa da ya gabatar da ita a gaban doka, yana mai cewa “takardar koke ba hukunci ba ce, kuma karɓar takarda ba hujjar aikata laifi ba ce.” Ya kuma ce EFCC hukuma ce ta Nijeriya, ba ta wata jam’iyya ko ɗan siyasa ba, don haka bai kamata a yi amfani da ita a matsayin makamin siyasa ba, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.














