ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Alƙur’ani Ya Dace Da Kimiyya Da Fasahar Ƙarni Na 21 (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
5 months ago
Kimiyya

Duk Kungiyar Da Ta Tilasta Bin Addini Ba Za Ta Yi Nasara Ba Mai Diwani ya bayyana cewa, duba da cewa, “rana tana kashe wasu kwari, hakan ba zai sanya a ce a daina amfani da ita ba”, wannan misali ne da ke nuna cewa, wannan zamanin da muke ciki, yana tattare da abubuwa masu amfani da yawa amma kuma yana da irin na shi kalubalen.

Wannan zamani na intarnet, wanda ke dauke da kafofin sada zumunta (Facebook, Tiktok, YouTube, Ɗ,…) masu yawa da ake yada ilimi mai kyau da akasin haka, ya dace, al’umma ta iya fayyace ilimi mai kyau da ke ciki domin amfanin kanta, sannan ta guji tasirantuwa da ilimin da bai dace da ita ba domin kiyaye martabarta.

  • Ramadan: Shehu Ismaila Ya Buɗe Tafsirin Alƙur’ani A Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Kaduna 
  • Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa, Ya Kamata Maulidin Baɗi Ya Zama Na Musamman – Sheikh Mai Diwani

Wannan kafofin sada zumunta, ba haka nan kawai suke ba, duk abin da ka aikata ko ka rubuta, tabbas ana bibiya, don haka, ya dace kowa ya yi amfani da su ta hanyar da ya dace domin neman ilimi.

ADVERTISEMENT

Almadda, ya yi karin haske da cewa, duk wanda ya yi da’awar yaki da sunan Addini (Musulunci ko Kiristanci), ba zai yi nasara ba, sabida ba a tilasta wa zuciya karbar abin da bata fahimta ba, domin wata rana, yaudara da ha’inci za ta shiga, kuma duk ranar da ta samu ƴanci zata gudu. Mafi yawancin wadanda Musulunci yasha wahalar su, su ne wadanda suka amshi Musulunci a ranar Fathu Makkah, sabida kusan dole ce ta sanya suka karɓi Musulunci.

Zamanin daular Abbasawa ta Musulunci a lokacin itace ke da karfi, tarihi ya tabbatar da cewa, ta yi amfani da karfi wajen tilasta shiga Musulunci da kuma yi wa gwamnatinta mubaya’a ta dole, hakan na nuna cewa, Fikihun zamaninsu ya sauya fahimtar addinin da Annabi SAW ya zo da shi. Don haka, mu duba tarihi muga yadda Allah ya yi da ita.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Daga cikin mabiya addinin Kiristanci, an taba yin wata tawaga dake yaki akan dole sai an bi addininsu, daga karshe, har shugabansu sai da aka kashe bayan an haramta duk wani abu da ya shafi tawagar.

Ya dace musulmai su wanke kwakwalwarsu daga batun “Haram”, da “Halal”, da batun cewa, komai sai an koma zamanin sahabbai an gano yaya suka yi rayuwa, wancan zamanin daban, wannan zamanin daban. Wannan tsarin, ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Musulmai baya a wannan zamanin, ta yadda suka kasa fahimtar zamanin su wajen kawo abubuwan cigaba na ilimi.

 

Mu Kula Da Kyawawan Dabi’u, Su Ne Waɗanda Annabi SAW Ya Kira Duk Halitta Akansu.

Kyawawan dabi’u, sune wadanda ke hada duk halitta, sune doka da za su zaunar da kowa lafiya, sabida sune hankali. In danAdam ya yi kure akansu, sai kaji ana cewa, “wane ba shi da hankali”.

Don haka, shi addini ba shi da kayan dole, ba shi da bulala ko takobin dole, ƴanci kawai yake so, sabida abu ne na zuciya, “la ikraha fiddin – ba dole acikin addini”, in baka bai wa zuciya dama ta karbi abu da kanta ba, to ka kera wa kanka “munafuki”, da zarar ya samu dama, zai gudu, amma in aka bata dama, ta karbi addini da kanta, to babu fargabar wata rana za ta gudu.

Musulunci ya fara samun kalubale ne a Fathu Makkata, yayin da Kuraishawa suka karbi addinin ba cikin son ransu ba. An ga haka, a yayin yakin Hunaini wanda Annabi SAW ya tafi jim kadan bayan Fathu Makkata, bayan ya samu labari cewa, kusan soja dubu talatin (30,000) sun taru a Hunain suna shirin kawo masa hari.

Ruwaya ta zo da cewa, Annabi SAW yazo Fathu Makkata da soja dubu 8 ko dubu 10, sannan ya kara da soja dubu 2 daga Makkah inda jimillar adadin sojan ya kama dubu 10 ko dubu 12, ana fara gwabza yaki, wannan mutanen na Makkah suka gudu, wanda hakan ya yi sanadin tarwatsewar sauran tawagar rundunar Annabi SAW, har sai da matayen mutanen Madina suka taso suka tarbi mazajensu da cewa, yaushe kuka fara guduwa ku bar Annabi SAW a filin yaki shi kadai? Ta kaka za ku biyewa wadanda suka shiga addini ba da zuciya daya ba!

A nan take, aka fahimci cewa, mutanen Makkah, ba da zuciya suka shiga addini ba, da jiki suka shiga.

 

Kar Kayi Magana Akan Abin da Baka Da Ilimi Akansa

Mai Diwani ya lissafo kyawawan dabi’u 10 wanda duk addinatai kusan suna kansu, sannan ya karo da wasu uku da suke gargadi.

Haram-haram guda 10 akan Muminai mabiya Annabi SAW, wadanda sun yi daidai a littafin Annabi Musa (AS), sun yi daidai da hikima ta Annabi Isah (AS), kuma sune hikima ta Lukmanal hakim:

Kar mu tara Allah da wani, kar mu kashe ‘yaƴanmu don tsoron talauci, kar mu kusanci alfasha daga abin da ya bayyana da wanda ya buya, kar mu kashe rai wacce Allah ya hana, kar mu kusanci dukiyar maraya sai da abin da yafi kyau, mu cika ma’auni, mu yi adalci a wurin magana, mu fadi gaskiya ko da akan abokanmu ne, mu cikawa Allah alkawari, sannan mu bi hanyar Ubangiji.

Wannan abubuwan da muka lissafo guda 10, kusan duk addinatai akansu suke babu saɓani, sai dai suratul Isra’i ta kara wasu guda Uku:

– Ciyarwa: ya dace mai hali ya taimaki abokin shi mabukaci, da nakasasshe da ƴan gudun hijira.

– Kar ka yi magana akan abin da baka da ilimi akansa. Ba ka da ilimi akan siyasa, ka yi shiru, ba kada ilimi akan kasuwanci, to shiru ya fi amfani.

– Kar ka yi girman kai. Wadannan abubuwan da aka lissafo, suna daga cikin hikima ta ubangiji da ya yi wahayi a gareka ya Rasulallahi.

Mumini Dole Ya Bi Direban Da Ya San Hanya Kuma Ya San Dokokin Tafiya (Shehi Masani)

Mai Diwani, ya cigaba da karatu game da yadda Suratul Furƙan, ta lissafo kyawawan dabi’u, duk da cewa na kowa ne amma sun fi karfi akan Muminai ba gama garin Musulmai ba.

Ya dace ga Mumini ya yi tafiya sannu-sannu, ya bi dokokin hanya kamar yadda ake alamtawa akan manyan hanyoyi domin kiyaye haddura. Kamar yadda hakan yake a tafiyar zahiri, kuma haka yake a tafiyar ruhi. Mumini, dole ya bi direban da ya san hanya kuma wanda ya san dokokin tafiya (Shehi masani), wanda zai nuna masa yadda ake tafiya kan lamarin ubangiji, tun daga:

– Attakwa ta Islam: Attaubatu, Al’istiƙamatu, da Attakwa.

– Attakwa ta Imani: Assidku, Al’iklas, da Addumaninatu.

– Attakwa ta Ihsani: Almurakaba, Almushahada, da Alma’arifa.

Daga nan, ya cigaba da tafiya har ila masha Allah.

Don haka, sufanci fanni ne da yake a tsare, duk wanda ya ara ya yafa, sai kaga cakudi a lamarin shi. Sabida komai a rubuce yake kamar yadda aka rubuta duk alamomin hanya, misalin in kana tafiya zuwa wani gari, za ka riƙa ganin dokokin hanya a rubuce a bakin hanya, kamar tsarin yadda ake son direba ya yi gudu ko ya rage gudu, hanya samɓal ce ko akwai kwana, an kusa zuwa cikin gari ko an fita daga gari, wurin tsallakwar mutane ne nan ko dabbobi, da sauransu dai. Kamar yadda aka gindaya wannan sharuɗan a tafiyar zahiri, haka yake a tafiyar ruhi, da faɗin ubangiji, “wa ibadurRahmanillazina yamshuna alal ardi haunan…”

Har ila yau, Suratu Furkan ta yi kira ga Malamai su iya zama da wadanda ba su da ilimi, don su (malaman) zauna lafiya.

Sannan ta jaddada muhimmancin zaman lafiya, da kokari ga yin addu’a

Kimiyya
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
EFCC Ta Bankaɗo Makarantar Koyar Da Damfara A Intanet A Abuja, Ta Kama Mutane 31

EFCC Ta Bankaɗo Makarantar Koyar Da Damfara A Intanet A Abuja, Ta Kama Mutane 31

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.