ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda FIFA Ta Yi Yunƙurin Sasanta Rikicin Israila Da Amurka A Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada
4 weeks ago
Duniya

Gianni Infantino, shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya, wanda yake fuskantar matsin lamba ya musanta wasu manya-manyan zarge-zarge da aka samu lokacin wasan kofin duniya tare da yaba wa Iran kan halartar gasar duk da rikicin da ke tsakaninta da ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi wato Amurka.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Istagram wanda FIFA ta ƙara turawa mutum miliyan takwas da ke binta – Infantino ya yi bayani ga waɗanda suka laɓe suna ta rubutu a bayan fage suna sukar su, maimakon yin abin da ya kamata.

Infantino ya shawarci masu suka da su mayar da hankalinsu kan ƙwallon ƙafa su ji daɗin wasannin da ake yi ba su riƙa yaɗa jita-jita ba kan shugabancinsa da FIFA game da Gasar Kofin Duniya.

ADVERTISEMENT

Ya ce gasar Kofin Duniya ta “nuna mutuntaka da matuƙar matsayi” yana cewa gasar 2026 “ta samar da tsaro da kwanciyar hankali, farin ciki da murna ga masu bibiyarta.

Ya ce FIFA ta yi ƙoƙari ba dare ba rana ta haɗa kan ƙasashe biyu da ke yaƙi da juna, kuma Iran ta shiga ƙasar wasa ba tare da wani rikici ba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Bayanan sa sun ci karo da na kocin Iran Amir Ghalenoei, wanda ya ce “tawagarsa ce wadda ta fi shan wuya” a gasar Kofin Duniya. A gasar ta kofin duniya dai an hana Iran biza a kan lokaci an kuma hana wasu jagororin da suke horar da tawagar biza baki ɗaya, wasu magoya bayan da suka sayi tikitinsu duka an ƙwace, kuma an tilsata wa Iran barin inda aka tanadar mata domin atisaye a Tucson a Arizona zuwa Tijuna da ke Meɗico.

Daga baya kuma suka fuskanci tsaiko na hana tafiya tsakanin wurin atisayensu da kuma inda suke wasa. Ba iya Iran ce ta fuskanci wannan matsalar ba, magoya bayan Haiti da na Senegal da na Iɓory Coast su ma hana tafiye-tafiyen da gwamnatin Trump ta yi ya shafe su.

A gefe ɗaya kuma alƙalin wasan Somaliya Omar Artan an hana shi bizar shiga Amurka – duk da cewa yana da fasfon diflomasiyya da bizar shiga Amurka falle guda – saboda ana zargin sa da alaƙa da wata ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya.

Infantino ya rubuta cewa mutane suna ta cewa an hana wasu mutane ƙalilan biza yayin da aka bai wa miliyoyi, daga sassa daban-daban na duniya. Saboda ƙwallon ƙafa na haɗa kan duniya, kuma sun ga hakan a aikace a wannan gasar.

Bugu da ƙari, FIFA na bincike kan rikicin Argentina da aka samu wasu masu taimakawa kocinsu da hannu ciki, yayin wasansu na ƙarshe da Sifaniya. Tana kuma bincike kan shahararren mai amfani da kafafen sada zumuntar nan ɗan Amurka Darren Jason Watkins Jr. da aka fi sani da IShowSpeed – yayin da aka kama magoya baya da yawa a wasanni daban-daban – ciki har da wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Ingila da Argentina.

An shigo da jami’an kwastam da na masu kula da shige da ficen filin wasa, wani abu da ya riƙa haifar da ruɗani. Infantino ya kuma yi magana kan sukar da aka riƙa yi musu game da yadda alƙalan wasa suka yi busar gasar, musamman kan yadda aka samu tasirin siyasa da shugaba Amurka ya yi magana kan ɗan wasan gabanta Folarin Balogun da ya buga wasan matakin ƴan 16 – bayan an dakatar da shi wasa ɗaya.

A cikin jan kati 191 da aka bayar a gasar kofin duniya ɗaya ne kawai ya taɓa tsallake dakatarwa. UEFA ta ce matakin ya wuce na jan kati inda ta bayyana shi a matsayin abin da ba a yi tsammani ba, da babu dalilin yin sa, a gefe ɗaya kuma hukumar ƙwallon ƙafa ta Norway za ta shigar da ƙara a hukumance kan karya dokar wasannin.

Bayan an kammala gasar da yamma Infantino ya yi taron manema labarai karon farko cikin shekaru uku – yayin da yake cewa masu suka su ci gaba da shanawa da hutawa. Wataƙila idan aka sake haɗa wata gasar sai su haɗa su ci gaba da ƙorafi bayan nan zai haɗa ya ba su amsa.

Duniya
Abba Ibrahim Wada
+ postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Har Yanzu Nijeriya Tana Fatan Zuwa Kofin Duniya Na 2026
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Mece Ce Matsalar Real Madrid? 
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Duniya

Mutane 6 Sun Jikkata Bayan Harbe-Harbe Yayin Yaƙin Neman Zaɓen NDC A Delta

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.