ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
3 months ago
matasa

Ga matasa masu sha’awar tsayawa takara a matakai daban- daban na siyasa  lokacin zabubbukan shekara 2027, babbar matsalar da a yanzu suke fuskanta ita ce bata da wata alaƙa da farin jini, ko mutane da yawa sun san mutum, ko ace sun yarda da shi, babbar matsalar ita ce tsada ko yawan kuɗin da mutum zai ba da kafin amince ma shi ya tsaya takarar.

A jami’iyyu da yawa, tsadar kuɗin na tsayawa takarar lamarin da ya kai ga bilyoyin Nairori, bugu da ƙari kuma idan mutum na da wanda ya tsaya ma shi wanda zai kai ga wanda za a kaɗa ma shi ƙuri’a d akuma wanda za a bari da tsintar hula.

Ganawa nasu yawa,takardun jam’iyyar sai kuma masu ruwa da tsaki yadda kuɗaɗensu su ke, kamar yadda binciken Jaridar LEADERSHIP ta ranar Lahadi ya nuna, duk da yake shekarun da aka ɗauka ana ta kai gwauro akai mari na tabbatar da ana tafiya tare da matasa wajen gyaran da ake son kawo wa na tafiya tare da matasa a harkokin siyasa,sai dai kuma yawancin matasa za su ci gaba da fuskantar matsala ne saboda ƙarancin rashin kuɗaɗe, da wasu bambance- bambance da za su ci gaba da fuskanta wajen ƙoƙarin da suke yi na samun damar ta a riƙa tafiyar da su wajen ganin sun cimma burinsu na siyasa, abin kowane lokaci kan kasance mai wahala a gare su.

ADVERTISEMENT

Irin yanayin ne ya sa aka fara shakkun ko shi lamarin siyasar an bar shi ne ga waɗanda suke da irin ƙunbar susa ta siyasa wato kuɗaɗe sai waɗanda suka mallakesu ne har za su samu damar da za a riƙa tafiya da su, bugu da ƙari kuma wa suka sani wa kuma ya tsaya masu dangane da har yadda za su samu ƙahon karo na siyasa.

Har ila yau bincike-binciken da aka yi ya  ƙara nuna ko bayyana yadda ake nuna sha’war tsayawa takara na sayen fom ɗin takara na Shugaban ƙasa, Gwamna, Majalisar Dattawa, da kuma ta Wakilai na tarayya, waɗannan ne nau’oin wahalhalun da mai neman a zabe shi a ɗaya daga cikin muƙaman zai fara fuskanta matuƙar har yana da sha’awar cimma burinsa na siaysa ga su ƴan siyasar.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Hari la yau binciken da Jaridar LEADERSHIP ta ranar Lahadi ta yi ya nuna a cikin shirin da ake yi na zabubbukan shekara ta 2027, babbar jam’iyya mai mulki ta nuna cewa fom ɗin nuna buƙata ta tsayawa takarar Shugaban ƙasa ana sayar da shi ne a Naira miliyan 100.

Mai kuma son tsayawa takarar Gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar shi zai ba da Naira miliyan 50 ne, yayin da mai son takarar Sanata zai biya Naira miliyan 20.

Yayin da mai son tsayawa takarar majalisar Wakilai ta ƙasa zai biya Naira miliyan 10, shi kuma wanda ke son tsayawa takarar majalisar Jiha zai biya Naira miliyan 2 ne kacal.

Haka ita ma jam’iyyar PDP, ta ce Naira miliyan 40 ne kuɗin fom ɗin tsayawa takarar Shugaban ƙasa.

Ga waɗanda suke buƙatar takarar muƙamin Gwamna kuma duk dai a jam’iyyar ta PDP za su ba da wuri na gugar wuri har Naira miliyan 21, masu neman takarar Sanatoci za su biya Naira miliyan 3.5, majalisar Wakilai ta ƙasa Naira miliyan 2.5 ne, yayin da kuma mai son tsayawa takarar ɗan majalisar Jiha zai sayi fom kan Naira 600,000 ne.

Duk da yake ita jam’iyyar ADC lamarin tsarin kuɗaɗen sayen fom ya yi mayuƙar yin ƙasa da na jam’iyyun APC da PDP, wasu matasa da ke sha’awar tsayawa takarar sun ce lamarin buƙatar kuɗaɗen wasu hidomomin da ke tattare da tsayawa takarar ne da dai sauransu, a halin da ake ciki miya mai daɗi sai dai su ji ƙanshin ta a wani gida, maganar takarar a yanzu dai abin ya fi ƙarfinsu sai dai kuma wani ikon Allah zai iya sa lamurran su su samu damar sauyawa.

Ga Muhammadu Indimi ɗan shekara 40, ɗan takara mai son zuwa majalisar Jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyyar ADC zai kuma wakilci mazabar ƙaramar Hukumar Maiduguri ta tsakiyar Birni, yadda kuɗaɗen suke ba kamar na sauarn jam’iyyun ba hakan ya samar da wani sauƙi idan aka kwatanta irin hakan da manyan jam’iyyun siayasa.

Indimi ya bayyanwa Jaridar LEADERSHIP ta ranar Lahadi cewar kuɗin da jam’iyyar ADC ta ƙaiyade na fom ɗin basu zarce Naira miliyan 2.5 ba, wanda ya ce hakan an samu sauƙi idan aka kwatanta da manyan jam’iyyu.

Kamar yadda ya ce, kuɗin da ADC ta ce a biya, idan aka yi la’akari da jam’iyyar APC wanda Naira milyan 6 ne, idan da haka ne ADC yawancin masu ƙaramin ƙarfi kuma suna son tsayawa takara ba za su ji ƙanshin wurin ba.

Ya ce duk da yake dai su jam’iyyun siyasa suna buƙatar kuɗaɗe ne na tafiyar da harkokinsu, yawan kuɗaɗen na sayen da wasu jam’iyyu ke sayarwa abin ta haka ne zai gagari matasa wajen sha’awar da suke ta tsayawa takarar.

Indimi ya ƙara jaddada cewar yawancin matasa ƴan Nijeriya waɗanda suke da alamun kwarjini na al’umma, amma ba su damar ba da maƙudan kuɗaɗen takarar da wasu jam’iyyu suka tsaya kai da fata dole ne sai an biya.

“Da zarar kuɗin sayen fom ya kasance da tsada, waɗanda za su tsaya takarar tamkar an ƙayyade su ne,ba domin kome ba sai saboda rashin kuɗaɗe, don haka ne sai wasu matasa abin ya kasance tamkar an kore su daga sahun ne saboda rashin kuɗi domin kuwa su ne ƙarfin yin ko wace irin hidim, ta duniya kamar yadda ya furta’’.

Yawancin matasan ƴansiyasa waɗanda suka tattauna da Jaridar LEADERSHIP ta Lahadi makon da ya gabata sun ce yadda lamarin siyasar ƙasar yake halin yanzu, abin ya fi taimaka ma waɗanda suke da kuɗi ne suke kuma sha’awar tsaywa takara.

Wasu ma sun yi zargin abin ya wuce lamarin fom ɗin takara, yawancin kuɗaɗen da ake kashewa waɗanda ba kan ƙa’ida suke ba aka kuma kusanta su da lamarin tuntuba, yadda za samarwa mutum magoya baya da kuma wakilai yadda za a samo su, hakan ma ya ƙara yawan kuɗaɗen da za a yi amafani da su.

Kamar yadda suka ce, yawancin matasan ƴan siyasa da suke da sha’awar tsayawa takara yanzu suna neman wanda zai ɗauki ɗawainiyarsu daga ubangida na siyasa, ko kuma  hankali kwance su manta da ƙudurinsu na son tsayawa takara.

Ɗaya daga cikin waɗanda suke da sha’awar tsayawa takara da abin ya shafa Oronsanyo Robert Uyi, ɗan shekara 44 daga Jihar, Edo, ya ce tun farko ya shirya zai tsaya takara ta ɗan Majalisar Wakilai ta tarayya mazabar Obia a ƙarƙashin jam’iyyar ta gwamnatin APC.

Uyi ya shaida wa LEADERSHIP Lahadi cewar dalilin sa neman ya tsaya takara shi ne shi ma yana sha’awar ba da tashi gudunmawar tafiyar da Gwamnati, ya kuma nuna cewa su ma matasa suna da irin gudunmawar da za su bayar.

Sai dai kuma ya fahimci, kanar darasin da ya koya kan lamarin siyasa ya gane yadda lamarin kuɗi da yadda ake tafiyar da ita siyasar na daga cikin abubuwan da suke damuwar yawancin waɗanda suke da buƙatar tsayawa takara.

Kamar yadda ya ce,bayan ya gama da irin siyasar cikin gida yadda take, ga kuma maganar kuɗaɗen da ake sa ran ɗan takara zai bada domi ya samu ayi tafiyar da shi, amma daga baya ya koma jam’iyyar NDC, saboda shi a nashi tunanin ƙananan jam’iyyun siyasa irin su ne za su iya ba da dama takara ga matasan ƴan siyasa masu tasowa.

Amma sai ya ce lamarin bai tsaya a can ba. Uyi ya ce duk da yake ya sauya jam’iyyar siyasa, dukkan irin kuɗaɗen da aka buƙace shi ya ba a waɗancan jam’iyyun, har yanzu bata canza dame ba duk Kanwar ja ce.

Darussan da ya koya su suka ba shi dama ta yanke shawarar ya kamata ma ya tsaya takarar.

“Ana so da matsawa matasa shiga lamarin siyasa a riƙa damawa da sai dai kuma kash! hanyar da za su bi ta zuwa ca sai mutum yana da kuɗi da kuma wanene ya tsaya ma shi  kamar yadda ya ce,”.

Kamar yadda Uyi ya ce, matsalar da matasan ƴan siyasa suke fuskanta ba wai b aba su iya magana bane ko babu da irin dabarar sanin abinda ya dace su faɗa ba, amma yawan kuɗin takarar ce yake kada masu gaba.

Ya ce sai dai kawai idan su jam’iyyun siyasa da kansu ba tare da wani ya ce su yi hakan ba, sun rage kuɗin takarar da kuma wasu hidindimun da ake yi, da kuma siyasar cikin gida , yawancin matasan da suka cancanci tsayawa takara za su kasance a wata duniya ta duhun siyasa.

Masu fashin baƙi kan lamarin siyasa sun ce irin wancan tunanin yana nuna ko shi lamarin siyasar a halin yanzu an bar wa masu kuɗi tafiyar da ita ne maimakon suna da abubuwan da za su faɗa amma an tsaya don kuɗi ne.

Dakta Christian Okeke, da ya karanci kimiyyar siyasa  ya na kuma koyarwa a Jami’ar Nnamdi Azikiwe shi cewa ya yi, babbar matsalar da matasan ƴan siyasa suke fuskanta abin ya wuce shekarun mutum nawa ko wata iya magana ba, amma abin yafi nasaba ne tsarin yadda tattalin arziki take.

matasa
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi
matasa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Turkiyya Ta Zama Ƙasa Ta Biyu Da Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya

Turkiyya Ta Zama Ƙasa Ta Biyu Da Ta Fice Daga Gasar Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.