A Arewacin Nijeriya, akwai ɗimbin mata da rayuwarsu ta sauya bakiɗaya bayan haihuwa saboda gagarumar matsalar da ta baƙunce su da hana masu sukuni tare da zama babban ƙalubale ga lafiyar su da barazana ga auren su.
Matan da lamarin ya shafa ba wai sun shiga halin ƙunci ne saboda sun rasa abin da suka haifa kawai ba, sai dai domin wasu daga cikinsu sun tashi daga gadon haihuwa da gawurtacciyar matsalar da ba su iya ɓoyewa wadda fitsari ke zuba ba ƙaƙƙautawa ba dare ba rana ba tare da sun iya sarrafa shi ba.
Wannan ba wata cuta ba ce face cutar yoyon fitsari wadda masana suka bayyana a matsayin wata kafa mara kyau da ke samuwa tsakanin mafitsara da farji, lamarin da ke haifar da zubar fitsari ba tare da ikon tsayar da shi ba wanda tuni ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka shaifi lafiyar mata masu juna biyu a Arewacin Nijeriya.
Galibi cutar yoyon fitsari na da alaƙa da doguwar naƙuda mai toshe hanyar haihuwa, musamman idan mace ba ta samu taimakon ƙwararren ma’aikacin lafiya cikin lokaci ba. Matsalar na iya ƙara tsanani a wasu yankunan karkara, inda rashin isassun cibiyoyin lafiya, ƙarancin ma’aikatan lafiya, nisan asibitoci da jinkirin kai mata masu juna biyu asibiti ke iya hana su samun kulawar da ta dace a lokacin haihuwa.
A wani rahoton bincike da Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) a Nijeriya ta wallafa a 2025, ya ƙiyasta cewa a Nijeriya akwai kimanin mata da ƴan mata 114, 048 da ke fama da cutar yoyon fitsari yayin da ake samun kimanin sabbin mutane 12, 000 da ke kamuwa da cutar a kowace shekara.
Haka ma tsarin dabarun Gwamnatin Tarayya kan kawar da cutar yoyon fitsari ya taɓa ƙiyasta cewar Nijeriya na da kusan mutane 150,000 masu fama da cutar, bugu da ƙari wani bincike ya nuna cewa a Nijeriya fiye da mata 200,000 na iya kasancewa cikin matsalar yoyon fitsari a yayin haihuwa.
Sai dai wannan adad ba lallai ne ya nuna ainihin girman matsalar ba, saboda akwai mata da yawa a yankin Arewa da ba su zuwa asibiti ko kuma ba a gano su ba saboda kunya da tsangwama.
Yoyon fitsari ba kawai matsalar fitsari ba ce, matsala ce da za ta iya shafar lafiyar mace, aurenta, tattalin arzikinta, mutuncinta da matsayinta a cikin al’umma. Lamari mafi muhimmanci shi ne a fahimci cutar yoyon fitsari ba makomar mace ba ce, a na iya yin rigakafinta, a na iya yi mata tiyata, kuma mace na iya komawa cikin al’umma bayan ta samu cikakkiyar kulawa.
Duk da cewa a na iya yin rigakafin cutar kuma a na iya yi mata magani, amma har yanzu ta na ci- gaba da jefa dubban mata a cikin matsanancin ciwo, kunya, wari, kaɗaici, rashin aikin yi da tsangama daga al’umma
Duk da cewa akwai cibiyoyi da shiraruwan tallafawa masu cutar yoyon fitsari musamman yi masu tiyata kyauta a sassan Arewa, samun maganin kyauta ba ya samuwa a kowane lokaci ko a dukkan asibitoci. A lokuta da dama, tallafin Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) da Gidauniyar Kula da Masu Yoyon Fitsari da gwamnatocin jihohi da sauran abokan hulɗa ne ke baiwa marasa lafiyar damar samun tiyata da sauran kulawa ba tare da biyan kuɗi ba.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar a wani bincike da aka gudanar a Sakkwato ya nuna yadda matsalar ta daɗe ta na addabar mata a yankin kamar yadda a binciken mata 361 da aka yi ya gano cewa kashi 82.79 cikin 100 sun samu yoyon fitsari sakamakon doguwar naƙuda.
Haka ma kashi 51.52 cikin 100 suna tsakanin shekaru 15 zuwa 19 wanda hakan ya nuna yadda shekarun mace, girman jiki, shekarun fara haihuwa da samun kulawar haihuwa ke da muhimmiyar rawa wajen kariya daga cutar.
Duka dai wannan binciken na ƙwararrun masana ya nuna kashi, 51.52% na matan da matsalar ta shafa suna tsakanin shekaru 15 zuwa 19, abin da ke nuna haɗarin fara haihuwa da ƙuruciya.
Haka ma Hukumar Kula da Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta ce a Nijeriya akwai sama da mata da ƴan mata miliyan 23 da aka aurar da su tun suna yara, abin da ke ƙara haɗarin fara ɗaukar ciki tun kafin jiki ya isa haihuwa lafiya. Bugu da ƙari UNICEF ta ce a bayanin da ta tattara kusan kashi 50 cikin 100 na matan da suka kai shekaru 20–24 a Arewa- maso- Gabas da Arewa- maso- Yamma sun yi aure ne kafin shekaru 18.
Sai dai a bayyane yake cewar masana ba su kallon yoyon fitsari a matsayin matsalar da ta shafi asibiti kaɗai; a wasu al’ummomin Arewa, matsalar ta na haɗuwa da talauci, rashin ilimi, nisan cibiyoyin lafiya da kuma ikon mace na yanke shawarar zuwa asibiti.
A ra’ayin su hakan na da muhimmanci saboda matsalar ba ta fara ne lokacin da fitsari ya fara zuba ba, a lokuta da dama, tushenta yana iya kasancewa tun lokacin da yarinya ta fara aure ko ɗaukar ciki kafin jikinta ya kai lokacin haihuwa lafiya.
Yankin Arewa na da manyan cibiyoyin da ke aikin magance matsalar cutar yoyon fitsari, daga Borno, Katsina zuwa Sakkwato, Kano, Kaduna da Bauchi amma yawan mata da ke buƙatar kulawa, matsalar samun cikakkun bayanai, ƙarancin ma’aikatan lafiya da kuma abubuwan da ke jawo cutar tun farko na nuna cewa har yanzu akwai babban aiki a gaba.
Fatima Lawal ƴar shekaru 16 ta sha wahala ta tsayin kwanaki uku ta na naƙuda a gida kafin a kai ta asibiti, sai daga baya aka yi mata aikin haihuwa a asibitin ƙwararru da ke Sakkwato amma ta riga ta kamu da cutar yoyon fitsari wanda a kan hakan aka tura ta asibitin Maryam Abacha da ke Sakkwato domin yi mata aiki.
A cewar ta bayan ta shafe watanni a asibitin bayan aikin farko, sannan ta sake zuwa aka yi mata aiki na biyu amma kuma a ƙarshe mijin ta ya sake ta lamarin da ya jefa rayuwar ta a mawuyacin hali a kan abin da ba ta yi tsammani ba.
Ita kuwa Asiya Habu ƴar shekaru wadda ta kamu da yoyon fitsari tun lokacin haihuwarta ta farko bayan ta shafe fiye da kwana biyu ta na naƙuda a gida, ta ce a lokacin da aka kai ta asibitin Murtala da ke Kano, ta haifi jaririn da bai zo da rai ba kuma an gano cewa ta kamu da cutar yoyon fitsari.
Asiya ta bayyana cewar ta warke bayan tiyatar farko, amma lokacin da ta sake samun ciki, iyayenta da mijinta suka matsa mata ta sake haihuwa a gida tare da taimakon ungozomar gargajiya a inda ta sake shafe sama da sa’o’i 24 ta na naƙuda, ta kuma sake samun yoyon fitsari, abin jimami kuma ta rasa jaririn.
Haka ma Maimuna Adamu, mai shekaru 25 daga jihar Neja, ta ce ta kamu da yoyon fitsari da bayan gida a shekarar 2021 bayan doguwar naƙuda da ta kai ga mutuwar tagwayen da take ɗauke da su kuma mijinta ya rabu da ita daga baya, lamarin da ya tilasta mata dogaro da iyayenta wajen rayuwa.
Asibitin Mata da Ƙananan Yara ta Maryam Abacha da ke Sakkwato na daga cikin muhimman asibitocin da ke bayar da kulawar musamman ga mata masu matsaloliin cutar yoyon fitsari, hasalima wani binciken kimiyya da aka gudanar a asibitin ya bayyana cewa ayyukan kula da masu cutar kyauta ne kuma cibiyar na samun tallafi daga ƙungiyoyi da abokan hulɗa.
A wani bincike da asibitin ta gudanar kan marasa lafiya 130 ya nuna cewa kashi 27 cikin 100 sun rabu da mazajensu ko kuma an sake su saboda yoyon fitsari da suke yi a yayin da kashi 85 cikin 100 na waɗanda aka bincika suna da alaƙa da doguwar naƙuda.
A 2025 Gwamnatin Tarayya ta assasa shirin musamman na yi wa mata masu fama da matsalar yoyon fitsari aiki kyauta a cibiyoyi 18 a faɗin ƙasa domin sauƙaƙa masu kamar yadda Ministan Lafiya ya bayyana.
Haka ma wakilin mu ya labarto cewar Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya na aiki tare da hukumomin gwamnati da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, ciki har da Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) wajen magance matsalar yoyon fitsari a Nijeriya.
Ƙoƙarin kamar yadda Minstar Lamurran Mata, Iman Sulaiman Ibrahim ta bayyana ya mayar da hankali ne kan samar da tiyatar magance yoyon fitsari, horas da likitocin da suka ƙware wajen yin tiyata da kuma tallafawa matan da suka tsira daga cutar ta fuskar tattalin arziki domin su samu damar komawa cikin al’umma.
Ma’aikatar na tallafa wa shirn samar da tiyatar gyaran yoyon fitsari kyauta, bayar da tallafi, ciki har da shiraruwa a yankunan da ake gudanarwa domin taimakawa ɗimbin mata da ke fama da matsalar.
Haka kuma, a na tallafawa shiraruwan horas da likitocin tiyatar yoyon fitsari a cibiyoyin kiwon lafiya na musamman da aka ware a sassan Nijeriya, domin ƙara yawan ƙwararrun da za su riƙa kula da masu fama da cutar.
Baya ga magani, shirin ya kuma ƙunshi tallafin kuɗi, koyar da sana’o’i da taimakon sake shigar da mata cikin al’umma, domin taimaka masu su shawo kan ƙyamar da suke fuskanta tare da sake gina rayuwarsu bayan sun warke.
A lokaci zuwa lokaci ƙungiyoyin ciki da wajen ƙasa kan bayar da tallafin musamman ga masu cutar yoyon fitsari a cibiyoyin kula da masu lalurar kamar yadda a kwanan Hukumar UNFPA ta bai wa Asibitin Maryam Abacha kayan aikin lafiya domin tallafawa masu fama da cutar.
LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa jagorar tawagar UNFPA a Sakkwato, Dakta Rabi’atu Sageer ce ta hannun ta kayan ga Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Abubakar Wurno, a makon jiya.
A yayin da yake karɓar kayan, Kwamishinan ya bayyana tallafin a matsayin wani babban ci- gaba a ƙoƙarin gwamnatin jihar na ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar mata masu juna biyu da haihuwa lafiya waɗanda za su taimakawa asibitin wajen samar da ingantacciyar kulawa, lafiya da kuma mutunta mutuncin mata masu fama da yoyon fitsarin da ya samo asali daga matsalolin haihuwa.
Da take bayyana hanyoyin da za a bi wajen daƙile matsalar, Dakta A’isha Adamu Buba, ƙwararriyar likitar mata a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Jihar Yobe ta ce yoyon fitsari sakamakon matsalolin haihuwa na daga cikin munanan sakamakon rashin kulawa da lafiyar mata masu juna biyu ke fuskanta.
Ta ce za a iya yin rigakafin cutar ta hanyar tsarin iyali, gano mata masu ciki da ke cikin haɗari tun da wuri, tabbatar da samun ƙwararrun ma’aikatan haihuwa da kuma samar da ayyukan kula da gaggawar haihuwa.
Shi ma Dakta Muhammad- Ado Zakari, Babban Likitan Tiyata a Cibiyar Yoyon Fitsari da ke Asibitin Hajiya Gambo Sawaba da ke Zariya, ya ce matsalar na ci- gaba da zama babban ƙalubale ga lafiyar jama’a da zamantakewar al’umma, musamman tsakanin matan karkara da ke fama da ƙarancin damar samun ingantacciyar kulawar lafiyar mata masu juna biyu.
Likitan ya bayyana yoyon fitsari a matsayin wata kafa mara kyau da ke samuwa tsakanin farji da mafitsara ko dubura, wadda galibi doguwar naƙuda mai toshewa ke haifarwa, lamarin da ke sa mace riƙa zubar da fitsari ko bayan gida ba tare da ikon tsayar da shi ba.
Masana dai na ganin yaƙi da matsalar yoyon fitsari a Arewa ba wai ya kamata ya tsaya ga yi wa mata tiyata bayan cutar ta same su ba, ya kamata ya fara ne tun kafin naƙuda ta hanyar samar da ilimin ƴaƴa mata, rage auren wuri, inganta asibitoci, samar da ƙwararrun ma’aikata da kuma tabbatar da cewa kowace mace ta samu taimakon gaggawa lokacin haihuwa, domin duk wata mace da aka ceta daga yoyon fitsari ba mutum ɗaya kawai aka ceta ba, an ceci iyali, an kare mutunci, kuma an baiwa mata damar ci-gaba da rayuwa cikin ƙoshin lafiya.














