ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kiristocin Arewa Sun Nemi A Yi Ƙidaya Don Gane Mabiya Addinan Da Suka Fi Yawa

by Idris Aliyu Daudawa
4 weeks ago
arewa

Shugaban kiristoci na Arewacin Nijeriya (NCA), Rabaran. Joseph John Hayab, ya yi kira da gwamnatin tarayya da cewar ta shigar da lamarin irin addinin da mutum ya ke yi a tambayoyin ƙidayar jama’ar da za ayi ta ƙasa nan gaba,abinda zai sa ayi hakan shi ne domin a gane waɗanne irin ƙungiyoyin addinai ne suke da nasu goyon baya da yawa.

Hayab  ya ce rashin haƙiƙanin abubuwan da za a dogara da su yawan magoya bayan addini ya sa ana ta wasu maganganun da basu da wata hujja da take nuna wane addini ne ya fi yawan waɗanda suke goyon bayan shi, domin kuwa irin hakan yana ta sa a riƙa tada jijiyar wuya,ga kuma rashin kwanciyar hankalin da zai iya samar da wani lamarin da zai yi wa al’umma daɗi ba.

Ya yi wannan kiran ne ranar Litinin lokacin shirin gidan Talabijin na Channels mai taken tsokacin safe,domin ya maida martini a maganganun da , Sheikh Sani Yahaya Jingir,ya yi inda yake kare lamarin ƴantakara Shugaban ƙasa musulmi da musulmi, saboda kwai la’akari da yadda yawan musulmi ya ke, da kuma yadda su Musulman suke da kuma yadda aka san su.

ADVERTISEMENT

Jingir ya yi maganar ne a wani taron da aka shirya wanda ƙungiyar Jama’atu  Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS) ta shirya a Kano, wanda Gwamnoni biyu suka samu halarta na Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Jigawa Jigawa, Umar Namadi.

A wani bidiyon da aka saki daga taron, Shehin ya yi kira da Muslimai su haɗa kansu, ba ma kamar idan suka yi la’akari da yawansu idan suna buƙatar su yi amfani da yawansu domin su samu abinda suke buƙata akan  lamarin siyasa, yayin da kuma yake cewar su Kiristocin ai “Kafirai ne.”

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Da yake maida na shi martanin dangane da maganganun da Sheikh Jingir ya yi,Hayab ya ce maganganun da aka yi sun ƙara nuna buƙatar da ake da ita ta ƙasar Nijeriya ta samu haƙiƙanin yawan mutanen da suke bin addinai mabambanta, ba kawai ayi ta dogaro da waɗansu abubuwan da ba a tabbatar da gaskiyar lamarin ba.

Shugaban na ƙungiyar Kiristocin da suke daga Arewacin Nijeriya ya yi kira da gwamnatin tarayya ta shigar da lamarin da ya shafi tambayoyi a kan addini a ƙidayar jama’ar da za a yi nan gaba, inda ya ke cewa duk bayanan da aka tattara za su iya nunawa gaskiyar yadda lamarin addinan ƙasa suke.

“Ya dace ayi tambaya game da addini. Mu san gaskiya wanda ya ke a ƙasar nan da kuma ko kashi nama ne suke, daganan mutane za su daina yi ma wasu ƴan Nijeriya maganganun da basu da ce ba kamar yadda Hayab ya ce,”.

Ya ce babu wani addinin da zai yi amfani da ƙarfin yawan magoya bayan sa ya sa magoya bayan addinin su riƙa yi ma wasu maganganun da basu dace ba,ko kuma su yi amfani da hakan domin su samu wani tagomashin siyasa fiye da sauaran ƴan Nijeriya.

Akan matsalar da take shafar takarar Shugaban ƙasa ta Muslim-Muslim wato ɗantakarar Shugaban ƙasa da mataimakin sa, Hayab cewa ya yi abinda ke damun Kiristoci ba wai su hana  Musulmai damar da suke da ita, ta taimakawa ɗantakarar da ya ke Musulmi ba, amma dai da buƙatar yin adalci, a riƙa tafiya tare da kuma ganin ƙima/ mutuncin juna.

arewa
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
arewa

Kungiyar Daliban Jami'ar ABU Ta Gudanar Gasar Girke-girken Abincin Gargajiya A Bude Bikin Al'adu Na Bana

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.