ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Matsalar Tsaro Ke Hana Manoman Arewa Zuwa Gonakinsu

by Sadiq
4 weeks ago

Matsalar rashin tsaro na ƙara jefa manoma a Arewa Maso Yammacin Nijeriya cikin matsala, inda tsoron hare-haren ‘yan bindiga ke hana wasu zuwa gonakinsu ko yin noma yadda ya kamata.

A wasu sassan Zamfara, Katsina, Sakkwato da Kaduna, manoma na fuskantar barazanar garkuwa, kisa da hare-hare a gonakinsu.

Wasu kuma na tsoron zuwa gonakinsu saboda ‘yan bindiga na iya kai musu hari ko garkuwa da su.

ADVERTISEMENT

A kan hanyar Zariya zuwa Sakkwato, musamman tsakanin Funtua da Gusau, rashin tsaro ya sa hukumomi suka hana manoma shuka amfanin gona masu tsayi a kusa da hanya.

Ana ganin ‘yan bindiga na amfani da dogayen amfanin gona wajen fakewa da kai wa matafiya da jami’an tsaro hari.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Saboda haka, manoma da ke kusa da manyan hanyoyi sun koma noman gyaɗa, wake, waken soya, shinkafa da dankali, waɗanda ba sa yin tsayi sosai.

Sai dai matsalar ta fi gaban haka, saboda wasu manoma sun ce tsoron ‘yan bindiga yana hana su zuwa gonaki, musamman a wuraren da aka samu yawaitar hare-hare da satar mutane.

Wani manomi a yankin Tsafe na Zamfara ya ce akwai lokutan da yake kasa zuwa gonarsa saboda tsoron kai masa hari.

Ya ce ɗan uwansa ya taɓa shafe kwanaki 11 a hannun ‘yan bindiga bayan an sace shi a gidansu, yayin da wasu manoma da suka je cirar rogo su ma aka sace.

Manoman sun ce rashin tsaro yana su zuwa yin noma, wanda ke shafar abin da suke samu da kuma samar da abinci ga al’umma.

Wasu daga cikinsu sun ce da babu matsalar tsaro, za su noma masara, dawa da gero tare da sauran amfanin gona.

Amma yanzu suna tilasta wa kansu yin noman da za su iya yi saboda fargaba.

Masana na ganin idan ba a magance matsalar tsaro ba, harkar noma a yankin za ta ci gaba da fuskantar koma baya, lamarin da ka iya ƙara tsadar kayan abinci da ƙarancin amfanin gona.

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Xavi Hernández Ya Zama Sabon Kocin Netherlands

Xavi Hernández Ya Zama Sabon Kocin Netherlands

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.