Tsohon kocin Barcelona, Xavi Hernández, ya zama sabon kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Netherlands, bayan da Ronald Koeman ya sauka daga muƙamin.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Netherlands (KNVB) ta tabbatar da naɗin Xavi a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa ya sanya hannu kan kwantiragin da zai ci gaba da aiki har zuwa gasar Kofin Duniya ta 2030.
Xavi, mai shekara 46, zai jagoranci tawagar ne bayan Koeman ya yi murabus sakamakon rashin nasarar Netherlands a gasar Kofin Duniya ta 2026 a hannun Morocco.
Naɗin ya kuma sa Xavi ya zama kocin ƙasar waje na farko da ya jagoranci Netherlands cikin kusan shekaru 50.
Kocin Austria, Ernst Happel, shi ne na ƙarshe da ya jagoranci tawagar kafin Xavi.
Xavi ya ce ya ji daɗin samun damar jagorantar Netherlands, yana mai bayyana cewa yana da kusanci da salon ƙwallon ƙafar ƙasar saboda tasirin fitattun masu horar da ‘yan wasa kamar Johan Cruyff da Rinus Michels.
Ya kuma ce yana son salon wasan Netherlands na buga ƙwallo na iya riƙe ƙwallo, kai hari.
Xavi ya koma aikin horarwa ne bayan kusan shekaru biyu ba tare da aiki ba, tun bayan da ya bar Barcelona a 2024.
A Barcelona, ya lashe gasar La Liga da Spanish Super Cup a shekarar 2023.
A matsayinsa na ɗan wasa, Xavi ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Barcelona da Spain, inda ya lashe Kofin Duniya na 2010 da gasar Euro sau biyu.
Zai fara aiki a matsayin kocin Netherlands a watan Satumba, lokacin da tawagar za ta kara da Jamus a gasar UEFA Nations League.
Yanzu ana sa ran Xavi zai fara gina sabuwar tawagar Netherlands da za ta fafata a gasar Euro ta shekarar 2028 da kuma Kofin Duniya na 2030.














