ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

 “Yadda Na Shirya Gudanar Da Bikin Karamar Sallar Bana”

by Rabi'at Sidi Bala
3 months ago
Sallar

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafin Bikin Sallah Karama, kasancewar wannan rana ita ce ranar da ake shagulgulan Sallah Karama, ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Wane irin abinci da abin sha ake da muradin ci/sha da zarar an dawo daga sallar idi?, Wane wurare ake da sha’awar zuwa tare da kai ziyara?, A fadi muhimmancin zumunci wanda aka sani, wacce shawara za a bawa ‘yan’uwa musulmi game da abin da ya shafi bikin Sallah Karama?”.

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

ADVERTISEMENT

Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos a Jihar Filato:

Da farko dai zan fara da taya daukacin ‘yan’uwa Musulmi, Barka Da Sallah. Da fatan an sha ruwa lafiya. Allah Ya sa mun yi ibada karbabbiya cikin wannan wata mai albarka da muka yi bankwana da shi. Yanzu da ake bikin sallah karama, baki ya bude za a koma ciye-ciye da nishadi iri-iri don nuna murna da farin ciki. Ni dai na fi sha’awar abu mai ruwa-ruwa, don haka zan fi son in samu lemo ko ‘ya’yan marmari da soyayyen nama da cincin, don ban fiye son abu mai maiko ba. Bayan nan zan zauna a gida tare da iyali da makwafta, sai zuwa yamma bayan rana ta yi sanyi, zan fita zuwa gaishe da iyaye, kawunnai, da yayye a gidajensu, don yi musu gaisuwar Barka Da Sallah. Hakan yana da muhimmanci sosai a tarbiyyar addinin Musulunci da kuma al’ada ta Malam Bahaushe. Sada zumunci da tallafawa juna a irin wannan lokaci abu ne da yake sanya farinciki a zukatan ‘yan’uwa da surukai da sauran dangi. A raba abinci dafaffe da abin sha a tsakanin juna, a yi wa yara alheri wajen basu kyautar kudade da sunan goron sallah, hatta mata a cikin gidaje kar a manta da su. Ka bai wa mata da yaranka goron sallah, yana kara soyayya da farinciki a tsakanin iyali. Allah Ya maimaita mana na badin badada. Amin.

LABARAI MASU NASABA

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:

Abin ci da sha duk wanda Allah ya bayar mu dai muna ganin shi ne daidai, ba mu da zabi sai na gurin Allah. Shawara kuma ga mutane, shi ne muna fatan yadda muka shiga cikin wannan watan sallah lafiya, Allah ya nuna mana na badi lafiya. Allah kuma ya karbi ibadunmu, ya saka mu cikin ‘yantattun bayi. Ayi sallah lafiya.

Sunana Aminu Adamu Malam Madori:

Allah ya karbi ibadarmu. Batun abinci kuma, waina (masa) da miyar yakuwa, zamu fara amfani da su bayan mun ci dabino mun tafi Sallar Idi, sai kuma abun sha shi ne Kunun Aya. To, batun ziyara kuma zamu ziyarci gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki domin ayi gaishe-gaishe da zumunci, har ma da dubiya ga marasa lafiya, ‘yan’uwa da abokan arziki. Batun muhimmanci zumunci kuma abu ne wanda yafi gaban kidayawa domin addininmu musulunci yayi magana akan muhimmanci na zumunci da kuma sakamakon masu yin zumunci. Shawarata a nan ita ce, mutane su yi bukata daidai aljihunsu, domin lokaci ne me wucewa kada ayi gasa ko wuce gona da iri wajen bukata, daga karshe kuma ya kamata mu dage da addu’ar samun zaman lafiya a kasar mu Najeriya baki daya dama duniya.

 Sunana Fatima Nura Kila daga Jihar Jigawa

Alhamdulillah gaskiya sai dai mu yi wa Allah godiya, ganin ga shi kamar yau za a fara amma har ana sallah. Gaskiya ni ana dawo wa nafi so na samu dan abin sha kafin akai ga abincin. Alhamdulillah zamu kai ziyara garin dangi da abokan ardiki. Gaskiya zumunci abu ne mai kyau, wanda mu mutanen yanzu bamu fiya damuwa da shi ba, amma zumunci ginshiki ne a rayuwar dan’adam. Ya kamata wadanda basu da shi su taimakawa na kasa da su domin kowa yayi bikin sallah lafiya cikin farinciki.

 Sunana Anas Bin Malik Achilafia ‘Yankwashi daga Jihar Jigawa:

Da zarar an dawo daga Sallar Idi, mutane da yawa suna da muradin cin abinci irinsu; Tuwo da miya, Shinkafa, Fura da Nono, ko kayan zaki, tare da shan abubuwa kamar; Kunu ko Lemo domin yin walima tare da iyali. Haka kuma mutane sukan yi sha’awar ziyartar iyaye, dangi, abokai, da makwafta, domin kara dankon zumunci da farinciki. Muhimmancin zumunci kuwa shi ne yana karfafa soyayya da hadin kai a tsakanin al’umma, yana kawo zaman lafiya da taimakon juna. Don haka shawarar da zan ba wa ‘yan’uwa Musulmi ita ce su yi bikin Sallah cikin ladabi, su guji barna da aikata abubuwan da ba su dace ba a addinance da al’adance, su taimaki marasa karfi, kuma su karfafa zumunci da juna.

 Sunana Hassana Sulaiman daga Hadejia Jihar Jigawa

Kai ziyara sun hada da gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki domin samun ladan zumunci musamman a wannan rana. Zumunci na da muhimmanci sosai a addinin musulunci kuma abu ne wanda ma’aiki ya kwadaitar da mu a kansa, saboda falala dake cikinsa dan kuwa ubangiji ma ya jaddada muhimmancin da tagomashin da masu yinsa za su samu da kuma tsoratarwa ga masu yanke shi. Shawarar da zan bawa ‘yan’uwa musulman duniya bakidaya, su zama masu taimakon juna da kulawarsu ga masu karamin karfi dama makwaftansu har da hakkin zamantakewa domin rabauta gobe kiyama.

Sunana Abubakar Usman Malam Madori:

A lokuta da dama ana dafa shinkafa da miya da kifi ko nama, ko kuma Funkaso ko Masa domin liyafar sallah. A ranar idi, mutane da dama kan so su je gidajen iyaye, ‘yan’uwa da abokai domin gaishe su. Wasu lokuta ana zuwa yawon shakatawa kamar gidan tarihi, gidan Zoo da wuraren wasa. Zumunci yana kara kauna da hadin kai tsakanin ’yan’uwa, yana saka mutane su rika taimakon juna a lokacin bukata. Haka kuma yana kawo zaman lafiya da fahimtar juna a cikin iyali. Shawara ya kamata Musulmai su yi bikin cikin godiya ga Allah bayan kammala azumin Ramadan, su kula da yin sallar idi tare da kuma sanya kyawawan tufafi, haka kuma su rika bayar da Zakkah domin taimakon marasa galihu.

Sunana Jibrin Yusuf Kaila, daga garin Hadejia, Jihar Jigawa:

Zumunci wani muhimmin jigo ne mai babbar daraja da lada a addinin Musulunci, haka ma a al’adar Bahaushe. Zumunci ne ginshikin al’adar da muka gada daga iyaye da kakanni. Zumunci na nufin kula da dangantaka tsakanin ‘yan’uwa ta hanyar gaisuwa, taimako, da ziyara. Lokacin bikin Sallah Karama, lokaci ne na ziyara. Kuma lokaci ne da yake daga cikin lokuta mafi dacewar karfafa zumunci, domin mutane sukan samu damar komawa gida su gana da iyayensu, ‘yan’uwansu da makusanta, musamman wadanda suka yi nisa da ‘yan’uwansu, saboda wasu dalilai irin na aiki ko cirani. Sannan lokaci ne da yake kawo albarka da lada a addini. A koyarwar Musulunci, kula da ‘yan’uwa da ziyartar su ibada ce mai girma. Duk wanda yake kyautatawa danginsa yana samun lada, kuma hakan yana sa Allah ya sanya albarka a rayuwarsa da zaman lafiyar iyalinsa. Saboda haka ina mai karfafa mana gwiwa kan muhimmancin ziyara a lokacin bukukuwan sallah, kasancewarsa aiki mai dimbin ladan a addinin Musulunci.

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, Karamar hukumar Dala, daga Jihar Kano:

Bayan dawowa daga sallar Idi, abincin da na fi sha’awar ci shi ne tuwon shinkafa da miyar taushe, tare da abin sha kamar kunun aya mai sanyi. Wannan lokaci ne na farinciki da iyalai ke taruwa su ci abinci tare. A wannan rana ta sallah in sha Allah zan ziyarci ‘yan’uwa da abokan arziki domin a gaisa, a yi wa juna fatan alheri don kara dankon zumunci. Zumunci yana da muhimmanci sosai a rayuwar al’umma, domin yana kara kauna, hadin kai da taimakon juna tsakanin mutane. Haka kuma addinin Musulunci ya yi umarni da kiyaye shi domin yana kawo zaman lafiya da fahimtar juna. Shawarata ga ‘yan’uwa Musulmi ita ce mu yi bikin sallah cikin nutsuwa da nuna godiya ga Allah, mu tuna da marasa galihu ta hanyar taimako, mu kuma guji almubazzaranci da duk wani abu da zai iya jawo sabani ko bata tarbiyyar matasa.

 Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:

Ai san samu a samu Sunasir da miyar taushe ko wainar shinkafa da miyar taushe gefe a samu Zobo mai sanyi ko lemon Ayya. Wurin zuwa dai san samu kwashi yara muje dan ziya gidanmu. Zumunci abu ne mai muhimmanci, Ubangiji da kansa ya ce tsagi ne daga jikin sunansa Arrahamanu, ayi komai cikin kiyaye dokokin ubangiji.

Sallar
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Sha Wata Wahala Ba A Gwagwarmayar Shiga Harkar Fim —Hadiza
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

MASU ALAKA

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
Taskira

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

June 13, 2026
Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure
Taskira

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

June 6, 2026
Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
Taskira

Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki

May 29, 2026
Next Post
Matsalar ADC Ta ADC Ce BA Ta APC Ba Ce

Matsalar ADC Ta ADC Ce BA Ta APC Ba Ce

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

June 13, 2026
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

June 13, 2026
Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

Wannan Hakki Na Tushe Yana Da Matukar Muhimmanci

June 13, 2026
An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

An Cafke Mutum Uku Kan Kisan Mawaki Dan Asalin Nijeriya Da Birtaniya

June 13, 2026
Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

Allah Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Matawalle

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.