A halin yanzu a iya cewa babu masu cin karensu ba babbaka a jihar Kano kamar ƴan daba, lamarin da ke ƙara ta’azzara rashin tsaro tare da jefa tsoro a zuƙatan al’ummar jihar. Amma idan ana buƙatar sanin mece ce daba sai an koma baya domin gano yaushe ta fara kuma su waye suka assa ta.
Tarihin fadan daba a Kano ya samo asali ne tun daga shekarun 1970 da 1980, inda aka fara shi a matsayin gungu na matasa masu amfani da sanduna da adduna domin kare unguwanninsu lokacin bukukuwan dambe da kokowa. Daga baya ya rikiɗe zuwa kungiyoyin ƴan banga da ƴan siyasa ke amfani da su a lokacin zaɓe, kafin ya zama matsalar rashin tsaro da ta shafi ƙwacen waya da fashi.
Asalin Daba (Shekarun 1970 zuwa 1980)
A da, “daba” na nufin gungun matasa masu kare unguwa ko gudanar da wasannin gargajiya kamar dambe da kokowa. A cikin Birnin Kano da kewaye, kowace unguwa tana da nata gungun, kuma galibi faɗan da suke yi na gargajiya ne tsakanin unguwa da unguwa ba tare da makamai masu haɗari ba.
Siyasa da Makamai a (Shekarun 1990 – 2000)
A wannan lokacin ne wasu ƴan siyasa suka fara ɗaukar matasan nan don amfani da su wajen tsoratar da abokan adawa ko yin awon gaba da akwatunan zaɓe. Hakan ya sa ƙungiyoyin suka fara mallakar makamai na zamani da suka haɗa da:
Adduna da wukake, Ƙwayoyi da sauran abubuwan da ke maye Gurneti da bindigogi na gida (a wasu lokutan)
Zamanin Kwacen Wayar Salula (2010 – Zuwa Yanzu)
Bayan an kwashe shekaru ana amfani da su a harkokin siyasa, yawancin matasan sun shiga halin rashin aikin yi. Hakan ya janyo ɓarkewar miyagun laifuka irin su ƙwacen waya da fashin ƴan ƙasa da ke tsoratar da al’umma. Fitattun yankuna da suka shahara da wannan matsala sun hada da Kurna, Kofar Mata, Yakasai, Rimi da Zango.
Matakan da Gwamnati Da Jami’an Tsaro Suka Dauka
Matsalar dabar ta zama babban ƙalubale ga zaman lafiya da tattalin arzikin Jihar Kano. Don kawo ƙarshen wannan matsala, hukumomi sun ɗauki matakai da dama, waɗanda suka haɗa da: Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ƙarƙashin kwamishinanta ta shiga lunguna da saƙuna domin cafke shugabannin ƴan dabar.
Kafa rundunonin sa-kai na jihar (kamar Kano State Neighborhood Watch Corps) da samar musu da motocci da kayan aiki domin sintiri a unguwanni.
Shirya wasannin ƙwallon kafa da sauran taruka na sada zumunci da matasa domin jawo hankalinsu su ajiye makamai.
Yin sulhu tsakanin tubabbun ƴan daba da jami’an tsaro don haɗa hannu wajen ciyar da jihar gaba.
Su Wa Ke Ƙara Rura Wutar Faɗan Daga A Kano?
Basiru Ado Musa, wani bincike kan al’amuran da suka shafi harkokin daga a Jihar Kano ya yi ƙarin haske kan haka inda ya ce, “Idan za mu faɗa wa kanmu gaskiya kowa ya sani babu masu cin moriyar wannan harkoki na daba kamar ƴan siyasa, ta yadda za ka ji an kama yaro an tsare shi a gidan kaso shekara da shekaru da yawa daga cikinsu ma kisan kai suka yi, amma da zarar lokuta irin waɗannan sun zo na zaɓe sai ka ga waɗannan yaran sun fito suna yawo kuma ba su fasa yin abin da suke na harkar dabar ba, wannan ne ke alamta cewa lallai akwai sa hannun masu riƙe da madafun iko.
A zamanin gwamnatin da ta gabata, an sha samun a rangama tsakanin yaran ƴan siyasa na gwamnatin mai mulki da na jam’iyyar adawa, wanda hakan ma yana
“Ko a wannan lokacin ma sa’adda aka je taro mai girma gwanma daga filin jirgin sama, nan ma an samu irin wannan faɗa na daba, kuma idan da a ce faɗan zai tsaya a tsakaninsu da an samu sauƙi, amma ta wannan faɗan za ka samu ana ɓalle shagunan mutane a yi musu sata, ana bin mutane ana daɓa musu wuƙa ana karɓe musu wayoyi, wanda ta haka ne wasu ke asarar rayukansu a jikkata wasu.
“Kazalika a ranar da aka rantsar da sabon mataimakin gwamnan Jihar Kano, an kashe mutane tare da jikkata wasu naya ga asarar dukiyoyi. To sai ka duba ka gani me ya haɗa rantsar da mataimakin gwamna da faɗan daba, sannan wane mataki gwamnatin ta ɗauka domin hana faruwar abin nan gaba? Amma an ja baki an yi shiru.
“Sannan kusan makonni biyu da suka gabata, faɗan daba ya sake kaurewa a daidai IBB nan kusa fa Triumph, inda sai da ta kai an sanya dokar hana fita saboda yadda lamarin ya ƙazance. To mu abin da ya sa muke ɗora alhakin abin akan ƴan siyasa saboda mulkinsu ne kuma ana zargin su ke ɗaure gindin yin hakan.”
Kisan ɗansanda
An kashe wani ɗansanda da ke aiki a sashen ƴansanda na Hotoro mai suna Sani S.O, yayin wata arangama tsakanin ƙungiyoyin daba masu gaba da juna a Kano, watanni kaɗan kafin ritayarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shi tare da wasu mutum huɗu a lokacin rikicin da ya faru a ƙarshen makon da ya gabata a yankin Hotoro da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da aka kuma bayar da rahoton mutuwar wasu mutum biyu a wani irin rikici makamancin haka tsakanin ƴan daba a Fagge da kasuwar mayanka ta Kano da ke makwabtaka da yankin.
Hakazalika, a ranar Laraba, wasu ƴan daba sun kashe shugaban mafarauta na Ƙaramar Hukumar Tofa a jihar, Kaura Mamiyo, yayin wani taron siyasa na nuna goyon baya ga wani ɗan majalisar dokokin jihar. Rahotanni sun ce ƴan dabar sun kashe shi ne da sanduna bayan sun yi ƙoƙarin amfani da wuƙaƙe da adduna amma abin ya ci tura.
Wata majiya da ke kusa da marigayin ɗansandan ta shaida wa manema labarai cewa an tura shi tare da wasu abokan aikinsa domin tarwatsa faɗan da ƙungiyoyin daban ke yi lokacin da ɗaya daga cikin ƴan dabar ya harbe shi da bindigar toka.
“Yana aiki ne a sashen ƴan sanda na Hotoro kuma an tura shi tare da wasu domin tarwatsa ƴan daban. Ba tare da saninsa ba, ɗaya daga cikinsu na ɗauke da bindigar toka wadda ya yi amfani da ita wajen harbe shi. An garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa,” in ji majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta.
Majiyar ta bayyana marigayin jami’in ɗansandan a matsayin mutum sananne kuma abin ƙauna a al’ummarsa wanda ya shafe sama da shekara talatin yana hidima.
“Mutum ne nagari wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga al’umma, musamman mutanen da ke kusa da shi. Makonni kaɗan ne kawai suka rage kafin ya yi ritaya aka kashe shi,” in ji majiyar.
Wani mazaunin yankin, Balarabe Ibrahim, ya ce kwanaki kaɗan kafin rasuwar jami’in, ya bayar da gudunmawar fanfunan iska da sauran kayayyakin da ake buƙata a masallacin al’umma.
An kashe ƙarin mutum huɗu
Wani mazaunin yankin Abubakar ya ce aƙalla wasu mutum huɗu ne aka kashe tare da jami’in ɗansandan a lokacin rikicin.
Ya bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba biyu masu gaba da juna a Tsallaken Maradi da Ramin Kwalabe, duk a unguwar Hotoro.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa ba wannan ne karo na farko da ƙungiyoyin ke faɗa ba, amma bai taɓa kai wa wannan matakin na zubar da jini ba.
Abin da ya faru a Hotoro, shi ya faru a Fagge
Unguwannin Fagge da kasuwar mayanka ta Kano su ma sun fuskanci rikice-rikicen ƴan daba da suka ɗauki hankalin jama’a a birnin cikin ƙasa da mako guda.
Abin da aka ce ya fara a matsayin saɓani kan kuɗi ya rikiɗe cikin gaggawa zuwa hare-hare da ramuwar gayya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a yankin.
Mai unguwar Fagge B, Nura Ubale, ya ce rikicin ya fara ne tsakanin wasu mutane biyu, Musa da Audu Mahaukaci, duk mazauna Fagge ne.
Ya bayyana cewa: “Audu Mahaukaci ya zargi Musa da ɗaukar kuɗinsa. Daga baya kuma aka zargi Mahaukaci da kashe Musa. A yayin haka, wasu da ake zargin abokan Musa ne suka kashe Mahaukaci.
“Ba wai rikici ne tsakanin mutanen yankin da ƴan kasuwar mayanka ba. Dukkan waɗanda suka mutu mazauna Fagge ne, sai dai Musa yana gudanar da sana’arsa a kasuwar mayanka. Ana zargin abokansa na can ne suka shirya kisan, wanda ya sa mutane suka riƙa cewa ƴan kasuwar mayanka na faɗa da mutanen Fagge.”
Ya ƙara da cewa kafin wannan lokaci, ba a taɓa samun rikici tsakanin yankunan biyu ba, yana mai jaddada cewa saɓanin rahotannin da ake yaɗawa, mutum biyu ne kawai suka mutu.
Ubale ya ce shugabannin yankunan da abin ya shafa sun riga sun gana da ƴansanda da kuma rundunar yaƙi da daba domin shawo kan lamarin.
“Shugabannin Fagge da na kasuwa sun zauna domin warware matsalolin. Mun yi taro har zuwa ƙarfe 1 na dare. Muna kuma shirin sake yin wani taron, duk da cewa an riga an dawo da zaman lafiya,” in ji shi.
Ya bayyana cewa yankunan biyu suna da kyakkyawar dangantaka, yana mai nuni da cewa hatta shugaban mahauta na jihar ma ɗan asalin Fagge ne.
Haka kuma, wani ɗan kasuwa a kasuwar mayanka, Haruna Salisu, ya ce rikicin da ya faru kwanan nan ya daƙile harkokin kasuwanci tare da sanya tsoro a zuƙatan ƴan kasuwa.
Sai dai ya ce yanzu al’amura sun daidaita sakamakon matakan gwamnati da ƴansanda.
“Mutane suna da ra’ayi mara kyau game da kasuwarmu cewa saboda muna amfani da wuƙaƙe wajen yanka da fatar dabbobi, to akwai ƴan daba da yawa a cikinta, amma hakan ba gaskiya ba ne. Kowa na iya shiga kasuwar ya ɓuya a cikinta domin aikata laifi. Muna addu’a irin wannan abu ba zai sake faruwa ba,” in ji Salisu.
“Abin da muke yi don magance matsalar – Ƴansanda”
Mun yi ƙoƙarin samun jin ta bakin rundunar ƴansanda amma lamarin ya ci tura, domin kakakin ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai ɗaga waya ko amsa saƙonni ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Sai dai kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta ƙaddamar da Sashen Gaggawar Yaƙi da Laifuka na Rikici domin tunkarar laifukan tashin hankali cikin sauri da ƙwarewa.
Ya bayyana cewa an kafa wannan sashi ne a watan Afrilu 2026 bisa umarnin Sufeton Janar na Ƴansanda, kuma an tsara shi domin amsa kiran gaggawa cikin sauri, hanawa da daƙile laifukan tashin hankali, tare da gudanar da bincike da gurfanar da masu laifi.
Kwamishinan ya ce an zabo tare da horar da jami’ai na musamman domin wannan sashi, kuma an tanade su da kayan aiki don gudanar da aiki cikin ladabi, gaskiya da mutunta haƙƙin ɗan adam.
Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar a ƙarƙashin jagorancinsa tana ɗaukar cikakken alhakin ayyukan wannan sashi, yana mai cewa za a gudanar da aiki bisa sahihan bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar al’umma, tare da kulawar jama’a domin gina amana.
“Mun ƙuduri aniyar gyara halayen ƴan daba – Gwamnatin Kano”
Gwamnatin jihar ta ce ta himmatu wajen gyara halayen ƴan daba domin su koma mutane nagari a cikin al’umma, ba kawai kawar da su ba.
Da yake magana a wata hira da wasu gidajen rediyo na cikin gida, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce gwamnati ta ƙaddamar da wani shiri mai suna “Operation Safe Corridor”.
Ya ce, “Wannan shirin na nufin gyara halayen ƴan daban nan ne. Burinmu shi ne mu gyara mutum 3,000, kuma mun riga mun shigar da rukuni na farko na mutum 1,000.”
Ya ƙara da cewa shirin na daga cikin dabarun da ba na amfani da ƙarfi wajen yaƙi da laifi a cikin al’umma ba, wanda gwamnati ta jajirce wajen aiwatarwa. Ya kuma ce ana ci gaba da amfani da dabarun amfani da ƙarfi wajen yaƙi da laifuka, shi ya sa gwamnati ta kafa rundunar Neighbourhood Watch domin taimaka wa sauran hukumomin tsaro.
Ƙaruwar ta’addancin ƴan daba a Kano gazawar al’umma ce baki ɗaya – Tsohon Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda
Wani ƙwararren masani kan tsaro kuma tsohon Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda (DCP), Yahaya Hashim, ya danganta ƙaruwa da tashe-tashen hankulan ƴan daba a jihar da siyasantar da matsalar tun da daɗewa da kuma gazawar al’umma gaba ɗaya.
Hashim ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa da a ce an tunkari matsalar tun tana ƙarama da tuni an magance ta.
Ya ce ƴan siyasa sun ci gaba da cin gajiyar ayyukan ƴan daba, inda suke ɗaukar su aiki a lokacin taruka sannan su riƙa ba su lada maimakon hukunta su. “Gwamna ko ma shugaban ƙasa ma za a tarbe shi da waɗannan ƴan daba masu ɗauke da makamai,” in ji shi.
Haka kuma, ƙwararren masani kan tsaro ya dora laifi kan iyaye da al’umma saboda gazawa wajen magance matsalar tun daga gida.
Ya jaddada cewa hanya mafi kyau ita ce a “komawa tushe,” inda ya buƙaci iyaye su duba tarbiyyar ‘yaƴansu, gwamnati ta kafa ƙarfafan dokoki kan ƴan daba, sannan ƴan siyasa su nisanci irin waɗannan ƙungiyoyi.
Ya kuma tunatar da cewa a wani lokaci, wani gwamna mai ci har ya taɓa naɗa Mashawarcin Musamman kan harƙar ƴan daba, abin da ya ce yana da matuƙar haɗari.
Hashim ya ƙara da cewa al’umma ma dole su ɗauki alhaki, domin an san ƴan daban a yankunansu sosai.
“Ko wannan yankin da aka kashe ɗansanda an san shi da yawan ƴan daba. Har ma mutane daga wasu sassan Kano suna zuwa can su ɗauki ƴan daba haya domin aikata laifi a wasu wurare,” in ji shi.
Ƙaruwar rikici yayin da zaɓe ke gabatowa.
A cikin makonni da suka gabata, Jihar Kano ta sake fuskantar ƙaruwa da rikice-rikicen ƴan daba a sassa daban-daban na birnin, ciki har da wuraren da ba a saba jin irin wannan tashin hankali a da ba. Wannan ƙaruwa na faruwa ne yayin da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Daga cikin wuraren da rikicin ƴan daba ya shafa a baya-bayan nan sun haɗa da Fagge, kasuwar Abattoir, Koki, Kurnar Asabe, Hotoro da Gyadi-Gyadi, da sauran yankuna.
Kafin makonni biyu da suka gabata, an ruwaito cewa aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu a wani rikici da ke da alaƙa da siyasa a ranar rantsar da sabon mataimakin gwamna a jihar.
Makon da ya gabata kuma, wasu ƴan daba da ake zargin suna halartar wani taron siyasa a kusa sun kai hari kasuwar GSM ta Farm Center, inda suka ƙwace kayayyakin ƴan kasuwa, abokan ciniki har ma da masu wucewa.















Discussion about this post