A siyasar Nijeriya, yawan bayyana a manyan kanun labaran jaridun kasa, tafiye-tafiye zuwa kasashen waje kan diflomasiyya na gwamnati, sukan zama tamkar wata babbar alamar iko da nasara. Duk da haka, bai hana wani jami’in gwamnati ya yi ƙoƙarin yin wani abu na daban na a zo a yaba kuma mai ɗorewa, kamar sauya tsarin manufofi gaba ɗaya. Wannan ne, a fannoni da dama, ya bayyana aikin Jakada Yusuf Maitama Tuggar a matsayin Ministan Harkokin Waje na Nijeriya a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tun daga farko, Jakada Tuggar ya gina aikinsa kan wata manufa mai sauƙi amma mai girman buri, cewa dole ne Nijeriya ta mu’amalanci duniya ba a matsayin mai dogaro ba, sai dai a matsayin ƙasa mai tafiya da cikakken tsari, ƙarfin gwiwa, da kuma kare muradun ƙasa. Wannan mai da hankali kan ‘yancin kai na dabarun ƙasa, na da nufin ƙarfafa alfahari da amincewa da sabon salo na manufofin ƙasashen waje na Nijeriya a idon duniya.
- Jihohi 7 Za Su Fuskanci Katsewar Wutar Lantarki Na Tsawon makonni
- Hukumar Zaɓe A Ƙarƙashin Amupitan Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyya – Dasuki
Masu sukar gwamnati na iya cewa manufofin harkokin waje na Nijeriya sun dade suna yin alkawura amma har yanzu shiru, don haka, ba laifi a bayyana wa masu suka wasu nasarori na zahiri, kamar alƙawuran jarin biliyoyin daloli da kuma ƙaruwar tasirin Nijeriya a ƙungiyar BRICS, wanda ya karu a hankali tsakanin 2023 zuwa 2026.
Waɗannan sakamako, suna nuna sabon salo na yadda Nijeriya ke mu’amala da duniya, wanda ya wuce maganganun fatar baki kawai.
A ƙarƙashin Tuggar, Nijeriya ta ƙarfafa jagorancinta a manyan cibiyoyin Afirka, tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannoni kamar zaman lafiya, tsaro, da jagorantar fannin tattalin arziki. An sake zaɓen ƙasar a Majalisar Zaman Lafiya da Tsaro ta kungiyar hadin kan Afirka (AUPSC) na zangon 2022–2025, inda ta ci gaba da kasancewa a kungiyar tun daga 2004.
A wani babban mataki na karfin tattalin arziki, Nijeriya ta samu kujera ta dindindin a kwamitin bankin Afirka na tsakiya da ake shirin kafawa wanda taron ya gudana a watan Fabrairun 2026, wanda ya ƙara ƙarfafa rawarta wajen tsara makomar kuɗaɗen nahiyar. Haka kuma, ƙasar ta ƙara ƙarfafa tasirinta ta hanyar sake zaɓen Bankole Adeoye a matsayin Kwamishinan AU na harkokin siyasa, zaman lafiya, da tsaro. A lokaci guda kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da jagoranci yankin yayin da ya jagorantar Majalisar Ministocin Harkokin Waje ta ECOWAS.
Bayan mukamai na hukumomi, Nijeriya ta ci gaba da taka rawa sosai a diflomasiyyar yankin da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya. A ƙarƙashin Yusuf Maitama Tuggar, ƙasar ta yi ƙoƙarin ci gaba da haɗin kai a yankin duk da matsalolin da suka biyo bayan ficewar wasu ƙasashen Sahel daga ECOWAS, tare da kuma goyon bayan zaɓen Jamhuriyar Benin a AUPSC.
Ta fuskar kuɗi, Nijeriya ta nuna sabon ƙuduri ta hanyar biyan cikakken harajin ECOWAS na shekarar 2023—karon farko cikin kusan shekaru ashirin—tare da bayar da gudunmawa mai yawa a shekarar 2024.
Wani muhimmin abu shi ne shirin gyaran cikin gida. Manufofin harkokin waje ba su da ƙarfi sai idan cibiyoyin da ke tafiyar da su suna da ƙarfi, kuma Tuggar ya fahimci hakan. Ƙirƙirar sashen fasahar basirar wucin gadi (AI Unit) don hasashen diflomasiyya da kuma ƙaddamar da sabbin ayyukan jakadanci na zamani sun nuna cewa Nijeriya na sabunta kanta tare da ƙarfafa fata da amincewa da makomarta.
Duk da haka, babu wani lokaci na shugabanci da ba shi da ƙalubale. Mayar da alƙawuran jari zuwa ainihin ci gaban tattalin arziki har yanzu ƙalubale ne mai gudana. Duk da muhimmancin bayyanar diflomasiyya, dole ne a ga tasirinta a cikin rayuwar cikin gida—ayyukan yi, ababen more rayuwa, da zaman lafiya. Saboda haka, ainihin auna wannan zamani ba zai kasance yawan yarjejeniyoyi ko tafiye-tafiye ba, sai dai dorewar tasirinsu ga ci gaban Nijeriya.
Babu shakka Tuggar ya kawo wani irin tsari mai ma’ana da zurfin tunani a wannan muƙami. Ya jaddada ƙwarewa, ya kare martabar jami’an diflomasiyya, kuma ya jaddada cewa, dole ne manufofin harkokin waje su kasance bisa ilimi da ƙwarewa.















Discussion about this post