ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar Zaɓe A Ƙarƙashin Amupitan Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyya – Dasuki 

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
5 months ago
Amupitan

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a Jihar Sakkwato, Honarabul Abdussamad Dasuki ya bayyana cewa hukumar zabe a karkashin jagorancin Joash Amupitan barazana ce ga dimokuradiyyar jam’iyyu da dama a Nijeriya.

Dan majalisar ya yi zargin cewa hukumar na yin hadin guiwa da wasu da ke kokarin danne jam’iyyun adawa domin mayar da Nijeriya kasa mai jam’iyya daya kacal.

ADVERTISEMENT
  • Xi Ya Bukaci Zurfafa Akidun Siyasa A Rundunonin Sojin Kasar
  • Rikicin Bashin ₦25,000 Ya Yi Sanadin Kashe Wani Matashi A Mashaya Giya

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya karbi katin zama dan jam’iyyar ADC a mazabarsa ta Dogon Daji/Salah da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar Sakkwato.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Da yake jawabi ga taron magoya bayansa, dan majalisar ya yi gargadin cewa sabbin abubuwan da ke faruwa a fagen siyasar Nijeriya na nuni da wani tsari da aka tsara domin raunana muryoyin ‘yan adawa da kuma tauye ginshikin dimokuradiyya.

Ya yi nuni musamman da matakin da hukumar zabe ta dauka na kin amincewa da shugabancin jam’iyyar ADC a karkashin David Mark, yana mai cewa wannan wani muhimmin mataki ne a abin da ya kira wani shiri na danne ‘yan adawa da rushe tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama.

A cewarsa wannan mataki an yi shi ne domin raunana tsarin jam’iyyun adawa, lalata tsarin jam’iyyu da yawa, tare da kai kasar zuwa ga tsarin jam’iyya daya kacal, inda jam’iyyar APC za ta zama ba kawai mafi karfi ba, har ma ita kadai ce za ta iya tsayar da dan takara mai karfi a zaben shugaban kasa a 2027.

Ya ce wannan ba batun jam’iyya daya ko rikicin shugabanci kadai ba ne, ya ce batu ne da ya shafi makomar dimokuraɗiyya.

Ya ce abin da ake gani a yanzu wani tsari ne da aka tsara domin rufe bakin ‘yan adawa, takaita sararin dimokuraɗiyya da kuma tilasta tsarin jam’iyya daya a kasa mai yawaitar bambance – bambance.

Ya kuma yi gargadin cewa irin wadannan matakai, idan ba a dakatar da su ba, na iya mayar da kasar baya a nasarorin mulkin dimokuradiyya da Nijeriya ta samu a tsawon shekaru.

Dan majalisar ya yi kira ga al’umma, kungiyoyin fararen hula da kuma kasashen duniya da su kasance cikin shiri, ya ce duk masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wajen kare cibiyoyin dimokuraɗiyya tare da tabbatar da bin doka da oda a Nijeriya.

Amupitan
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ posts Bio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato
Amupitan
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Sabon Salon Nuna Karfin Soja Na Japan Na Sake Haifar Da Barazana 

Sabon Salon Nuna Karfin Soja Na Japan Na Sake Haifar Da Barazana 

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.