Da yammacin yau Laraba, an gudanar da taron manema labarai a Aerospace City dake birnin Beijing domin gabatar da ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-21 ga manema labarai da kuma jama’a. Wannan shi ne karo na farko da ’yan sama jannatin Shenzhou-21 da suka hada da Zhang Lu da Wu Fei da Zhang Hongzhang suka fito a fili tun bayan dawowarsu doron kasa da kammala killacewa da murmurewa.
An bayyana a gun taron cewa, ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-21 suna cikin koshin lafiya, kuma a yanzu ana mayar da hankali kan lafiyarsu. Kuma bayan an kammala aikin tantance lafiyarsu, za su koma bakin aiki yadda ya kamata.
’Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-21 sun kafa sabon tarihi na tsawon lokacin da ’yan sama jannatin rukuni guda daya suka shafe suna aiki a sararin samaniya, inda suka shafe kwanaki 210. Da hadin gwiwa da masu bincike a doron kasa, sun kuma kammala gwaje-gwajen kimiyya da dama a fannoni kamar na kimiyyar kayayyakin sararin samaniya, kimiyyar rayuwar sararin samaniya, ilmin likitancin sararin samaniya, da fasahohin sararin samaniya.(Safiyah Ma)














