Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ɗora sakamakon rumfunan zaɓe 1,386 na zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar a shafinta na IReV.
Da aka duba shafin da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ya nuna cewa an ɗora sakamakon rumfuna 1,386 daga cikin 3,763 da ake da su, wanda ya kai kashi 36.83 cikin 100.
An ɗora sakamakon na ƙarshe da misalin ƙarfe 5:24 na yamma daga rumfar zaɓe mai lamba 29/02/04/002, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a ƙananan hukumomi 30 na jihar.
Shafin IReV na bai wa jama’a damar ganin sakamakon kowace rumfar zaɓe ta intanet yayin da INEC ke ci gaba da ɗora sauran sakamakon.
Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord na neman sake lashe zaɓen, inda yake takara da Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, Najeem Salaam na jam’iyyar ADC da sauran ‘yan takara.
Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon, ana sa ran INEC za ta ci gaba da ɗora sauran sakamakon rumfunan zaɓen a shafin.














