ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Tawagar Ƙwallon Ƙafa Ta Maza da Mata a Nijeriya Suka Gaza Zuwa Gasar Kofin Duniya

by Rabilu Sanusi Bena
4 weeks ago

A daren Alhamis ne tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, Super Falcons, ta sha kashi a hannun Banyana-Banyana ta Afirka ta Kudu da ci 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta mata ta 2027 da za a gudanar a Brazil.

Wannan rashin nasara ya sa Super Falcons ta kasa samun gurbin gasar a karon farko cikin shekaru 30, lamarin da ya sake jawo hankalin masu ruwa da tsaki kan makomar ƙwallon ƙafar mata a ƙasar.

A ɓangaren maza ma, Super Eagles ta kasa samun gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka gudanar a Amurka, Mexico da Canada. Nijeriya ta rasa tikitin ne bayan rashin nasara a hannun Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wasan neman gurbin shiga gasar. Wannan ya kasance abin takaici ga masu sha’awar ƙwallon ƙafa, musamman ganin yadda Nijeriya take daga cikin ƙasashen da suka fi ƙarfi a Afirka, inda take matsayi na huɗu a jadawalin FIFA na nahiyar.

ADVERTISEMENT

Nijeriya ta daɗe tana daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi samun damar shiga gasar Kofin Duniya, inda Super Eagles ta halarci gasar sau shida tare da kaiwa zagayen ’yan wasa 16 sau uku, a 1994, 1998 da 2014. Sai dai rashin samun tikitin gasar sau biyu a jere ya haifar da tambayoyi kan alkiblar ƙungiyar, inda ake zargin matsalolin gudanarwa a Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF), tsarin horarwa da kuma irin ’yan wasan da ake gayyata.

Abin da ya ƙara dagula lamarin shi ne yadda Afirka ta samu ƙarin gurabe a gasar Kofin Duniya ta 2026, amma Nijeriya ta kasa cin gajiyar damar. Wannan ya sake buɗe muhawara kan yadda ake tafiyar da ƙwallon ƙafa a ƙasar, daga tsarin zaɓen ’yan wasa zuwa shirye-shiryen wasanni da gudanarwar ƙungiyoyin ƙasa. A bangaren mata kuwa, duk da wannan rashin nasara, Super Falcons na da tarihin nasarori a Afirka da kuma matakin duniya, abin da ke nuna cewa akwai ginshiƙan da za a iya gina sabon shiri a kansu.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

A ƙarshe, gazawar Super Eagles da Super Falcons na samun gurbin gasar Kofin Duniya a lokutan da suka gabata ya kamata ta zama abin nazari mai zurfi ga masu gudanar da ƙwallon ƙafa a Nijeriya. Tambayar da ke gaban ƙasar yanzu ita ce: a ina matsalar take cikin gudanarwa, horarwa, zaɓen ’yan wasa ko kuma tsarin ci gaban ƙwallon ƙafa tun daga matakin ƙananan yara?

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Za’a Dakatar Da Wasa A Farkon Minti 10 Na Kowane Wasa A Kasar Argentina Saboda Girmama Messi
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Ahanor Kan Fam Miliyan 40

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post

An Nemi A Gaggauta Ceto Ɗaliban Makarantar Da Aka Sace A Jihar Borno

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.