ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Na Kokarin Cika Wa’adin Dokar Zabe

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
2027

Bisa amincewa da dokar zabe ta 2026 da sabon jadawalin lokacin zaben 2027, jam’iyyun siyasa a Nijeriya suna cikin matsin lamba wajen kokarin cika ka’idoji na wa’adin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta fitar.

Ko da yake cibiyar hadakar jam’iyyun siyasa (IPAC), ta yi barazanar kin halartar zaben idan ba a gyara wasu tanade-tanaden doka ba, da yawan jam’iyyun siyasa sun fara daidaita hanyoyin cikin gida don ya dace da sabin abubuwan da ake bukata.

  • Sin Ta Himmatu Wajen Raya Ci Gaban Duniya Na Bai Daya
  • Kawar Da Dukkanin Haraji Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar Sin Daga Afirka Zai Bunkasa Cinikayyar Albarkatun Gona Na Afirka Ta Kudu

Binciken shirye-shirye a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa ya nuna cewa an samu mabambantan ra’ayoyi. Yayin da wasu jam’iyyun ke cewa sun shirya don tunkarar zaben, wasu na fama da kalubale na kudade da rikice-rikicen cikin gida da kuma gyare-gyaren gudanarwa da sabon tsarin zaben ya bukata.

ADVERTISEMENT

Bayan amincewa da kudirin dokar zabe na 2026, INEC ta saki sabon jadawalin zabukan 2027, ta saka ranakun zaben shugaban kasa da na majalisun kasa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Daya daga cikin manyan sauyin da dokar ta tanada shi ne, ana bukatar jam’iyyun siyasa su fitar da ‘yan takara ta hanyar zaben fid da gwani na kai tsaye ko kuma ta hanyar yarjejeniya, wanda ya kawar da tsarin wakilai da ake amfani da su a jam’iyya a baya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku

2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Wani tanadin kuma ya hana kotuna dakatar da ayyukan zabe yayin da shari’o’i suke cikin jiran hukunci.

Bugu da kari, ana bukatar jam’iyyun siyasa a yanzu su kiyaye cikakken rajistar mambobinsu ta intanet wanda ya kunshi bayanan sirri, ciki har da lambobin shaidar dan kasa (NIN).

Dole ne a gabatar da rajistar ga INEC akalla kwanaki 21 kafin zabukan fitar da gwani na jam’iyyu da babban tarurrukan jam’iyyu.

Wadannan sabbin bukatu sun tilasta wa jam’iyyun siyasa a Nijeriya sauye-sauyen cikin gida da shirye-shiryen gudanarwa.

Jam’iyyar LP karkashin jagorancin, Sanata Nenadi Usman, tana kokarin samun kudade wajen sake gina tsarinta kafin zaben 2027.

Bayan fitowar sabon jadawalin zabe da INEC ta fitar, jam’iyyar ta kara matsa kaimi wajen sake tabbatar da rajista mambobinta a fadin kasa nan. Sakamakon rikice-rikicen cikin gida da karancin kudade da jam’iyyar take fuskanta ya rage mata tagomashi cikin ayyukanta.

Rahotanni sun nuna cewa yanayin ya kawo wa jam’iyyar cikas wajen shirya tarukanta a fadi kasar nan, inda wasu jami’ai ake cewa suna tallafa wa ayyukan jam’iyya daga dukiyoyinsu na kashin kai.

Tsohon sakataren watsa labarai na wucin gadi na jam’iyyar, Mista Tony Akeni, ya nuna damuwa game da yanayin da jam’iyyar take ciki a wata sanarwar da ya fitar.

“A matsayina na tsohon sakataren watsa labarai na wucin gadi na jam’iyyar LP, na tilasta wa kaina yin hijira daga Jihar Edo zuwa Abuja a ranar 7 ga Agusta, 2025.

“Tun daga wannan lokaci, ina gudanar da dukkan ayyukana a ofis daga masaukin otel ba tare da samun kobo daga jam’iyyar LP ko masu ruwa da tsaki ba, sai dai kudi data da aka taba ba ni na naira 10,000,” in ji shi.

Ya bayyana lamarin a matsayin wata manufar jam’iyya da ta samu kanta na kowa ya dauki nauyin kansa wadda ke raunana ayyukan jam’iyyar.

Duk da wadannan tarin matsaloli, jam’iyyar LP ta riga ta mika jerin sunayen mambobin kwamitin gudanarwarta na jihohi 32 da Babban Birnin Tarayya Abuja, ga INEC a matsayin wani bangare na kokarin sake tsarin jam’iyyar.

Sanata Nenadi-Usman ta kuma nuna amincewa da karfafa jam’iyyar a matakin kasa, ta lura cewa masu goyon bayan jam’iyyar suna karuwa a dukkan sassan kasar nan baki daya.

Ita kuwa jam’iyyar APGA ta ce ta riga ta dauki matakai masu muhimmanci don bin sabon tsarin zabe.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Mazi Ejimofor, ya ce APGA ta fara rajistar mambobinta ta intanet tun daga ranar 1 ga Yuni, 2024, kafin cikar wa’adin dokar zabe.

“Mun shirya sosai saboda idan ka duba abin da APGA ke yi, ko kafin yanzu, za ka fahimci cewa alama mun riga mun dauki matakin dokar zabe.

“Mu ne jam’iyya ta farko da ta fara yin rajistar mambobita ta intanet tun ranar 1 ga Yuni, 2024,” in ji shi.

APGA ta kuma bukaci INEC ta tabbatar da cewa ka’idojinta sun yi daidai da na dokar zabe, kuma ka da ta kirkiro wasu karin matsaloli ga kananan jam’iyyun siyasa.

A halin yanzu, jam’iyyar APC mai mulki ta ce ta kara yin shiri domin zaben 2027 tare da amfani da bayanan mambobi na fasaha da sabon tsarin doka ya zo da shi.

Shugaban jam’iyya APC ta kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa APC yanzu tana da wani ingantaccen tsarin bayanai na intanet ga mambobita sama da miliyan 10 da aka hada da lambobin shaidar dan kasa.

“Rijistarmu ta intanet tana ba mu damar samun bayanan mambobinmu. Mun san ko su wane ne, inda suke zaune da kuma yadda za mu isa gare su. Wannan yana ba mu damar tattarawa yadda ya kamata da kuma gudanar da zabukan fid da gwani mafi kyau,” in ji shi.

Yilwatda ya kuma ce shawarar jam’iyyar ta yi aiki ba tare da kwamitin amintattu ba. Yana mai jaddada cewa APC na so mambobinta su dauki nauyin mallakar jam’iyyar.

A matsayin wani bangare na shirin zaben 2027, jam’iyyar ta kaddamar da kwamitin shirya babban taronta na kasa, wanda tsohon shugaban majalisar wakilai, Aminu Bello Masari, ke jagoranta.

Kazalika, jam’iyyar PDP ta kuma ce ta shirya sosai don tunkarar zaben 2027, duk da rashin jituwa da rikicin cikin gida da take fama a kotu.

Mataimakiyar sakatariyar yada labarai ta PDP, Farida Umar, wadda ta nuna amincewa da shirin jam’iyyar, ta ce, “Mun shirya sosai. Mun kasance a shirye kuma a sahun gaba don karbar mulki daga wannan gwamnati mai rashin tabbas ta Bola Tinubu da jam’iyyar APC.

“Mun gudanar da tarukanmu daga matakin karamar hukuma zuwa matakin jiha kuma mun dauki duk matakan da suka dace don kasancewar PDP.”

Umar ya kuma ki amincewa da cewa raguwar yawan gwamnonin jam’iyya zai iya shafar karfinta na tara kudi.

Sakataren yada labarai jam’iyyar PDP ta kasa, Ini Ememobong, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta fara yin rajistar ‘yan jam’iyya ta yanar gizo bisa bin sabon dokar zabe.

Haka kuma jam’iyyar ADC ta yi gargadin kan jaddawalin da INEC ta fitar cewa dokokin sun yi wa jam’iyyun adawa tsauri.

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce bukatar yin rajistar mambobin jam’iyyu ta intanet a dan gajeren lokaci ba abu ne mai yiwuwa ba.

“Kusan yana da wuya mu yi wannan a aikace. Abin da jam’iyyar gwamnati ta dauki fiye da shekara guda tana yi shi ne abin da suke sa ran mu yi cikin wata daya,’’ in ji shi.

A cewarsa, yanayin na iya kawo rashin amfani ga jam’iyyun adawa.

Duk da wannan yanayin, jam’iyyun siyasa a fadin kasar suna kara yin shiri wajen tunkarar zaben 2027.

2027
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

MASU ALAKA

Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku
Tambarin Dimokuradiyya

Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku

June 19, 2026
2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

June 12, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

June 12, 2026
Next Post
Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar 

Arsenal Na Tattaunawa Da Declan Rice Kan Tsawaita Kwantiraginsa A Ƙungiyar 

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

June 25, 2026
An Fara Gasar Tseren Dawakai Ta ‘Renewed Hope’ da Sabon Salo A Kano

An Fara Gasar Tseren Dawakai Ta ‘Renewed Hope’ da Sabon Salo A Kano

June 25, 2026
APC Ta Dage Yakin Zaben Shugaban Kasarta A Kano

An Dakatar Da Shugaban APC Na Kebbi Da Kwamishina Kan Zaɓen Cike Gurbin Zuru

June 25, 2026
Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

Ndume Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Yake Goyon Bayan Ƙudirin Kafa ‘Yansandan Jihohi

June 25, 2026
EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

EFCC Za Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah Kan Zargin Almundahanar Dala Miliyan 2.53

June 25, 2026
Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

Maroko Ta Zama Ƙasa Ta Farko Daga Afirka Da Ta Tsallaka Zuwa Zagaye Na 32 A Gasar Kofin Duniya

June 25, 2026
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa — Atiku

June 25, 2026
Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.