ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Fitar Da Gwani Na APC: Tinubu Zai Shiga Tsakani Wajen Warware Rikicin Jam’iyyar

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
APC

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tsoma baki kan rikicin da ya biyo bayan zaben fid da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a fadin kasar nan, tare da alkawarin magance koke-koke da suka taso, musamman a jiharsa ta Legas.

Wani majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa, ta ce an fara aiwatar da aikin kuma shugaban kasa da shugabannin jam’iyyar za su duba lamarin.

Haka kuma majiyar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya umarci ‘yarsa, Hajiya Folashade Tinubu-Ojo, da ta dakatar da shirin zanga-zangar da aka tsara kan sakamakon zabuka a Legas har sai an warware koke-koken da ‘yan takara da masu ruwa da tsaki suka bayyana.

ADVERTISEMENT

Tinubu-Ojo, a yayin wani taro da shugabannin ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a ofishinta a Alausa, makon da ya wuce, ta yi barazanar yin zanga-zanga kan abin da ta bayyana a matsayin rashin daidaito a wajen gudanar da zaben fitar da gwani.

Majiyar fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa bai ji dadin rahotannin da ke nuna cewa wadanda aka dora musu alhakkin gudanar da harkokin jam’iyya a Legas na iya yin abin da ya saba wa ra’ayin mambobin jam’iyya ba.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Majiyar ta kara cewa za a sake duba duk korafe-korafen da suka taso daga zaben fitar da gwani a dukkan fadin kasar nan bayan dawowar shugaban kasa Abuja.

A yayin martani ga tarurrukan da aka yi tsakanin wasu ‘yan takara da aka bayyana da Shugaba Tinubu a lokacin hutun Sallah a Legas, majiyar ta ce bai kamata a fassara irin wadannan haduwa a matsayin tabbacin takararsu ba.

“Duk wadannan tarurrukan an shirya su a matsayin wani bangare na tafiyar shugaban kasa tun kafin a gudanar da zaben fid da gwani. Don haka, ganawa da ‘yan takarar da aka sanar da shugaban kasa ba ya sanya su masu nasara kai tsaye.

“Shugabancin kasa zai duba kiran kuma ya yanke shawara ta karshe. Ba a Jihar Legas kadai ba ne. A duk fadin kasar ne. Wannan shi ya sa tikitin da aka tabbatar kawai har yanzu shi ne na shugaba kasa kadai,” in ji majiyar.

APC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Harkokin Kasuwanci

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Harkokin Kasuwanci

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.