Dakarun rundunar haɗin gwuiwa ta Arewa maso Yamma da ke gudanar da aikin ‘Operation FANSAR YAMMA’ sun samu nasarar halaka wasu ‘yan ta’adda da kuma kama wani mutum mai shekaru 57 wanda ake zargi da yin safarar makamai. Mutumin an kama shi ne ɗauke da abubuwan fashewa guda 180 da ya ke kan hanyar kai wa ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja ya fitar, ya bayyana cewa, jami’an na Sector 2 sun gudanar da aikin sintiri a ƙaramar hukumar Birnin Magaji a ranar 14 ga watan Agusta 2026, inda suka yi arangama da ‘yan ta’addan a yankin Garin Kaso tare da yin musayar wuta mai tsanani. An tabbatar da kashe ‘yan ta’adda biyu a karon farko, yayin da dakarun suka kwato bindigu biyu, sinƙin harsasai guda tara, da kuma babura guda biyu.
Laftanar Kanar Danja ya ƙara da cewa, wani gungun ‘yan ta’adda sun yi yunƙurin yi wa sojojin kwantan ɓauna a yayin da suke sintirin, amma dakarun sun mayar da martani mai zazzafa inda suka fatattaki maharan sannan suka tilasta wa sauran guduwa. .
Koda yake ba a san ainihin yawan waɗanda suka mutu a harin na biyu ba, rahotanni daga yankin sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun jidi gawarwakin ‘yan uwansu da suka mutu da kuma waɗanda suka samu raunuka daga harbin bindiga.
A wani ci gaban kuma a ranar, dakarun sun cafke wani mai suna Sani Umar, ɗan shekara 57, a lokacin da suke gudanar da bincike akan ababen hawa. Binciken motarsa ya sa an gano abubuwan fashewa guda 180 kirar ‘Super Power’ wanda ake zargin ana jigilarsa ne daga ƙaramar hukumar Gusau don kai wa ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Jibia ta Jihar Katsina.
A halin yanzu ana tsare da wanda ake zargin, da motarsa da kuma abubuwan fashewar don gudanar da bincike.














