Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce ya kafa Jami’ar American University of Nigeria (AUN) da ke Yola, Jihar Adamawa, ne domin zuba jari a fannin ilimi da kuma taimakawa wajen bunƙasa Arewa, ba wai domin neman riba ta ƙashin kansa ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da yake mayar da martani ga wani mai amfani da kafar sadarwar da ya tambaye shi irin gudunmawar da ya bayar wajen magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa. Ya ce da manufarsa ita ce samun riba, da ya fi dacewa ya kafa jami’ar a Abuja ko Legas, inda damar kasuwanci ta fi yawa.
Ya ce zaɓin Yola ya samo asali ne daga burinsa na samar da damarmaki ga al’ummar yankin da kuma kawo ilimi mai inganci kusa da mutanen da suka daɗe suna buƙatarsa. Atiku ya kuma bayyana cewa jami’ar ba mallakarsa ko ta iyalinsa ba ce yanzu, bayan da ya sanya hannu kan takardar bayar da ita ga al’umma, yana mai cewa AUN ta zama mallakin al’ummar da aka kafa ta domin yi wa hidima.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen AUN na tallafa wa yara masu rauni, ciki har da shirin Feed and Read, wanda ke samar da abinci ga yara Almajirai tare da koyar da su karatu da lissafi. Ya ce wani shiri na amfani da fasahar sadarwa wajen koyarwa ya taimaka wa fiye da yara 20,000 da suka rasa matsugunansu sakamakon rikice-rikice wajen koyon karatu ta shirye-shiryen rediyo.
Atiku ya kuma ce jami’ar ta bayar da tallafin karatu ga wasu daga cikin ƴan matan da suka tsere daga hannun Boko Haram bayan sace ɗaliban Chibok a 2014. Ya jaddada cewa ganin yara suna bara a titunan Nijeriya ya kamata ya damu kowane ɗan ƙasa, yana mai cewa burinsa shi ne ganin kowane yaro a makaranta maimakon yawo da kwanon bara.














