Ministan Ayyuka, Injiniya Daɓid Umahi, ya ce gwamnatin tarayya za ta tura jami’an tsaro domin kare ababen more rayuwa da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano daga lalatawa da masu zagon ƙasa.
Umahi ya bayyana hakan ne ranar Litinin lokacin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS) waɗanda suka kai masa ziyarar girmamawa a ma’aikatar.
Ya ce ɗaukar wannan mataki ya zama dole ne sakamakon ƙoƙarin wasu masu lalata dukiyoyin gwamnati na lalata sabbin sassan manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.
Ya ce: “Yanzu na dawo daga Lagos inda muka ƙaddamar da jami’an tsaron babbar hanyar gaɓar teku. Za mu ƙaddamar da irin wannan tsaro a kan babbar hanyar Abuja, Kaduna, Zaria, Kano.
“Na ga wasu mutane suna haƙa siminti domin cire sandunan ƙarfe. Amma na ce idan za su iya yin irin wannan aiki, to za mu ba su wani aiki mai amfani.”
Ministan ya ce hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano, wadda ta kai kimanin kilomita 750 na titin mota, ta samu sama da Naira biliyan 200 daga gwamnatin tarayya, yayin da ayyukan da ake gudanarwa a kan hanyar a yanzu suka kai darajar Naira biliyan 752, kuma an riga an biya sama da kashi 80 cikin 100 na kuɗin.
Ya ce gwamnati na fatan cewa kafin watan Nuwamba za a kammala dukkan sassan hanyar, inda ya ƙara da cewa za a girka fitilu masu amfani da hasken rana a gefen babbar hanyar.
Umahi ya ce ayyukan hanyoyin da gwamnati ke gudanarwa sun samar da guraben aikin yi a sassa daban-daban na ƙasar, inda ya bayyana cewa: “Babu wani wurin aiki a cikin waɗannan ayyukan da ke da ma’aikata ƙasa da mutane 1,000.”














