Duk da cewa sayen makamai da ƙasashen Afirka ke yi daga ƙasashen ƙetare ya ragu da kimanin kashi -41, kamar yadda Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya ta Stockholm (SIPRI) ya nuna, amma ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara sun ƙara yawan makaman da suke saye.
Wannan labarin ya yi nazari kan ƙasashen Afirka 10 da ke kudu da hamadar Sahara waɗanda suka fi sayen makamai, kamar yadda cibiyar ta SIPRI ta bayyana.
Ƙasashe kamar Nijeriya da Senegal da Mali na daga cikin waɗanda suka fi sayen makamai daga ƙasashen ƙetare, in ji rahoton, kamar yadda darakatan nazari kan harkar makamai na cibiyar, Dr Mathew George ya yi bayani.
Nijeriya
Nijeriya ce ƙasar da ta fi kowace sayen makamai daga ƙetare a cikin ƙasashen Afirka da ke kudu da hamada.
Nijeriya ce ke da kashi 16 na yawan makaman da ƙasashen ke saye.
Makaman da Nijeriya ta fi saye su ne jiragen yaƙi da jiragen soji masu saukar ungulu da motocin sulke da jiragen ruwa da kuma jirage marasa matuƙa.
Nijeriya na sayen makamanta ne daga ƙasashe daban-daban. Daga cikin irin waɗannan ƙasashe akwai Turkiyya da Koriya ta Kudu da China da Netherlands da Faransa da Italiya da Brazil da Amurka da Rasha da Afirka ta Kudu da Pakistan da Canada da Saudiyya da Austria da kuma Malaysia.
Nijeriya ce ke sayen kashi ɗaya cikin shida na makaman da ke zuwa ƙasashen Afirka da ke kudu da Sahara.
Senegal
Senegal ta yi yunƙuri sosai wajen haɓaka ƙarfin sojinta. An yi ƙiyasin cewa tana da kashi 8.8 na makaman da ƙasashen Afirka ke saye.
Ita ce ƙasa ta biyu mafi sayen makamai a yankin, inda take sayen jiragen sojin ruwa domin tsaron bakin gaɓar tekunta da haƙar ɗanyen man fetur a teku, sannan kuma tana sayen jiragen yaƙi da kuma na tattara bayanan sirri.
Senegal ta sayi makaman kai hari kan jiragen ruwa da motoci masu sulke da makaman atilare.
Ƙasar na sayen makamai ne daga ƙasashen Faransa da Bulgaria da China da Afirka ta Kudu da Indonesia da Denmark da Italiya da Jamus da Amurka da Turkiyya da Spaniya da kuma Canada.
Mali
Ƙarfin sojin ƙasar Mali ya riƙa ƙatuwa tun daga shekara ta 2020. Yaƙin da ƙasar ke yi da ƙungiyoyin ƴan bindiga shi ne silar ƙara ƙarfin sojin.
Mali ta zamo ƙasa ta uku mafi sayen makamai tsakanin ƙasashen Afirka, kuda da Sahara.
Ƙasar ta zuba maƙudan kuɗaɗe, wanda hakan ya sanya take da kashi 80 na dukkanin makaman da ƙasashen Afirka, kudu da Sahara ke saye.
Mali ta sauya ƙasashen da take hulɗar tsaro da su, inda yanzu ta karkata zuwa ga Rasha bayan saɓanin da ta samu da Faransa.
Mali ta sayi kayan yaƙi kamar motpoci masu sulke da jiragen ɗaukar dakaru da jiragen yaƙi da manyan makaman atilare da makamai masu linzami da sauran su.
Ethiopia
Sanadiyyar rikicin gida na yankin Tigray, ƙasar Habasha ta riƙa sayen jirage marasa matuƙa, waɗanda ta dogara sosai a kansu.
Haka nan ƙasar ta sayi jiragen saman yaƙi da makaman atilare da motocin sulke da na ɗaukar dakaru sai kuma jiragen horo da na kai hari.
Ethiopia na sayen makamanta ne daga ƙasashen Rasha da Turkiyya da Iran da Amurka da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Bosnia.
Angola
Angola wadda ta daɗe tana fama da yaƙi ta shafe kimanin shekara biyar tana sayen makamai, inda makaman da ta saya suka kai kashi 4.7 na makaman da ke shiga ƙasashen Afirka, kuda da Sahara.
Angola ta fi mayar da hankali ne kan tsaron bakin iyaka da kuma sararin samaniyarta.
Makaman da take saye sun hada da injunan jiragen sama da jiragen kwale-kwalen soji.
Ƙasar kan sayi makamanta ne daga ƙasashe kamar Spanin da Belarus da Faransa da kuma Canada.
Kenya
Kenya na fuskantar matsalar tsaro musamman a kan iyakokinta, inda ake sake samun ɓarkewar hare-haren ƙungiyar Al-Shabab da kuma sauran ayyukan laifuka, musamman a arewa maso gabashin ƙasar da kuma Nairobi, babban birnin ƙasar.
Domin shawo kan matsalar, Kenya ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayen makamai.
Ta sayi makamai kamar jiragen ɗaukar dakaru da jiragen saman yaƙi da makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuƙa na Bayraktar TB-2 da kuma jirage masu saukar ungulu daban-daban, ciki har da Hughes-500D.
Ƙasar na sayen makamai ne daga ƙasashe kamar Hadaddiyar Daular Larabawa da Jamus da Isra’ila da Turkiyya da Amurka da kuma Koriya ta Arewa.
Mauritania
Duk da cewa Mauritania na daga cikin ƙasashe masu zaman lafiya a yankin Sahel, ƙasar na fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci a kan iyakokinta na arewa da kuma gabashi, musamman yankunan da take iyaka da ƙasashen Algeria da Mali.
Ƙasar ta sayi makamai masu linzami da ke kai hari kan tankokin yaƙi da jiragen jigilar dakaru da sauran motocin yaƙi, sannan ta sayi garkuwa daga makamai da kuma motocin sulke.
Burkina Faso
Burkina Faso ta shafe shekaru tana fama da rikicin ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, lamarin da ya haifar da ɗimbin asarar rayuka da tarwatsa al’umma daga muhallansu.
Ƙasar ta sayi makamai masu linzami da bama-bamai da motocin sulke da jiragen yaƙi da masu saukar ungulu da makaman atilare da kuma jirage marasa matuƙa da sauran su.
Iɓory Coast
Duk da cewa akwai kwanciyar hankali a kudancin ƙasar, Cote d’Iɓoire na sanya ido sosai kan yankunan arewaci, inda take iyaka da Burkina Faso da kuma Mali, wuraren da ake samun barazanar hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Iɓory Coast ta sayi makamai da suka haɗa da jirage masu saukar ungulu na AS-350 da H-125, da jirage masu saukar ungulu na kai hari da motocin sulke da kuma ƙananan jiragen ruwan sintiri na gaɓar teku.
Rwanda
Rwanda ta ƙara ƙarfin garkuwarta ta hare-garen sama, inda makaman da ta saya suka kai kashi 3.5 na makaman da ƙasashen Afirka, kudu da Sahara ke shigarwa.
Makaman da Rwanda ta saya sun haɗa da jirage masu saukar ungulu na kai hare-hare da motocin sulke da makaman kakkaɓo makamai masu linzami da kuma wasu da dama.
Me Ya Sa Trump Ke Neman Ɗauki Daga Ƙungiyar NATO A Yaƙin Iran?
Shugaba Trump ya ce yana tattaunawa da ƙasashe da dama domin taimakawa wajen ƙwace ikon mashigar Hormuz a daidai lokacin da yaƙinsa da Iran ke ci gaba da illa ga tattalin arzikin duniya.
Sai dai Mista Trump ya yi gargaɗi ga ƙungiyar tsaro ta NATO idan har ba ta taimaki Amurka ba.
“NATO za ta fuskanci mummunar makoma,” kamar yadda shugaban ya bayyana a wata hira da ya yi da jaridar Financial Times.
Shugaban ya sake yin kira ga ƙasashe su shiga ƙoƙarin tabbatar da buɗe mashigar Hormuz da yake yi domin ba jiragen ruwa damar tsallake shingen Iran.
Ya ce Amurka ta taimaka wa Ukraine a yaƙinta da Rasha, don haka yana tsammanin taimakon ƙasashen Turai kan babbar hanyar ruwa ta Hormuz da Iran ta toshe.
Rufe mashigar dai ya haifar tsadar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Mista Trump ya kuma ce zai jinkirta taron da zai yi da shugaban China Ɗi Jinping yayin da yake matsin lamba ga taimakon China domin buɗe mashigar.
Trump ya ce China da ƙasashen Turai da dama sun fi dogaro fiye da Amurka kan man da ke fitowa daga yankin Tekun Fasha.
“Waɗanda suka fi amfana da mashigin ne ya kamata su taimaka domin tabbatar da wani mugun abu bai faru ba a can,” in ji Trump.
Ya shaida wa manema labarai cewa Amurka na tattaunawa da kusan ƙasashe bakwai domin neman taimakon su sa hannu wajen ceto mashigar Hormuz.
Tuni ƙasashen Japan da Australia suka ce ba za su tura sojojin ruwa ba. Amma Japan ta ce za ta fara fitar da rarar manta domin rage giɓin da na Iran ya haifar, duk da cewa ita ma ta dogara ne da man da ke fitowa daga yankin Gabas Ta Tsakiya.
Babu tabbas game da tsawon lokacin da yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran zai ɗauka da kuma tasirin da zai yi ga kasuwar mai a duniya, inda farashin ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zaɓi a cikin makwanni biyun da suka gabata sakamakon ƙarancinsa.















Discussion about this post