ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙungiyar NUJ Ta Karrama Shugaba Da Babban Editan Kamfanin LEADERSHIP A Abuja

by Sani Anwar
4 months ago

A ranar Talata ne Shugabar kamfanin jaridar LEADERSHIP Zainab Nda-Isaiah da Babban Editan Jaridar Mista Azu Ishiekwene suka karɓi lambar girmamawa daga ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa reshen Babban Birnin Taratyya Abuja.

A jawabin ta, Shugabar Jaridar LEADERSHIP, Zainab Nda-Isaiah, ta yaba da tsayin daka, jajircewa da kuma ƙwarewar ƴan jaridan Nijeriya, inda ta bayyana jajircewarsu a matsayin wani ginshiƙi na ɗorewar demokuraɗiyya, duk da cewa; suna gudanar da aikin nasu cikin yanayi mai matuƙar wahala.

Ta gabatar da wannan yabo ne a ranar Talata a Abuja, yayin bikin makon manema labarai na ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ), na 2026.

ADVERTISEMENT

Da take magana a wajen taron ƙwararrun, Nda-Isaiah ta bayyana yadda ta samu kanta a shugabancin jaridar LEADERSHIP, inda ta bayyana cewa; ta ɗauki gagarumin nauyi tun a farko, wanda ba ta taɓa tsammanin ɗauka ba.

Ta ce: “Tafiya ce wadda kawai ta zo min ɓagatatan, wadda kuma dole ne na sanya takalmin, wanda ko da wasa ban taɓa tsammanin zan iya sanyawa ba,” in ji ta.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Kazalika, ta danganta ci gaban kafafen yaɗa labaru da jajircewar ƴan jarida da kuma ƙwararrun, waɗanda a cewarta; suke jajircewa wajen ganin cewa, “duk abin da Nijeriya ta samar, za mu faɗa, ta hanyar jin muryoyinmu.”

Nda-Isaiah ta bayyana yanayin gudanar da aikin ƴan jarida, a matsayin mai matuƙar ƙalubale, inda ta yi nuni da cewa; har yanzu kafafen yaɗa labarai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga gwamnatocin siyasa daban-daban.

Haka zalika, ta yaba wa ƴan jaridar, sakamakon kiyaye mutuncin sana’ar da kuma ci gaba da faɗin gaskiya ga masu mulki, duk kuwa da kasadar da ke tattare da yin hakan.

Ta kuma ƙara da cewa, ƴan jarida sukan yi aiki a wurare masu matuƙar haɗari, musamman ta fuskar faɗin gaskiya, amma duk da haka suna ci gaba da kiyaye ƙa’idojin  da kuma yin kula a cikin rahotannin da suke bayarwa.

Nda-Isaiah ta bayyana yanayin gudanar da aikin ƴan jarida a matsayin mai matuƙar ƙalubale, inda ta yi nuni da cewa; har yanzu kafafen yaɗa labarai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga gwamnatocin ƴan siyasa daban-daban.

Shugabar Jaridar LEADERSHIP ɗin, ta kuma yaba wa manyan ƴan jarida, ciki har da Babban Editan Jaridar, Mista Azu, wanda ta bayyana a matsayin ginshiƙin bayar da tallafi, wanda jajircewarsa take taimaka wa ƙungiyar.

“Ba zan iya bayyana irin tallafi da gudunmawar da shi kansa da sauran mutanen da ke wannan kamfani na LEADERSHIP suka bayar ba, shi ya sa har yanzu muke tsaye da ƙafafunmu,” in ji ta.

Nda-Isaiah, wacce ta yarda da cewa; ita ba ƙwararriyar ƴar jarida ba ce, amma kuma ta dangantakar danginta da wannan aiki na jarida, inda ta bayyana shi a matsayin sana’a mai tushe da sha’awa da kuma gado.

A ƙarshe, ta bayyana godiyarta ga ƴan jarida, kan ci gaba da yi wa ƙasa hidima, inda ta ce; tsayin daka da sadaukarwar da suke bayarwa ta sa sana’ar take ci gaba da wanzuwa tsawon zamani.

Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
Sanata Jibrin Ya Musanta Janyewa Daga Takarar Sanatan Kogi Ta Gabas

Sanata Jibrin Ya Musanta Janyewa Daga Takarar Sanatan Kogi Ta Gabas

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.