ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: APC Ta Soki Atiku Kan Alƙawarin Dawo Da Tallafin Man Fetur

by Sadiq
3 weeks ago

Jam’iyyar APC ta soki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kan alƙawarin da ya yi na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya yi wannan alƙawari ne yayin wani tattaunawa kai-tsaye da aka yi a shafinsa na Facebook.

Ya ce da farko bai yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma yanzu ya canja ra’ayinsa.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, har yanzu ba a bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka aka samu bayan cire tallafin ba.

Atiku ya tambayi ko an yi amfani da kuɗaɗen wajen inganta harkokin lafiya, ilimi da tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, zai dawo da tallafin man fetur.

Ya kuma ce duk wanda ya sace kuɗaɗen tallafin zai dawo da su.

Sai dai Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya soki matakin na Atiku.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Morka ya ce Atiku ya sauya matsayinsa daga goyon bayan cire tallafin man fetur a 2023 zuwa alƙawarin dawo da shi a 2027.

Morka ya bayyana matakin na Atiku a matsayin alamar buƙatar samun goyon bayan jama’a.

Ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai fahimci halin da tattalin arziƙin Nijeriya ke ciki ba kuma bai gabatar da wata ingantacciyar manufar tattalin arziƙi a matsayin madadin cire tallafin ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
“Shirin Shekaru Biyar-biyar Na Uku” Na Macau Ya Rubuta Sabon Babi Na Nasarar Aiwatar Da Manufar “Kasa Daya, Tsarin Mulki Biyu”

“Shirin Shekaru Biyar-biyar Na Uku” Na Macau Ya Rubuta Sabon Babi Na Nasarar Aiwatar Da Manufar “Kasa Daya, Tsarin Mulki Biyu”

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.