ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Ba Ni Da Wani Ɗan Takara Da Nake Mara Wa Baya — Sarkin Musulmi

by Rabi'u Ali Indabawa
1 month ago
sarkin musulmi

Sarkin Musulmi na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya musanta wani rahoto da ke yawo a wasu kafofin sada zumunta da ke cewa ya buƙaci ƴan Nijeriya su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da Sashen Yaɗa Labarai na Sarkin Musulmi ya fitar ta hannun Prince Bashir Adefaka a ranar Talata, an buƙaci ƴan Nijeriya daga kowane ɓangare na al’umma da su yi watsi tare da yin Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin wani mugun ƙoƙari da ba na kishin ƙasa ba, na jawo martabar Sarkin Musulmi cikin siyasar jam’iyyu domin cimma muradun wasu.

Sanarwar ta ce: “ Cibiyoyin masarauta da addini da Sarkin Musulmi ke jagoranta cibiyoyi ne na uba ga kowa. Saboda haka, Mai Alfarma ba zai kauce daga wannan matsayi ba, inda yake bai wa ƴan siyasar Nijeriya shawara, albarkar sarauta da ta addini, da kuma jagoranci idan suka nemi hakan.

ADVERTISEMENT

Ƙofofin Sarkin Musulmi a buɗe suke ga duk wanda ya zo wajensa, ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ko ra’ayinsa na siyasa ba. A kodayaushe Mai Alfarma ya nuna cewa shi uba ne ga kowa, kuma zai ci gaba da mu’amala da dukkan ƴan Nijeriya ba tare da nuna bambanci ba.”

Saboda haka, Sashen Yaɗa Labaran ya yi kira ga jama’a da su ƙi duk wani yunƙuri na karkatar da matsayin Sarkin Musulmi ko danganta shi da yaƙin neman zaɓe ko takarar kowane mutum gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Sashen ya jaddada cewa Sarkin Musulmi, bisa matsayinsa na uba ga dukkan ƴan Nijeriya, zai ci gaba da jajircewa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da zaman tare cikin lumana tsakanin al’ummomi da mabiya addinai daban-daban a Nijeriya.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ƴan jarida da masu amfani da kafofin sada zumunta da su kasance masu bin ƙa’idojin aikin jarida ta hanyar tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su, domin kauce wa ruɗar da jama’a ko jefa manyan cibiyoyin gargajiya da na addini cikin rikice-rikicen siyasa na jam’iyyu.

sarkin musulmi
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
sarkin musulmi

Wani Jigon APC A Kebbi Ya Fice Daga Tafiyar Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.