Wani jigon jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kebbi Adamu Yahaya ya sanar da janye goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a shekara ta 2027.
Jigon jam’iyyar ya bayyana wannan mataki ne sakamakon abin da ya ƙira rashin cika alƙawuran da aka ɗauka wa al’umma da kuma ƙaruwar matsin tattalin arziki da jama’ar ƙasa ke fuskanta.
Wannan mataki da jigon jam’iyyar ya ɗauka ya haifar da kace-nace a tsakanin mambobin jam’iyyar mai mulki a Jihar Kebbi, yayin da wasu ke kallon matakin a matsayin wani babban ƙalubale ga haɗin kan jam’iyyar a yankin.
Mazauna da masu lura da al’amuran siyasa a jihar sun bayyana cewa wannan sauyin sheka ko janye goyon baya zai iya haifar da mummunan tasiri ga tsarin tafiyar da siyasar jam’iyyar APC a Arewa maso Yamma masamman gabanin zaɓuka masu zuwa.














