ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Sabuwar Muhawara Ta Kaure Kan Cancantar Tinubu

by Yusuf Shuaibu
1 month ago
Tinubu

Fitar da sunan Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi, ya sake tada da zazzafar muhawara kan cece-kuce game da takardun karatunsa, wanda ya fara fitowa tun a zaɓen 2023.

Wannan dai kamar yadda INEC ta bayyana cewa ba ta bincikar sahihancin takardun karatu da sauran shaidar da ƴan takara suka gabatar kafin a fitar da sanyasu.

A cikin takardun cancantar ƴan takarar shugabancin da INEC ta fitar a ranar Asabar, INEC ta saka cewa Tinubu ya samu shaidar digiri a fannin kimiyyar kasuwanci daga jami’ar Chicago da ke ƙasar Amurka a shekarar 1979, ba tare da wani takardar shaidar makarantar firamare ko sakandare a cikin takardun da aka bayyana ba.

ADVERTISEMENT

Wuraren da aka tanada don saka shaidar karatun firamare da sakandare ba a cika su ba. Akwai an saka takardar digiri na shugaban da takardar shaidar kammala bautar ƙasa (NYSC) a matsayin takardunsa.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya lissafa ƙwarewarsa ta shadai karatun firamare da ya samu a 1954 da na sakandare da ya samu a 1961 ba tare da ambaton sunayen makarantu ba. Haka nan ya nuna cewa ya samu digiri na biyu a 2020 daga jami’ar Anglia Ruskin.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Shi kuwa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya nuna cewa ya halarci makarantar firamare ta St. Augustine, Anambra (1973) da makarantar sakandare ta Christ the King College a 1978 da kuma jami’ar Nijeriya ta Nsukka, inda ya samu digiri a fannin falsafa a 1984.

Rashin ambaton takardun makarantar firamare da sakandare na Tinubu ya dawo da tunanin gwagwarmayar shari’a da ta biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lokacin da Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya zargi cewa ya miƙa takardun bogi ga INEC.

A wancen lokaci, duk da cewa jami’ar Amurka ta tabbatar cewa Tinubu ya kammala karatunsa daga wannan makaranta a shekarar 1979, rikice-rikice kan takardar shaidar digiri da ake zargin an miƙa wa INEC sun zama ɗaya daga cikin manyan batutuwa a shari’ar bayan zaɓen. Kotun sauraron ƙarar zaɓen shugaban ƙasa da kotun ƙoli sun yi watsi da ƙarar tare da tabbatar da zaɓen Tinubu.

A cikin tambayoyi daban-daban da aka yi, lauyoyi da jam’iyyun adawa sun tambayi dalilin da ya sa ba a saka takardun shaidar makarantar firamare da sakandare na shugaban ƙasa a cikin takardun da hukumar zaɓe ta fitar ba.

Sun ce rashin saka takardun ya sake sanya damuwar jama’a da ba a warware ba game da cancantar karatun Tinubu, suna kiran a yi ƙarin gaskiya wajen bayyana takardun ƴan takara.

Wani babban lauya a Nijeriya, Mumini Jimoh, ya ce karatun makaranta har zuwa matakin sakandare na daga cikin manyan sharuɗɗan da ake buƙata ga ƴan takarar shugaban ƙasa, wanda hakan ke sa kusan ba zai yuwu ba ga wanda bai samu wannan takardu ba.

Shi ma wani babban lauya, Mohammed Abeni, ya ce rashin ambaton shaidar makarantar sakandare daga cikin takardun da aka ɗora yana haifar da tambayoyi da kuma shakku, musamman ma a ciki halin da ake ciki na cece-kuce da suka biyo baya kan bayyanan ilimin shugaban ƙasa.

Ƙwararren lauya, Danjuma John, ya ce idan mutum ya cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa a Nijeriya ƙarƙashin dokokin mulki na yanzu, dole ne ɗan takara ya cika wasu muhimman sharuɗɗa, ya kasance yana da aƙalla takardar shaidar makarantarsa.

Duk da haka, Lauya Taiye Oniyide bai yarda ba, yana jaddada cewa rashin ambaton ba ya haifar da wata illa ta doka ta tanada, sannan kuma bai kamata a cakuɗa shi da cancantar da kundin tsarin mulki ya tanada ba.

INEC ta bayyana cewa ƙarƙashin dokar zaɓe ta 2026, aikinta shi ne ta wallafa bayanan ƴan takara da takardunsu don jama’a su duba, yayin da duk wata ƙalubale kan gaskiya ko ingancin waɗannan takardun, kotu ce za ta iya warwarewa.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai na INEC, Wilfred Osilama Ifogah, ya bayyana haka a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan wallafa bayanan cancantar ƴan takara na zaɓen 2027.

Jam’iyyar ADC ta zargi Tinubu da ƙoƙarin ɓoye wani abu ta hanyar ƙin saka takardun shaidar makarantar firamare da sakandare a shafin INEC.

Sakatare yaɗa labarai na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya shaida cewa, “Ta hanyar barin waɗannan matakan ilimi, kamar yana ba da gaskiya ga jita-jitar cewa Tinubu yana da wani abu da yake ɓoyewa game da da’awarsa. A gare mu a matsayin jam’iyya, shugaban Nijeriya bai kamata ya kasance da irin wannan ɓoyayyiyar magana a kansa ba.

Haka kuma, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar NDC, Osa Director, ya bayyana cewa rashin saka takardun shaida na makarantar firamare da sakandare na Tinubu a cikin shafin INEC a matsayin abin mamaki.

Ya ce, “Abin mamaki ne saboda duk mun san cewa ba za ka iya samun takardar shaidar jami’a ba tare da takardun makarantar firamare da sakandare ba, waɗanda suke a matsayin sharaɗi.”

Duk da ƙoƙarin jin martani daga fadar shugaban ƙasa ya ci tura, domin ba a samu wayar mai bai wa shagaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, yayin da shi ma mai ba shagaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwar, Daniel Bwala, bai amsa kiran wayarsa ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, saƙonni da aka aika wasu ta WhatsApp mataimakan shugaban ƙasan guda biyu ba su amsa ba.

Tinubu
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Mutum 7 Na Fuskantar Shari’a Kan Safarar Jarirai A Jihar Gombe —NAPTIP

Mutum 7 Na Fuskantar Shari’a Kan Safarar Jarirai A Jihar Gombe —NAPTIP

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.