ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Dr. Jamil Isyaku Gwamna Ne Ya Fi Dacewa Da Mulkin Jihar Gombe  – Ibrahim Shawai

by Bello Hamza
3 months ago
Jamil

Ibrahim Sani Shawai shi ne mai magana da yawun Sardaunan Gombe, Dr Jamil isyaku Gwamna ɗaya daga cikin waɗanda ke neman takarar kujerar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar APC. A tattaunawarsa da Editanmu Bello Hamza, ya yi bayani a kan ƙwarewarsa da kuma irin tanadin ayyukan alhairi da ya shirya yi wa al’ummar jihar Gombe in ya kai ga ci. Ga dai yadda hirar ta kasance;.

Da farko, ko zaka ba mu bayani a taƙaice a kan wane ne Dr. Jamil Isyaku Gwamna

Dr jamilu Isyaku Gwamna, wanda aka fi sani da Sardaunan Gombe, an haife shi ne a ƙaramar Hukumar Gombe da ke Jihar Gombe. Ya yi firamare da sakandare dukka a Gombe. Daga nan ya tafi Jami’ar ABU Zaria, inda ya yi digirinsa na farko a fannin Tattalin Arziki, wato Accountancy, a shekara ta 1986. Daga nan ya tafi Jami’ar Metropolitan da ke birnin Landan inda ya kammala digirinsa na biyu a shekara ta 2004 a harkokin tattalin azriƙi da hada-hadar kuɗaɗe, wato “Economics and Finance”. Haka kuma ya ci gaba da digirinsa na uku a fannin tattalin Arziƙi a dai wannan Jami’ar da ke birnin Landan, inda ya kammala a shekara ta 2008.

ADVERTISEMENT

Dr. Jamil ya yi aiki a wurare daban-daban, kama daga gwamnati da kuma kamfanoni. Ya kuma yi tafiye-tafiye zuwa kasashe daban-daban a Duniya.

  • Gidauniyar Bukola Saraki Za Ta Fara Raba Abincin Buɗe Baki Daga Gobe
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata

A halin yanzu guguwar siyasar 2027 ta kaɗa, wa kake ganin ya dace ya jagoranci jihar Gombe a matsayin Gwamna a wannan lokacin?

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

Da farko dai, dole ne mu fara da yaba wa irin gagarumar nasarar da Jihar Gombe ta samu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya. Babu shakka, an samu sauyi a fannoni da dama; daga inganta ababen more rayuwa, zuwa bunƙasa tattalin arziki da kuma ƙoƙarin daidaita harkokin gwamnati cikin tsari mai kyau. Gwamna ya bunƙasa harkokin noma, ya samar da kayayyakin inganta karatu daga mataki na firamare har zuwa gaba da sakandare.

A irin wannan yanayi, abin da Gombe ke buƙata a yanzu shi ne shugaba wanda zai gina a kan wannan turba, ba wanda zai rushe ta ba. Mutumin da zai zo da sabon hangen nesa amma kuma yana mutunta nasarorin da aka riga aka samu.

A ganina, lokaci ya yi da za a zaɓi shugaba mai kishin jama’a, mai gaskiya da riƙon amana, wanda zai iya ɗaukar Gombe daga matakin da take kai yanzu zuwa wani sabon matsayi mafi girma.

 

Wani sabon salon mulki kake ganin Dr. Jamil Isiyaku Gwamna (Sardaunan Gombe) zai bijiro da shi a Jihar Gombe da ba a saba gani ba?

Idan muka kalli irin tubalin da Gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ta shimfiɗa, za mu ga cewa akwai kyakkyawan tushe da duk wani shugaba mai hangen nesa zai iya gini a kai.

Dr. Jamil Isiyaku Gwamna (Sardaunan Gombe) mutum ne mai fahimta da hangen nesa. Salon mulkinsa zai zo ne da sabbin dabaru da suka haɗa da: Inganta amfani da fasaha wajen tafiyar da gwamnati, Samar da ƙarin damammaki ga matasa Maza da Mata, Ƙara buɗe ƙofa domin zuba jari da bunƙasa kasuwanci da kuma ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da al’umma.

Abin da zai bambanta shi shi ne yadda zai haɗa sabbin tunani da kuma ci gaba da kyawawan manufofin da gwamnatin Inuwa Yahaya ta fara, domin a samu ci gaba mai ɗorewa.

 

Ganin mutane da dama sun nuna sha’awarsu na zama Gwamnan Gombe a wannan lokacin, ya kake ganin tagomashinsa?

Haƙiƙa, yawan masu neman kujera alama ce ta dimokuraɗiyya mai ƙarfi, kuma hakan ma wata nasara ce da za a danganta da kyakkyawan yanayin siyasa da gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ta samar.

Amma duk da haka, ba yawan masu nema ne ke ba da nasara ba, inganci da karɓuwa ne suka fi tasiri.

Game da Sardaunan Gombe, yana da wasu muhimman abubuwa da ke ƙara masa armashi: sun kuma haɗa da, Karɓuwa a tsakanin jama’a musamman matasa, Tarihi mai kyau da mutunci da kuma mutuntawa, Fahimtar tsarin gwamnati da kuma yadda za a gina kan nasarorin da aka samu da kuma salon siyasa mai tsafta da mutunta kowa da kuma ba kowa haƙƙinsa.

Wadannan su ne ginshiƙan da ke sa a duba shi a matsayin wanda ya tsere sa a.

 

A baya Dr. Jamilu Gwamna ya taka wani matsayi na ɗaukaka a rayuwarsa, waɗanne abubuwa ya yi wa al’ummar Jihar Gombe da zai zama hujja a gare su na zaɓensa?

Abubuwan alkhairin da ya yi wa al’ummar Jihar Gombe ba za su ƙididdigu ba, amma ga wasu daga ciki;

Samarwa matasan Gombe aiki a hukumar KEDCO da Kaduna Electric Sama da Mutum dubu ɗaya, Samarwa mutane daban-daban aiki a Gombe Water Board sama da Mutum dubu ɗaya, Lokacin yana shugabantar hukumar. Haka kuma ya bayar da gidaje da filaye kyauta domin ci gaban ilimi a Jihar Gombe, ya kuma raba motoci ga ƙungiyoyin addini domin sauƙaƙa musu zirga-zirgar ayyukansu, ya kuma gyara masallatai wato ‘renoɓation’ da kuma gina wasu masallatan sabbi.

Ya kuma raba wa mutane abun hawa, kama daga motoci da baburan hawa domin inganta rayuwarsu. Ya tallafa wajen aurar da ‘yaƴan marasa ƙarfi da yawa tare da yi musu kayan ɗaki. A fannin lafiya na san yaron da maciji ya sara a Kaltungo daga ƙarshe cancer ta shiga ƙafar aka yanke, Sardauna ya kai shi wani asibiti a Inugu aka yi masa ƙafa na musamman. Haka kuma akwai waɗanda aka yi wa tiyata da ya ɗauki nauyin su da yawa.

Haka kuma a ƙarƙashin Gidauniyar Agaji ta ‘Sardauna Foundation’ an raba wa mata keken ɗinki, da injin markaɗe, da firinjin ƙanƙara, da kuma bayar da jari domin dogora da kai. Ya biya wa yara ƴan Gombe su 39 kuɗin makaranta a Yamusa science Academy Birnin Kebbi, kuma dukkanin su sun kammala. Da dai ayyukan alhairi na bunƙasa rayuwar al’umma.

Abin da ya fi ban mamaki game da halayyarsa shi ne jajircewarsa wajen haɗakan al’umma da magance damuwarsu. Shi mai fafutukar ƙarfafa mata ne, mai ba da shawara ga matasa, kuma mai fafutukar kare haƙƙin naƙasassu. Ɗabi’arsa ta son zaman lafiya ta sa ya sami girmamawa daga ƴan jihar Gombe waɗanda ke godiya da halayyarsa ta yin shawara da haɗɗaka fahimtar juna, ba tare da nuna banbancin addini ko ƙabila ko kuma al’ada ba.

 

Idan Allah Ya sa Dr. Jamilu Gwamna ya zama Gwamnan Jihar Gombe, waɗanne fannoni kake ganin zai fi bai wa fifiko a mulkinsa?

Dr. Jamilu Gwamna zai fi ba da fifiko a fannin gina al’umma da kuma fannin ilimi. Yana da fahimtar cewa waɗannan su ne ginshiƙan da ake samar da al’umma mai nagarta. A wajensa, gina al’umma ta hanyar samar musu da ayyukan yi, da koya musu sana’o’i, da ba su jari don su zamo masu dogaro da kansu, shi ne kan gaba, kafin a yi batun samar da abubuwan more rayuwa.

Ta fuskar ilimi kuwa, a wajen sa, ilimi shi ne ginshikin cigaban kowacce al’umma. Ya yi imanin cewa kowane yaro da yarinya ƴan Jihar Gombe sun cancanci samun ingantaccen ilimi, ba tare da la’akari da asalinsu ko yanayin arziƙinsu ba. Yana da burin inganta horar da malamai, da inganta yanayin koyo da koyarwa, da kuma samar da tallafin karatu ga ɗaliban da ba su da galihu, tare da tabbatar da cewa matasanmu suna da ƙwarewa da ilimin da suke buƙata don samun nasara a rayuwarsu.

 

Ko akwai wani kira na musamman da zaka yi wa al’ummar Jihar Gombe?

Ina kira ga al’ummar Jihar Gombe da su ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen ci gaba irin waɗanda gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ta kawo. Hakazalika: Su zaɓi shugabanni bisa cancanta da nagarta. Su guji siyasar rarrabuwar kai da ƙiyayya. Su ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya. Su ba da dama ga matasa domin su taka rawa a ci gaban Jihar Gombe.

Idan muka haɗa kai, muka gina a kan nasarorin da aka riga aka samu, babu shakka Gombe za ta zama abin koyi a Nijeriya.

Gombe na kan tafarkin ci gaba. Abin da ya rage shi ne a tabbatar an samu shugabanci mai ɗorewa wanda zai ci gaba daga inda aka tsaya, ba tare da katse wannan kyakkyawan tafiya ba.

Mun

gode ƙwarai da gaske

Nima na gode

Jamil
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

MASU ALAKA

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz
Manyan Labarai

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

July 7, 2026
Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano
Labarai

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

July 7, 2026
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Manyan Labarai

ADC Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 17 Cikin Yunwa

July 7, 2026
Next Post
Buƙatar Taimaka Wa Al’umma Ba Sai Sun Yi Roƙo Ba

Buƙatar Taimaka Wa Al'umma Ba Sai Sun Yi Roƙo Ba

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

Iran Ta Harba Wa Jiragen Ruwa Makamai Masu Linzami A Mashigar Hormuz

July 7, 2026
Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

Hukuma Ta Tilasta Wa Alƙali Yin Ritaya Saboda Karɓar Cin Hanci A Kano

July 7, 2026
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

ADC Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 17 Cikin Yunwa

July 7, 2026
Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

Kasuwa Ce Ke Saita Tsarin Cinikayyar Sin Da EU In Ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin

July 6, 2026
Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

Dukkan Kabilun Kasar Sin Na Zaman Tsintsiya Madaurinki Daya

July 6, 2026
Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

Mutane 15 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jihar Kwara

July 6, 2026
Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

Gwamnatin Sin Ta Fara Aika Zagayen Farko Na Kayakin Agajin Gaggawa Ga Venezuela

July 6, 2026
FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

FIFA Ta Tsallake Iyakarta Dangane Da Batun Dakatarwar Balogun – UEFA

July 6, 2026
Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

Shugabannin Sin Da Montenegro Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Cika Shekaru 20 Da Kulla Alakar Diflomasiyya Tsakaninsu

July 7, 2026
Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

Rashin Tsaro: Kisa Ne Ya Fi Cancanta Ga ‘Yan Ta’adda Ba Gyaran Hali Ba – Ɗan Majalisa Gagdi

July 6, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.