Gwamnatin Jihar Bauchi ta umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓukan fidda gwani na jam’iyyunsu da su yi murabus daga mukamansu kafin ko zuwa a ranar Juma’a, 24 ga Afrilu, 2026.
Wannan umarni na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Laraba.Sanarwar ta bayyana cewa umarnin ya zo ne domin bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 (da aka yi wa kwaskwarima).
- Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
- Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
- Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
- Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
A cewar sanarwar, matakin ya yi daidai da ƙa’idojin doka da ke tsara yadda masu riƙe da muƙaman gwamnati za su shiga harkokin zaɓe, tare da tabbatar da cikakken bin doka.
Gwamnatin ta kuma nuna godiya ga waɗanda abin ya shafa bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban Jihar Bauchi, tare da yi musu fatan alheri a rayuwarsu na gaba.
A cewar sanarwar, an kuma umarci dukkan waɗanda za su ajiye aikin nasu da su miƙa dukkan ragama ofisoshinsu da ƙadarorin gwamnati da ke hannunsu, ga jami’in ya dace a cikin ma’aikatunsu, sassa da hukumominsu (MDAs).














