Gwamnatin Jihar Nasarawa ta gargaɗi masu amfani da harkokin siyasa wajen tayar da fitina, tana mai cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jihar ba.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Shuaibu Magaji Labaran, ya sanya wa hannu a ranar 10 ga watan Agusta, 2026.
Sanarwar ta ce gwamnati ta lura da wasu abubuwan da ke faruwa yayin harkokin siyasa, ciki har da cin zarafi, toshe hanyoyi, lalata tutoci da allunan tallan siyasa, tunzura jama’a da kai wa wasu ’yan ƙasa hari.
Ta ce irin waɗannan ayyuka na iya barazana ga tsaro da zaman lafiya da kuma kyakkyawar mu’amala tsakanin al’ummar jihar.
Gwamnatin ta jaddada cewa kowa na da damar goyon bayan ɗan takarar da yake so a zaɓen 2027, matuƙar yana yin hakan ta hanyar bin doka.
Sai dai ta gargaɗi masu ƙoƙarin tayar da rikici cewa za a ɗauki matakin shari’a a kansu.
Gwamna Abdullahi A. Sule ya kuma yi kira ga ’yan jihar da su guji tashin hankali tare da bin doka da oda.
Haka kuma, gwamnatin ta umarci hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da tabbatar da zaman lafiya a jihar.














