ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Na Yi Amfani Da Intanet Wajen Bunƙasa Sana’ata —Fatima Mubaraka

by Sulaiman
1 month ago
intanet

Fatima Mubaraka matashiya ce da ta jajirce wajen amfani da kafafen yaɗa labarai na zamani wajen bunƙasa sana’arta ta ɗinki. A hain yanzu tana hulɗa da mutane da dama daga sassan ƙasar nan dama wasu ƙasashen duniya. A hirarta da wakilinmu Muhammad Baƙir Bello, ta bayyana yadda ta fara sana’ar da yadda iyayen ta suka tsayu domin ganin ta yi nasara da kuma yadda ta samu nasarar horas da wasu matasan inda da dama daga cikinsu na cin gashin kasu a halin yanzu. Ga dai yadda hirar ta kasance:

 Za mu so mu san takaitaccen tarihinki?.

Assalamu alaikum, da farko sunana Fatima Mubaraka sunan mahaifina Muhammad Isa mahaifiyata kuma Zahra El Yakub, na yi makaranta na a Kano firamari da sakandari ɗina a Kano, sannan na yi Jami’an Kimiya da Fasaha na wudil, ina da ƴan uwa guda uku.

ADVERTISEMENT

Ta yaya kika tsinci kanki a wannan sana’ar?

Yadda na tsinci kaina a wannan sana’ar da nake yi na ɗinki shi ne, na kasance ina son ƙyale-ƙyale tun ina ƙarama, sannan kuma ina son kwatanta duk abin da na gani, saboda haka nake gani kamar wata baiwa ce na duk abin da na gani wanda ya shafi ɗinki sai na gwada, da haka na fara sannan sai na shiga inda zan ƙara koya don in samu ƙwarewa sosai, na fara ne tun shekarar 2020 har zuwa yau.

LABARAI MASU NASABA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

Kina amfani da kafafen sa da zumunta wajen kasunwancin ki ?

Eh ina amfani da kafafen sada zumunta kamar su Instagram da Tiktok da kuma Facebook da WhatsApp, na fara buɗe group kafin na zo na buɗe Page, a halin yanzu muna da masu bibiyan shafin mu mutane masu yawan gaske.

Zuwa yanzu kin yi shekara nawa kina wannan Sana’ar ?

Da fara wannan sana’ar zuwa Yanzu aalla na yi shekara 6 zuwa bakwai a wannan sana’ar na ɗinki, amma kafin nan tun ina arama nake ɗan yin sana’a a lokacin muna siya ne sai mu siyar amma yanzu mu muke ɗinka kayan da muke siyarwa.

Ta yaya kika iya haɗa karatu da sana’a?

Alhamdulillahi ta fuskacin haɗa karatu da sana’a bai kasance min da wahala ba saboda dama tun ina da ƙarancin shekaru na fara kasuwanci, iyaye na sunsa ido sosai wajen ganin na maida hankali a karatu, saboda haka bai bani wahala ba, ina samun lokutan da bana komai sai in tsara abubuwa na, a lokacin da nake jami’a, makarantan mu tana da nisa daga wajen mu, don haka nake ware ranaku kamar ƙarshen mako idan na samu ayyuka a wajen abokan karatuna sai na yi amfani da wannan lokacin in ɗinka masu saboda haka gaskiya bansha wahala ba wajen haɗa karatu da sana’a, kusan zan iya cewa lokacin da sana’a ta take bunƙasa nafi ƙoƙari a makaranta.

Aƙalla yanzu kin koya wa mutane nawa aiki ?

Eh toh akwai masu koyan sana’ar a waje na, wanda ada ban yi tunanin hakan ba, amma saboda yau da gobe mutane suna sha’awan aikin, shi yasa muka yi tunanin fara koyarwa, zuwa yanzu kusan na koyar da mutune aƙalla basu gaza goma sha biyar ba, wanda yanzu ko wanne a cikin su ya tsayu da kafan sa,

Wasu irin nasarori da ƙalubane kika  fuskanta?

Alhamdulillahi ta fuskacin nasarori sai dai mu yi godiya ga Allah da kuma iyayen mu mahaifina da mahaifiyata da gudunmawar da suka bani wajen ganin na tsayu da aafana, wanda su suka fara siyan min keken ɗin na sai  kuma gwaggona wato ƙanuwar mahaifiyata  saboda tsayuwarta da jajircewarta, wanda tun muna da shago ɗaya gashi yanzu har sun zama biyu, wannan yana daga cikin nasarorin da muka samu, kuma Alhamdulillahi duk wasu ƙananun buƙatu ba sai ka Jira an yi maka ba, babban nasara shi ne koyar da mutane da na yi.

Ta ɓangaren ƙalubale gaskiya ba zan iya cewa ga wani ƙalubalen da nake fuskanta ba Alhamdulillahi.

Wani irin buri kike dashi a wannan sana’a ?

Burina shi ne ya zama na samar da katafaren wuri wanda zai mana branch mai girma wanda za a dinga yin ‘production’ kuma ya samu karɓuwa a kowane ɓangare na ƙasannan, sannan kuma ya zama duk bayan wasu lokutan muna yaye waɗanda muka koya wa sana’a domin su tsaya da ƙafan su kuma suma su koyar, gaskiya wannan shi ne kusan babban burina, kuma ya zama mun buɗe reshe a wajaje daban-daban, sannan kuma ina son nan gaba in dinga ɗaukan nauyin masu ƙaramin ƙarfi da marayu ina taimaka masu wajen koya masu sana’a  kyauta gaskiya shi ne burina.

Kina da saƙo na musamman da kike son isar wa masu karatu ?

Sakona zuwa ga masu karatu musamman matasa, shi ne a wannan lokaci ba lokaci ne na ɓoye baiwar da Allah ya yi wa mutum ba,mutum ya yi amfani da baiwar da Allah ya yi masa ta hanya mai kyau wajen ganin ya taimaka wa kansa da al’umma baki ɗaya.

Mun gode

Nima na gode

intanet
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
Tattaunawa

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

August 28, 2026
Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattaunawa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

August 20, 2026
Nijeriya
Tattaunawa

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

August 8, 2026
Next Post
Ci Gaban Bangaren Ciniki A Kasar Sin Ya Nuna Yadda Kasar Ke Samar Da Damammaki Ga Kasashen Duniya

Ci Gaban Bangaren Ciniki A Kasar Sin Ya Nuna Yadda Kasar Ke Samar Da Damammaki Ga Kasashen Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.