ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027:Atiku Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Ya Janye Takararsa Ya Mara Wa Obi Da Kwankwaso Baya

by Yusuf Shuaibu
4 months ago
Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yana fuskantar matsin lamba mai tsanani kan ya dakatar da burinsa na takarar shugaban kasa a 2027, ya mara wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, baya domin samun tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC.

An ruwaito cewa bangaren Atiku, wanda Dele Momodu ke jagoranta na matsa kaimi kan samun tikitin tararar shugaban kasa tsakanin Atiku da Obi, sai dai wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyya suna goyon bayan Obi da Kwankwaso su samu takara a jam’iyyar ADC a zaben 2027.

ADVERTISEMENT

Ko da yake wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyya suna ganin ADC ba za ta iya yin nasara a zaben ba tare da Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa, wasu kuma suna da ra’ayin cewa Atiku ya fi kwarewa kuma zai samu kuri’u da yawa daga arewacin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne ke bayan kokarin samun tikitin Obida Kwankwaso, yayin da yake kuma goyon bayan hadin gwiwar ‘yan adawa wuri guda domin kayar da Shugaban kasa, Bola Tinubu.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Masu sharhi kan harkokin siyasa suna ganin cewa kiran sake dawo da tikitin Obi da Kwankwaso na nufin raunana ikon Atiku a kan ‘yan adawa da hana maimaita gasa ta rarrabuwar kawuna a 2023.

Kazalika, wasu masu ruwa da tsaki na ADC a arewa da kudu suna matsa lamba kan Atiku ya janye muradinsa na tsayawa takara domin da bai wa matasan wuri.

Yayin da wasu manyan ‘yan jam’iyyar suna tuntubar tsohon mataimakin shugaban kasa a asirce, wasu kuma sun bayyana ra’ayinsu a fili.

Kwanan nan, Sanatan Anambra ta tsakiya, Bictor Umeh a wata hira a talabijin na kasa, ya ce ya kamata Atiku ya ba wa wadanda suka fi shi kananan shekaru dama, yana bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa mutum ne da ake girmamawa a siyasar Nijeriya kuma yana fafutuka don zama shugaban kasa tun daga 2003.

Haka kuma, wani mashahurin mai bincike a kafofin watsa labarai, Jimi Disu ya ce Shugaba Tinubu zai ci zabe idan ADC ta tsayar da Atiku.

A cewarsa, za a dauki Atiku a matsayin gwarzo idan ya yarda ya janye wa matashi.

“Atiku zai zama jarumi idan ya janye kudirinsa na tsayawa takara, ba lallai sai shi ba. Idan Atiku zai fafata da Tinubu a 2027, zan iya hango sakamakon zaben”, in ji shi.

Matsayar Atiku

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, ya tsaya kan cewa babu wani mai neman shugabancin kasa a ADC da zai iya daidaita karfin zabensa, musamman a yankin arewa.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce yanzu haka Jihar Kano ta fita daga hannun Kwankwaso. Ya jaddada cewa jihar yanzu ta rabu gida biyu tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba Yusuf.

Duk da haka, Atiku ya yi alkawari a bainar jama’a cewa zai goyi bayan kowane dan takara na hadin gwiwa da ya fito ta hanyar dimokuradiyya.

Sai dai kuma magoya bayan Obi da Kwankwaso karkashin jagorancin sabon kungiyarsu ta Obi–Kwankwaso (OK), sun hade karfi karfe don tabbatar da cewa babu wani dan takara da zai samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyya ADC sai Obi da Kwankwaso.

Mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Habibu Mohammad, a cikin wata tattaunawa ta musamman, ya bayyana fatan cewa Obi da Kwankwaso za su fito a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ADC.

Rahotanni sun nuna cewa fafatawar neman tikitin takarar shugaban kasa a ADC ta haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin masu goyon bayan Atiku da wadanda ke neman takarar Obi da Kwankwaso.

Yayin da magoya bayan takarar haddn gwiwa na Obi da Kwankwaso suke gefe daya, masu goyon bayan Atiku Abubakar suna gefe na daban.

Daya daga cikin manyan masu goyon bayan Atiku, AbdulAziz Na’ibi Abubakar, ya yi barazana a wani sabon rubutu a D cewa za a yi zanga-zanga a kasar baki daya idan Atiku ya janye wa wani dan takara.

“Idan Atiku ya yanke shawarar janye takararsa don wani dan takara a 2027, tabbas za a sami zanga-zanga a kasar nan baki daya. “‘Yan Nijeriya ba za su yarda su rasa wata daman samun kyakkyawan shugabanci da gaskiyar dimokuradiyya ba,” in ji shi.

Sakon ya jawo suka mai tsanani, musamman daga masu goyon bayan Obi da Kwankwaso, wadanda suka ki ra’ayin AbdulAziz kuma suka nace cewa ADC za ta iya cin nasara ne kawai idan Obi yana cikin takardar jefa kuri’a na shugaban kasa.

A cikin goyon bayan matsayar AbdulAziz, wata majiya daga arewa a cikin wani rubutu a D ta bayyana cewa ‘Masu goyon bayan Peter Obi su ne abokan gaba mafi girma nashi.’

“’Yan arewa ba za su zabi Peter Obi ba. Cin mutunci Atiku Abubakar iri daya ne da cin mutunci ga duk arewacin Nijeriya”.

Atiku
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Jam’iyyun Adawa Sun Hada Kai Don Tsayar Da Dan Takara Guda A Zaben 2027

Jam'iyyun Adawa Sun Hada Kai Don Tsayar Da Dan Takara Guda A Zaben 2027

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.