ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jam’iyyun Adawa Sun Hada Kai Don Tsayar Da Dan Takara Guda A Zaben 2027

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
Adawa

Jam’iyyun adawa a fadin Nijeriya sun ajiye bambance-bambancensu, sun nuna niyyarsu ta gabatar da dan takarar shugaban kasa daya a zaben 2027, wajen kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC.

Sun yi gargadin cewa abin da ake ganin rinjayar jam’iyyar APC, na iya zama barazana ga zabe mai zuwa. Sun dauki wannan matakin ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron kolin da ya gudana a garin Ibadan.

A taron, wanda manyan ‘yan adawa suka halarta ciki har da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Rotimi Amaechi, Peter Obi da Rauf Aregbesola, sun hadu don tsara wata dabarar hadin gwiwa.

ADVERTISEMENT

Bayan karanta sanarwar, shugaban zagin jam’iyyar PDP, Taminu Turaki, ya ce, “Za mu yi adawa da duk wani shiri na APC don tilasta wa Nijeriya tsarin jam’iyyar guda daya kuma mu yi yaki don tsiratar da jam’iyyu da dama a kasarmu. Duk da hare-hare da dabarun jam’iyyar gwamnati, za mu tura ‘yan takara mu yi gogayya a zaben shugaban kasa da sauran zabuka a 2027.

“Za mu yi aiki tare don fitar da dan takarar shugabacc kasa a zaben shekara ta 2027, wanda dukkan jam’iyyun adawa masu halartar wannan taro sun goyi baya don ceto kasarmu da talakawanta da suka dadde suna wahala.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Joash Ojo Amupitan, wanda ya nuna son rai da nuna bangaranci wajen taimakon APC mai mulki, bai kamata ya jagoranci zaben 2027 ba. Ci gaba da kasancewarsa a ofis yana haifar da damuwa kuma yana iya jawo rikice-rikice a fadin kasar nan. Majalisar dokoki ta kasa ya kamata ta sake duba dokar zabe ta 2026 nan take, don cire duk sashe-sashen da ke barazana ga sahihincin zabuka.

“Muna daukar sabbin ka’idodin da INEC ta fitar a matsayin shinge, wanda aka tsara su da niyya sanya sharudda da wa’adin lokaci ga jam’iyyun adawa. INEC ya kamata ta kara wa’adin gudanar da zabukan fitar da gwani har zuwa karshen watan Yulin 2026.”

A farkon jawabinsa, gwamna mai masaukin baki, Seyi Makinde, ya yi gargadin cewa dimokuradiyyar Nijeriya na fuskantar rushewa a hankalin yanzu, saboda raunana jam’iyyun adawa.

Ya ce, “A fadin Nijeriya a yau, muna shaida wani irin matakin na siyasa wanda ya kamata ya dame mu duka. Suna nuna wani tsari wanda ya saba wa gasar siyasar kasar nan.”

Makinde ya gargadin cewa dimokiradiyya ba a hallaka ta cikin dare daya ba, amma ana raunana ta a hankali-hankali. Ya jaddada cewa lokacin da adawa ta zama mara tasiri, dimokiradiyya kanta tana fara rasa ma’ana.

Ya jaddada cewa dole ne a fayyace dimokuradiyya ta hanyar kasancewar zabuka na gaskiya, kuma ya yi gargadin cewa ba tare da wannan ba, “abin da muke da shi na iya ci gaba da kiran sa dimokuradiyya, ba zai ci gaba da aiki a matsayi daya ba.”

Gwamnan ya kuma fayyace manufar taron, yana mai cewa, “Ba wani yunkurin haduwa ne don kai hari ga mutum guda ba. Kuma ba game da buri na mutum daya na zama shugaban kasa ba. Abin da yake magana a kai shi ne, buri na hadin gwiwar ‘yan Nijeriya don samun dimokuradiyya mai kyau wanda aka ayyana daidai.

Ya karfafa masu ruwa da tsaki su yi tunani mai kyau, su yi magana da gaskiya, kuma su yi aiki da hadin kai da ya zarce iyakokin jam’iyya.

Da yake magana a taron, shugaban jam’iyyar ADC, Dabid Mark, ya bayyana taron a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Nijeriya, inda ya kira shi da suna, “wani gaggawar amsa kiran kasarmu na yi aiki tare.”

Ya ce: “Addu’ata ita ce tarihi ya maimaita kansa a gare mu, cewa lokacin da kasa ta yi ihu don a ceci ta, mun amsa. Lokacin da yara suka kwanta barci da yunwa, mun amsa, lokacin da ‘yan kasa masu aiki tukuru suka koma bara, mun amsa.

“A fadin kasarmu, rashin tsaro ya zama wani bangare na rayuwar yau da kullum. Nijeriya na fuskantar wani babban kalubale na tarihi. A shekarar 2025 kadai, Nijeriya ta samu fiye da mutuwar mutane 12,000 sakamakon rikice-rikice. Yanzu haka Nijeriya ta kasance ta hudu a cikin jerin kasashe masu fuskantar ta’addanci na duniya. Akalla ‘yan Nijeriya 15 ake kashewa kullum, yayin da kusan mutane 19 ake sacewa.

“Muna cikin wata kasa da kullum tana cikin bakin ciki, amma gwamnatin APC ta yi kamar komai lafiya lau. Ta mayar da hankali ga harkokin zabe da siyasa gaba daya.

“Wannan zabe zai kasance ne a tsakanin jam’iyyar mulki ta APC, da mutanen Nijeriya. Muna tare da mutanen kasar nan. ‘Yan Nijeriya sun rasa amincewa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. Bari wannan taron ya shiga tarihi a matsayin lokaci da kome ya canza. Mun zabi hadin kai a kan rarrabuwar kai, sadaukarwa ga kasa sama da komai.”

Adawa
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

MASU ALAKA

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
Tambarin Dimokuradiyya

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

July 11, 2026
Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
Tambarin Dimokuradiyya

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 11, 2026
makarfi
Tambarin Dimokuradiyya

Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi

June 26, 2026
Next Post
Sabon Tsarin Tattaunawa Don Kawo Karshen Rikicin Fulani Makiyaya Da Manoma

Sabon Tsarin Tattaunawa Don Kawo Karshen Rikicin Fulani Makiyaya Da Manoma

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.