Kamar gwamnatocin baya, Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta rungumi al’adar nan ta auren gata, wadda aka fi sani da Auren Zawarawa.
A makon da ya gabata ne, gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 300, domin gudanar da bikin auren na gata ga ma’aurata 1,500 a faɗin jihar.
A yayin wani shirin wayar da kan ma’aurata kafin auren, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ta Kano ranar Alhamis, Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar, Malam Aminu Daurawa, ya bayyana yadda bikin zai gudana da kuma irin tallafin da koɗanne ma’aurata za su samu.
Shugaban ya bayyana cewa, kowace amarya za ta samu kimanin Naira 200,000, a matsayin sadaki daga cikin kuɗaɗen da gwamnatin jihar ta ware, sannan kuma za a saka kuɗin ne kai tsaye a cikin asusun bankinta, domin tabbatar da ganin cewa; kuɗin ya riske ta.
Har ila yau, gwamnatin jihar za ta samar wa da kafatanin ma’auratan kayan ɗaki, tufafi da kayan abinci, baya ga kuɗi a matsayin wani ɓangare na tallafi na musamman.
Hakan ne ya sa tsawon kwanaki, titunan birnin ya cika da hayaniyar shagulgula, inda amare da danginsu ke shirya kayayyakin aure tare da halartar wasu tarurruka da shirye-shirye da aka tanadar musu.
Bugu da ƙari, an yi ta ganin amare sanye da jajayen hijabai, yayin da kuma angwaye ke sanye da fararen riguna da jajayen huluna a ranar Juma’ar da ta gabata. An dai ɗaura wannan aure ne a fadar Sarkin Kano.
A ranar Asabar ne aka kammala shagulgulan auren, inda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shirya wata liyafa ga sabbin ma’auratan tare da yi musu fatan alheri da addu’ar samun zaman lafiya da albarka a rayuwarsu ta auren.
Kazalika, an tsara wannan shiri ne, domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda ba za su iya ɗaukar nauyin kuɗaɗen aure ba, sakamakon matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a wannan lokaci.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Gwamnatin Jihar Kano, ta kashe kimanin naira biliyan 1.5, wajen gudanar da wannan shiri na auren gata.
Shirin ya haɗa da biyan sadakin amare da samar da kayan ɗaki da kuma sauran kayayyakin gara ga amaren.
An dai fara gudanar da wannan aure na gata ne a shekarar 2012, lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Kwankwaso, inda aka fara da ma’aurata 100, waɗanda mafi yawancinsu zawarawa ne.
Tun bayan wannan lokaci, gwamnatoci daban-daban da suka biyo baya, sun ci gaba da gudanar da wannan shiri, yayin da adadin masu amfana ke ci gaba da ƙaruwa a kowace shekara, sakamakon ƙaruwar buƙata.
Ko shakka babu, wannan shiri na auren gata, na da matuƙar farin jini, wanda har ta kai ga cewa; ma’aurata 5,000 ne suka nemi shiga cikinsa a wannan shekara.
Haka zalika kuma, shirin ya haɗa har da waɗanda suke da buƙatar ƙara aure, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada tare da amincewa da shi.
A koda-yaushe, Hukumar Hisbah ce ke shirya gudanar da shirin a madadin gwamnatin jihar, kuma ɗaya daga cikin muhimman ayyukanta shi ne, tantance ma’auratan da ke son yin aure.
Haka zalika, Jihar Kano na da rinjayen al’ummar Musulmi, sannan kuma ana aiwatar da dokokin Shari’ar Musulunci a jihar tare da tsarin dokokin farar hula na ƙasa.
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Mujahid Aminudeen, ya bayyana cewa, ko kaɗan wannan aikin ba mai sauƙi ba ne, aiki ne mai matuƙar wahalar gaske.
“A duk lokacin da muka gano akwai wani abu na ruɗani ko shakku game da wasu ma’aurata, mukan cire su daga cikin shirin.”
Ya ƙara da cewa, wasu ma’auratan kan yi bakin ƙoƙarinsu, wajen gamsar da jami’ai cewa; suna son junansu da gaske, alhali abin da ya fi ɗaukar hankalinsu shi ne, tallafi da alfanun da ake samu daga shirin.
Har ila yau, gwamnatin jihar ta kashe kusan kimanin naira miliyan ɗaya, kan kowane ma’aurata da suka amfana da shirin.
A cewar Hukumar Hisbah, ƙunshin tallafin da kowanne ma’aurata ke samu ya haɗa da muhimman kayan da ake buƙata wajen fara sabuwar rayuwar aure, kamar gado da katifa da zanin gado da matasai da kayan ɗaki da kuma kayan abinci.
Kazalika, kowace amarya na samun sadaki na naira 100,000, yayin da ake bai wa ma’auratan ƙarin naira 100,000, a matsayin jarin fara sana’a, domin ƙarfafa dogara da kansu bayan aure.
Haka kuma, duk masu neman shiga shirin, dole ne su yi cikakken gwajin lafiya, wanda ya haɗa da gwajin cutar HIƁ, ciwon hanta (hepatitis) da juna-biyu da kuma gwajin dacewar jinsin halitta (genotype), kafin a ba su damar shiga shirin.
Aminudeen ya bayyana cewa, an cire wasu ma’aurata daga cikin shirin bayan an gano cewa, sun aikata rashin gaskiya wajen sauya sakamakon gwajin lafiyarsu.
Sannan kuma, an gano wata budurwa da ke shirin yin wannan aure ta gabatar da Ɗan’uwanta a matsayin sabon angonta, domin ta samu damar cin gajiyar tallafin da shirin ke bayarwa.
Wani ɗan jarida a Kano, Yusuf Ali Abdallah, wanda ya shafe shekaru yana bibiyar auren gatan, ya ce; halin matsin tattalin arziƙi da Nijeriya ke ciki ne ya sa mutane da dama suka ƙara ƙoƙarin shiga shirin a wannan shekara.
“Kamar yadda kowa ya sani, aure na buƙatar kuɗaɗe masu yawa, sannan kuma tattalin arziƙin ƙasar ba ya cikin yanayi mai kyau a halin yanzu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, wannan ne ya sa wasu mutane ke matuƙar ƙoƙarin ganin sun samu shiga cikin jerin sunayen masu amfana da shirin.
Kazalika, ya ƙara da ce; akwai ma wasu ma’auratan da tuni sun riga sun yi aure, amma suka yi ƙoƙarin gabatar da kansu a matsayin masu shirin yin auren, domin samun tallafin shirin. Sai dai an gano su, aka cire su daga cikin shirin.
Haka kuma, wasu ƴan damfara sun yi ƙoƙarin cin moriyar waɗanda ke ɗokin shiga jerin sunayen masu amfana da shirin, wanda aka fitar makwanni biyu da suka gabata.
Wani mazaunin Kano da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, an nemi ya bayar da cin hanci, domin a sanya sunansa cikin jerin masu amfanar.
“Daga baya na gano cewa, waɗanda suka nemi waɗannan kuɗaɗe a wurina, ba ma’aikatan Hisbah ba ne, shi ya sa na yi wa masu shirya shirin adalci,” in ji shi.
Duk da haka dai, shi da budurwarsa ba su samu shiga cikin ma’auratan da aka zaɓa ɗin ba, domin wannan aure na bana (2026), amma ya ce; zai sake gwada sa’arsa a shekara mai zuwa.
Aminudeen ya amince cewa, Hisbah na da masaniya kan irin waɗannan zarge-zargen da suke tasowa.
“Mun gano cewa, akwai wasu mutane da ke neman wasu su biya wasu kuɗaɗe, domin a sanya sunayensu cikin jerin masu amfana da shirin.”
Sai dai, jami’in na Hisbah ya yi ƙoƙarin tabbatar wa waɗanda ke fatan yin aure a cikin shekaru masu zuwa da cewa; dukkan tsarin shiga shirin, ba ya buƙatar ko sisin kwabo.
“Muna son mutane su sani cewa, wannan tsari gaba-ɗayansa kyauta ne, kuma babu wani kuɗi da ya kamata a biya, domin samun damar shiga ciki,” kamar yadda ya bayyana.
“Muna son sanar da al’ummar Kano cewa, dukkan tsarin shirin kyauta ne. Tun daga zaɓen masu amfana, zuwa gwaje-gwajen lafiya, har zuwa kayan da aka tanadar wa ma’auratan, gwamnati ce ke ɗaukar nauyin yin komai.”
Ɗaya daga cikin angwayen da suka amfana da shirin, Rabiu Yusuf, ɗan kasuwa mai shekaru 43 ya ce; tsarin neman shiga shirin ya gudana cikin sauƙi a gare shi.
“Babu wanda ya nemi wani abu na kuɗi ko makamancin haka daga gare ni. An gaya min cewa, gwamnati ce za ta ɗauki nauyin komai.”
Aisha Auwal, ita ce sabuwar matar tasa, kuma sun haɗu ne sakamakon yadda take yawan zuwa shagonsa, domin sayen kaya.
Yusuf, wanda tuni yake da yara biyar tare da matarsa ta farko, ya ce; yana cikin matuƙar farin ciki, kuma yana cikin ɗokin fara sabuwar rayuwa tare da amaryarsa.
Amina Alhassan mai shekaru 24, ita ma ta bayyana irin wannan farin ciki, tana mai cewa; ba ta fuskanci wata matsala ba lokacin da ta nemi shiga shirin, domin a aurar da ita ga Nura Abdullahi mai shekara 40.
Tun da farko dai, iyalansu ne suka haɗa wannan aure nasu a ƙauyen Ɗambatta, kafin daga bisani su gabatar da kansu ga Hukumar Hisbah, domin shiga cikin shirin.
“Komai kyauta ne, kuma ina so na yaba wa gwamnatin Kano, kan wannan shiri da ta aiwatar, domin da ba don shi ba, da mutane da yawa ba za su iya yin aure ba, saboda tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.”














