ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarayyyar Turai Ta Yi Watsi Da Aikin Sa Ido A Zaɓen Nijeriya Na 2027

by Yusuf Shuaibu
3 weeks ago
Nijeriya

Tarayyar Turai (EU) ta yi watsi da cikakken aikin lura da zaɓen Nijeriya na 2027, tana mai cewa matsalar tsaro tana ƙara taɓarɓarewa kuma abin da suka kira rashin kyakkyawar mu’amala ga masu lura da zaɓe da jami’ansu bayan zaɓukan 2023.

Wannan mataki ta kawo ƙarshen jerin ayyukan lura da zaɓen da EU ta yi a Nijeriya na kusan shekaru fiye da ashirin.

EU ta bayyana matakin ne a matsayin amsa ga wata wasiƙa daga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), wadda ta gayyaci ƙungiyar don ta sa ido kan zaɓukan 2027.

ADVERTISEMENT

A cikin martini kan wasiƙar, EU ta kawo dalilai biyu na yanke hukuncinta, na farko shi ne, taɓarɓarewar tsaro a duk faɗin ƙasar da kuma rashin kyakkyawar mu’amala da masu lura da jami’anta bayan fitar da rahoton ƙarshe game da zaɓen 2023.

Maimakon tura manyan jami’ai a lokacin zaɓen, EU ta ce za ta ajiye ƙananan jami’ai kaɗan a Abuja don sa ido kan abubuwan da ke faruwa kuma su ba da rahoto zuwa Brussels.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

INEC ta rubuta wa EU tana neman masu aikin sa ido a 2027. Hukumar ta saba aika irin wannan gayyata kafin kowane zaɓen tun bayan dawowar mulkin farar hula a 1999.

EU ta sa ido kan zaɓen Nijeriya a shekarun 2003, 2007, 2011, 2015, 2019 da 2023. Babban mai sa ido, ɗan majalisar Turai na Ireland Barry Andrews, ya bayyana cewa sau 7 yana sa ido a zaɓen Nijeriya tun daga 1999.

A zaɓen 2023, wata tawagar ƙwararru 11 ta isa Abuja a ranar 11 ga Janairu, makonni shida kafin zaɓen shugaban ƙasa. Bayan haka, an tura masu sa ido a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Wani tawagar majalisar Turai ma ta shiga aikin sa ido don zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar ƙasa. Tawagar ta tsaya a ƙasar har zuwa 11 ga Afrilu, makonni bayan zaɓukan shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu da na gwamnonin jihohi na ranar 18 ga Maris. Tawagar ta gabatar da rahoton na ƙarshe a Abuja a watan Yuni, 2023.

Rahoton ya ƙunshi shawarwari 25 a faɗin manyan yankuna guda shida. Ya gano abin da ya bayyana a matsayin rauni masu ɗorewa a tsarin zaɓe. Ya ce gazawar a dokar zaɓe da gudanarwa sun hana gudanar da zaɓuka masu kyau da kuma sun lalata amincewar jama’a da INEC.

Sakamakon binciken ya haifar da zanga-zanga a ofishin jakadancin EU a Abuja, inda masu shirya zanga-zangar suka zargi ƙungiyar da tsoma baki a harkokin cikin gudanwa a Nijeriya kuma suna neman a janye rahoton.

Wasu ƴan adawa da ƙungiyoyin farar hula sunn cewa magoya bayan jam’iyyar APC ne suka ɗauki nauyin zanga-zangar. An musanta wannan zargi.

Matakin EU ta zo ne a yayin da ake fuskantar tashin hankali a wasu sassan arewa maso yamma da arewa maso gabas da arewa ta tsakiya da kudu maso gabas, inda hana fita da hare-hare kan wuraren zaɓe suka kawo cikas ga zaɓen 2023 a wasu jihohi.

Harkokin sanya idanu kan zaɓe na buƙatar masu sa ido su tafi wuraren kaɗa ƙuri’a a ƙauyuka da wurare masu nisa, sau da yawa ba tare da isasshen tallafin tsaro ba, wanda ke sanya aikin tura su ya zama mai wahala sosai.

Ana kuma sa ran wannan mataki zai tasiri ga kulawar duniya kan zaɓen 2027, la’akari da girma ayyukan EU da suka gabatar.

Nijeriya
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Nijeriya

Har Yanzu Manyan Mutane Na Samun Rakiyar Ƴansanda Duk Da Haramcin Shugaban Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.