ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Fara Binciken Mutuwar Malamar Da Ƴan Uwan Ɗalibi Suka Kashe A Kogi

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Rundunar ‘yansandan Jihar Kogi ta fara bincike kan mutuwar wata malamar makarantar firamare da ake zargin an yi wa duka saboda ta ladabtar da wani ɗalibi a ƙaramar hukumar Olamaboro ta jihar.

Rundunar ta bayyana cewa an shigar da ƙarar a shalƙwatar ‘yansanda ta Olamaboro ranar 25 ga Yuni, 2026, kuma ana bincikenta a matsayin laifin kisan kai.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Oyiza Salisu Afusat, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi.

ADVERTISEMENT

Binciken farko ya nuna cewa a ranar 18 ga Yuni, wani mutum mai suna Abdullahi Ishaka tare da wasu mata biyu sun je makarantar Brains Minds Nursery and Primary School da ke Ugbamaka, inda ake zargin sun kai wa wata malama mai suna Maryam Usman hari saboda ta ladabtar da wani ɗalibi.

Maryam Usman mai shekara 30 ta samu munanan raunuka sakamakon harin. An fara ba ta magani a wani asibiti da ke Ugbamaka kafin daga bisani a tura ta zuwa asibitin Iko-Ojo da ke Okpo domin ci gaba da jinya.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

Sai dai malamar ta rasu a ranar 25 ga Yuni sakamakon raunukan da ta samu. Afusat ta ce jami’an ‘yansanda sun kai ziyara wurin da lamarin ya faru da kuma gidan marigayiyar bayan an kai rahoton, inda suka gudanar da binciken farko tare da tattara bayanai.

Ta ƙara da cewa ana shirye-shiryen kai gawar marigayiyar zuwa Babban Asibitin Ankpa domin a yi binciken gawar da tantance musabbabin mutuwarta.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargi sun tsere kafin isowar jami’an ‘yansanda, amma ana ci gaba da ƙoƙarin kamo su. Ta bayyana cewa da zarar an kama su, za a miƙa shari’ar ga sashin Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da cikakken bincike.

Rundunar ‘yansandan Jihar Kogi ta jaddada aniyarta ta tabbatar da cewa an hukunta duk waɗanda ke da hannu a wannan lamari bisa doka.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

MASU ALAKA

Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Next Post
Atiku Ya Yi Zargin Ana Shirin Hana ADC Shiga Zaɓen 2027

Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.