ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Ya Yi Zargin Ana Shirin Hana ADC Shiga Zaɓen 2027

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wani shiri na hana jam’iyyar ADC shiga zaɓen 2027. Ya ce ya samu sahihan bayanai da ke nuna cewa ana ƙoƙarin amfani da hanyoyin siyasa da na shari’a domin cire jam’iyyar daga takarar zaɓe.

Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar. Wannan na zuwa ne bayan tsohon Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Timi Frank, shi ma ya yi irin wannan zargi kan wata maƙarƙashiya da ya ce ta shafi Fadar Shugaban Ƙasa, da INEC da wasu ɓangarori na shari’a.

Atiku ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tashi tsaye wajen kare dimokuraɗiyya, yana mai cewa babu wata gwamnati da ke da ikon hana jama’a zaɓar jam’iyyar da suke so. Ya ƙara da cewa idan APC tana da tabbacin farin jininta, bai kamata ta ji tsoron ADC ba.

ADVERTISEMENT

Ya kuma yi kira ga alƙalai, da INEC, da hukumomin tsaro da ƙungiyoyin fararen hula su kasance cikin shiri domin kare sahihancin zaɓe. A cewarsa, amfani da cibiyoyin gwamnati ko kotuna wajen murƙushe adawa barazana ce ga dimokuraɗiyya.

Atiku ya jaddada cewa babu wata barazana ko matsin lamba da za su hana miliyoyin ‘yan Nijeriya ci gaba da goyon bayan ADC, yana mai cewa burin sauyi ba za a iya dakatar da shi ba kuma ƙudurin al’umma zai yi nasara.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

MASU ALAKA

Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Tura Motocin CNG 40 Da Adaidaita Sahu 200 Kano

Gwamnatin Tarayya Ta Tura Motocin CNG 40 Da Adaidaita Sahu 200 Kano

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.