A yau Juma’a 31 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru cewa, tun fara gudanar da shekarar Sin ta kungiyar APEC, an riga an gudanar da tarukan manyan jami’ai uku, da tarukan ministoci biyar, da sauran taruka da bukukuwa fiye da 180 masu nasaba da fannoni daban daban bisa taken “Raya Asiya da tekun Pasifik bisa tsarin bai daya, da sa kaimi ga samun wadata tare”, kuma tun daga farko an kai ga cimma nasarori da dama.
Mao, ta ce a nan gaba kuma, za a gudanar da tarukan manyan jami’ai 2, da tarukan ministoci masu lura da inganci abinci, da kamfanoni kanana da matsakaita, da makamashi, da sufuri, da albarkatun kwadago, da kudade da sauransu. A matsayin mai karbar bakuncin taron kungiyar APEC na shekarar nan ta 2026, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da bangarori daban daban, don mayar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, wanda za a gudanar a watan Nuwanba, ta yadda zai zama muhimmin taro da zai sa kaimi ga hadin gwiwar dake tsakanin mambobin kungiyar APEC, da samar da babbar gudunmawar raya Asiya da tekun Pasifik bisa tsarin bai daya.
A kwanakin baya, An karrama matasa masana ilimin lissafi na kasar Sin da lambobin yabo na Fields Medal, kana an sanya hoton ‘yan kasuwa matasa a fannin mutum-mutumin inji na kasar Sin a shafin farko na mujallar Times. Game da hakan, Mao Ning ta bayyana cewa, ana jin dadin ganin yadda karin matasan kasar Sin suke fitowa dandalolin duniya, ba ma kawai domin su yi kokari da kansu ba, har ma an shaida cewa matasan kasar Sin na sabon zamani suna son neman ci gaba. Ana fatan matasan kasa da kasa za su yi hadin gwiwa da juna, don taimakawa bunkasar dukkan duniya, da kuma samar da kyakkyawar makomar bil Adama baki daya. (Zainab Zhang)














