ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kama Uwa Da Abokiyar Burminta Kan Kisan Jariri A Jihar Yobe

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
yobe

Rundunar Ƴansanda ta Jihar Yobe ta kama wata mace tare da wani da ake zargi da hannu wajen kisan gillat jaririyarta da aka haifa a Damaturu, inda rundunar ta bayyana lamarin a matsayin “mummuna da rashin imani.”

A cewar wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar, Dungus Abdulkarim ya fitar, an zargi matan ne da shaƙe jaririyar, sannan daga bisani suka ɓoye gawarta a cikin akwati tare da jefar da ita a bayan wani masallaci da ke rukunin gidaje na Anguwar Boka ta Damaturu.

Rundunar ta bayyana cewa jami’an sashen yaƙi da manyan laifuka (Ɓiolent Crime Response Unit) sun ɗauki mataki ne bayan samun kiran gaggawa ranar Talata game da zargin kisan jaririn da kuma ɓoye gawar tasa.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce: “Binciken farko ya nuna cewa wata mace da ake zargi, wadda ta haihu kwanan nan, ana zargin ta da hannu a wani lamari inda aka shaƙe jaririyar sannan aka ɓoye gawar a cikin akwati kafin a jefar da ita a bayan wani masallaci a yankin Anguwar Boka da ke Damaturu.”

Rundunar ta ƙara da cewa ɗaukar matakin gaggawa da ƴansanda suka yi ya kai ga kama mutum biyu waɗanda a halin yanzu ake gudanar da bincike a kansu.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Bayan ɗaukar matakin gaggawa na ƴansanda, an kama mutum biyu da ake zargi kuma a halin yanzu suna taimaka wa binciken. Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin yayin da Rundunar ke ci gaba da tattara hujjoji domin ganin an yi adalci,” in ji Abdulkarim.

Allah wadai daga kwamishinan ƴansanda

Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya yi tir da wannan ɗanyen aiki, inda ya jaddada cewa kowane yaro yana da haƙƙin rayuwa, kariya, da mutunci ƙarƙashin doka.

“Rundunar ba za ta lamunci kowace irin tursasawa ko tashin hankali ga yara ko kowane mara kariya ba, kuma duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi daidai da tsarin doka,” in ji Jibrin.

Rundunar ta sake jaddada cewa kowane yaro da aka haifa yana da wasu hakkoki na asali kuma ya cancanci kulawa, kariya, da mutunci, inda ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifin take waɗannan haƙƙoƙi zai fuskanci cikakken fushin doka.

Yunƙurin Sayar Da Jariri A Jihar Anambra

Wannan lamari yana zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan da jami’an Rundunar Ƴansanda ta Jihar Anambra suka daƙile yunƙurin wata budurwa ‘yar shekara 21 na sayar da jaririyarta a Igbariam, cikin Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 22 ga watan Yuni, Rundunar Ƴansandan Anambra ta bayyana cewa jami’anta da ke ofishin Oyi sun yi aiki ne bisa sahihan bayanan sirri da suka samu ranar 19 ga watan Yuni, inda suka yi nasarar hana gudanar da wannan ciniki na miyagun mutane.

Sanarwar ta ce: “Jami’an ƴansanda sun gaggauta tsare uwar da jaririyarta tare da haɗa su da sauran mambobin iyalansu domin tabbatar da samun ingantacciyar kulawa, kariya, da goyon baya.”

Waɗannan abubuwa guda biyu da suka faru sun sake farfaɗo da fargaba game da laifukan da suka shafi jinjirai da ƙananan yara marasa kariya, yayin da hukumomin tsaro ke sake jaddada aniyarsu ta kare haƙƙin yara da tabbatar da cewa an hukunta masu laifi.

yobe
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
yobe

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.