Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwa masu sayar da kayan marmari da ganye na Kasuwar Utako Babban Birnin Tarayya Abuja Hamza Mu’azu Karzai ya yi kira da waɗanda ke da ruwa da tsaki kan lamarin kuɓutar da ɗaliban 42 ƴan makaranta Firamare ta Mussa da kuma ƙaramar makarantar Sakandare ta Uba Askira na Jihar Borno,wanda kamar yadda ya ce a halin da ake ciki ɗaliban sun zarce wata uku a hannun ƴan ta’adda. Ya ce su ɗaliban ƙaramar hukumar Orire ta Jihar Oyo kwana 56 suka yi a hannun ƴan ta’addar aka samu ceo su, amma a cewar shi shiru kake ji sai kace an aiki Bawa garinsu ko kuma an shuka Dussa.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake hira da manema labarai a ofishinsa inda ya ƙara da cewa‘ lamarin yana da matuƙar ɗaure kai saboda kuwa duk da ye su ɗaliban sun zarce kwana 30 a hannun ƴan ta’addar,amma kuma irin matakan da aka ɗauka dangane da Jihar Oyo ya sha bambam domin kuwa kamar na Jihar Borno tamkara ana yi ma lamarin riƙon sakainar kashi, abinda ya ce sam bata saɓo wato bindiga a ruwa saboda kuwa ai su ma ƴaƴa ne’.
Ya ce irin wannan alamari na tamkar ana nuna ko ma ana son a nuna bambanci ne an maida wasu ƴan Mowa yayin da wasu kuma aka maida su ƴaƴan Bora, lamarin da ya ce sam bai kamata ba,abin har ma ya sa Iyayen su sun ɓara domin kuwa sun nuna buƙatar su da a kuɓutar masu da ƴaƴa.
Ya yi kira da mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, mataimakin Shugaban majalisar Dattawa, Ministocin tsaro babba da ƙarami wato ritaya janar Christopher Musa da Muhammadu Bello Matawalle, Gwamnonin Borno da Yobeƴan majalisun Borno, majalisun Wakila da Dattawa da duk wani mai faɗa aji da cewa a taimaka don Allah da ma’aikinsa a taimaka a samu ceto ɗaliban na Jihar Borno.














