Asibitin Ƙwararru da ke Potiskum a Jihar Yobe ya tabbatar da ɓullar cutar ciwon ido ta ‘Acute hemorrhagic conjunctiɓitis’, da aka fi sani da (Apollo), yayin da fargaba ke ƙaruwa kan yadda cutar ke yaɗuwa a garin.
Asibitin ya ƙara da kiran mazauna yankin da su kiyaye tsaftar kai da ta muhalli, sannan su bi matakan kariya domin daƙile yaɗuwar cutar.
Shugaban kwamitin shawarwari kan harkokin lafiya na asibitin, Dr. Abubakar Sadiƙ Zakari, wanda ya wakilci Daraktan Asibitin, ya bayyana cewa cibiyar ta rubuta samun mutane da dama da suka kamu da cutar.
To sai dai kuma, ya ce adadin mutanen da suka kamu na iya fin haka, kasancewar wasu ba sa zuwa asibiti sai dai su yi wa kansu magani a gida.
Zakari ya shawarci mazauna yankin da su riƙa wanke hannayensu akai-akai, su guji taɓa idanunsu, kuma su daina amfani da tawul, tufafi, kayan shimfiɗa, kofuna, ko sauran kayan amfanin yau da kullum tare da mutumin da ke da cutar.
Haka zalika, ya yi kira ga mutanen da suka kamu da su rage haɗa jiki da mutane kuma su nufi asibiti da zarar sun fuskanci alamun cutar.
Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Ajo na Jihar, Dr. Muhammad Lawan Gana, ya bayyana cewa ma’aikatar ta riga ta ƙarfafa matakan gaggawa domin ɗaƙile yaɗuwar cutar.
Ya ce an tsara muhimman saƙonni an rarraba su ga masu ruwa da tsaki da kafofin sada zumunta, sannan an umarci Jami’an Inganta Lafiya da su fahimtar da al’umma ta hanyar Masu Haɗa Kai na Ƙauyuka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna shiyya daban-daban a Potiskum sun ba da rahoton ƙaruwar mutanen da ke samun jajayen idanu ko kumburi da ƙaiƙayi da ciwo, da kuma fitar ruwa daga ido.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa mutane da dama a gida guda sun kamu da cutar, lamarin da ke ƙara firgita jama’a kan saurin yaɗuwarta.
Wani mazaunin garin, Haladu Badejo, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin mai ban tsoro, yana mai cewa cutar na yaɗuwa cikin sauri.
Wani mazaunin daban, Idris Bello Danchuawa, cewa ya yi: “Subhanallahi! Cutar Apollo (Ciwon Ido) tana ci gaba da yaɗuwa a Potiskum.”
Wani mai jinya, Abubakar Suleiman, ya bayyana cewa cutar ta zama babbar abin damuwa a garin.
“Wannan ciwon ido na Apollo ya zama kamar annoba a Potiskum. Rabonmu da mu ga cuta tana yaɗuwa haka tun daɗewa. Yana da wuya ka ziyarci gidaje biyu ba tare da ka tarar da wanda ya kamu da cutar ba,” in ji shi.
Suleiman ya ce cutar tana haifar da tsananin ja da ciwo a ido, ya kuma ƙara da cewa wasu marasa lafiyar sun sami sauƙi bayan amfani da ruwan ido (eye drops) da ƙwayoyin magani.














