ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Warware Rikicin Da Ya Bullo A Kungiyar Gwamnonin APC —Uba Sani

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
Uba sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce babu rikicin shugabanci a cikin kungiyar Gwamnonin APC ta Progressibe Gobernors’ Forum (PGF), yana mai jaddada cewa Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, har yanzu shi ne shugaban kungiyar.

PGF wata kafa ce da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC ke amfani da ita wajen hada manufofi da karfafa hadin kai a cikin jam’iyyar mai mulki.

Sani, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar, ya ce sabanin da ya kunno kai a cikin kungiyar gwamnonin APC kwanakin baya “karamin rashin fahimta ne” kawai wanda tuni aka warware.

ADVERTISEMENT

Gwamnan Kaduna ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Telebision.

Kalaman nasa sun biyo bayan rahotannin da suka bayyana a makon da ya gabata cewa wai an cire Uzodimma daga shugabancin PGF tare da maye gurbinsa da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, bayan wata ganawa mai zafi da aka yi a Abuja.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Rahotannin sun kuma yi ikirarin cewa kungiyar ta kasu gida biyu, inda wani bangare ke goyon bayan Uzodimma yayin da wani bangare ke mara wa Gwamnonin Dapo Abiodun na Ogun da Abdulrahman Abdulrazak na Kwara baya.

Lamarin ya haifar da hasashe kan yiwuwar rarrabuwar kai a cikin gwamnonin APC, inda aka ce Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani domin kwantar da hankula tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Sai dai Sani ya ce babu wani sauyin shugabanci a kungiyar, yana mai cewa dukkan gwamnoni sun sake haduwa.

Ya ce: “A ganina, ba babban al’amari ba ne kamar yadda wasu ke kokarin nuna shi.

“Saboda a dimokuradiyya mutane na iya yarda ko sabani da juna. Don haka a ganina karamin rashin fahimta ne kawai.

“A yanzu babu wata matsala. Dukkan gwamnoni suna tare. Mai girma Hope Uzodimma shi ne shugaban kungiyar Progressibe Gobernors Forum. Ni kuma, Sanata Uba Sani, ni ne mataimakin shugaban kungiyar,” in ji shi.

Sani ya bayyana cewa an warware matsalar gaba daya kuma ba za ta sake haifar da ce-ce-ku-ce ba.

“Ba na tunanin za ku sake jin wani abu game da wannan. Ina tabbatar muku, ba za ku sake jin wani abu ba,” in ji shi.

Da aka tambaye shi kai tsaye game da sabanin da ya faru a kungiyar, gwamnan Kaduna ya ce hakan abu ne da ya saba faruwa a siyasar dimokuradiyya.

“Abu ne na yau da kullum mutane su yi sabani. Amma kamar yadda na fada, wannan karamin rashin fahimta ne kawai, ba wani babban rikici bane, kuma an warware shi,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce da ace da gaske an samu sauyin shugabanci, da shi ne zai karbi shugabancin kungiyar a matsayinsa na mataimakin shugaban kungiyar.

“Idan da akwai sauyin shugabanci, ni a matsayina na mataimakin shugaban kungiyar da na karbi shugabancin. Amma zan iya tabbatar muku cewa ni ina wurin, kuma ni ne na bayyana cewa muna hade kuma komai lafiya,” in ji Sani.

APC
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
kwankwaso

2027: Hadakar Obi Da Kwankwaso Na Shan Suka Daga Wasu Jagororin Siyasar Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.